Haka Dija tayi ta tijara tana sakin maganganu amma Alh Sani Bai Kuma tanka mata ba don baya son suna musayar yawu da Dija a gaban Ya’yan nasu don gudun su fahimci wani Abu a tsakanin su
Washe gari kuwa Dija ta fice daga gidan zuwa korau ventures inda ake kawo kekunan Yara kala kala.ta zabowa salim da muhd kekuna masu kyau don bata samu irin na Al Mustafa ba Amma ta samu masu kyau ta siyo musu ta dawo gida tana jiran yaran su dawo makaranta tayi musu surprised
Suna shigowa gidan da gudun su suna tambayar momy kin siyo mana keken?
Ta tarbe su tana kama Hannun su zuwa falo inda ta ajiye musu kekunan a ledar su tana fadin
“Gasu nan kowa ya dauki nashi aje a huta kuka.
Salim ya dubi keken wanda babu danja babu tsuwwar da ke kiran thank you Daddy sai kawai ya fasa kuka yana fadin
“Ni ban son wannan momy baya fadin thank you daddy kuma babu wuta da danja.
Shi kuwa muhd da ya fasa nashi kukan jifa yayi da keken yana fadin
“Ni bana son wannan irin na Al Mustafa nake so sai suka kaure da kuka suna rikita falon da koke koken su .
Alh Sani ya shigo Salim da ya ruga da gudu yana makale uban nasu yana Fadin
“Baba momy tayi mana karya tace zata siya Mana keke Amma ba irin na Al Mustafa ta bamu ba don Allah ka siyo Mana zamuyi kokarin muma .
Alh Sani ya rufe bakin Salim yana fadin
“Subhallahi Salim momyn ce tayi muku karya? yaron yayi maxa ya Amsa Yana Fadin
“Eh ita tace zata siya mana irin na Al Mustafa kuma ba irin shi ta bamu ba.
“A kul na kuma jin kace momy tayi karya kar ka sake kaji ko? Ba zata iya siya muku bane shiyasa amma Idan kuna son irin keken Al Mustafa Ni zan siya muku smma sai kunyi kokari a makaranta kun kuma yi sauka maza kuje ku cire kayan makarantar nan kuyi salla .
Suka wuce suka bar Dija tsaye .
Alh Sani ya dube ta Yana fadin
“Sai ki mayar da su don na san iya karfin ki ne kika siya smma irin na Al Mustafa fa ba zaki iya siya ba in Kuma zaki iya kije Alfijir can ne zaki same shi ki taya kudin sa Sai ki yarda da Ni ba Zaki iya siye ba . Da zaki gane da kin daina son burge Ya’ya ki barsu a tafiyar da su da tarbiyar Ya’yan malam bahaushe ba irin Yadda kike so ba tunda suka fara Karya ta ki in aka wuce haka me kike zato?
Nan ya bar Dija cike da takaici dole ta Kwashi kekuna ta mayar ta Kuma Isa Alfijir taga irin keken Al Mustafa Amma Bata yarda ba ta iya siya ba sai da taji kudin su . Keke ne amma ya bawa dubu dari da hamsin Baya lallai kuwa ta yarda ba zata iya siya ba ina ita ina fidda kusan dubu dari hudu ta siyi keke biyu? Sai dai ta saka target da fatan kafin uban su ya siya musu itace zata siya musu
Al Mustafa da yake yaro Mai sanyi sai keken sa ya zama nasu su uku salim ya hau muhd ya hau wani lokacin ma zai bar musu ne suyi ta zagaye gidan suna jiniya suna Dariya yayin da alh Sani in ya gani yake fadin
“Al Mustafa lamarin ka akwai Allah a cikin sa Allah ya dafa maka ya taimake ka.b babu uwa babu uba lallai Allah gwani ne kuma tabbatacce.
Tunda Dija ta soma tsanar Al Mustafa sai ya zamo hatta hanne Dija ta kafa mata kahon zuka abun da ya kai da wanda bai Kai ba sai tayi ta kwara Mata ashar tana cin mutuncin ta. Amma Hanne sai ta danne tayi kamar bata san Dija nayi ba tunda ta gama Gane abinda dijar take nufi
Ganin hanne ta danne komai yasa Dija zuwa ta samu Haj kaltume ta zayyana mata karya da gaskiya akan Hanne da kuma Yadda alh Sani yake fifita Al Mustafa fiye da su Salim. karya da gaskiya tare da sharri kala kala duk Dija ta fadawa Haj kaltume wacce ta taho tana bal balin balaki ta Kuma iso gidan tana masifa.
Ta dubi hanne tana fadin
“Ke yar nan kin san matsayin ki a gidan nan? Hanne ta amsa da sauri.
“To fada min matsayin ki da har matar gida zata ce ga yadda take so ke kice ba haka ba? Ina ce matsayin ki bai wuce mai Rainon wannan kahirin yaron mai kama da dan Ruwa ba? To Aikin naki ya Isa haka tunda Abun naku babu mutunci maza tattare kayan ki ki kama gaban ki.
Alh Sani ya fito Yana yiwa mahaifiyar tasa sannu da zuwa tayi maza ta daga mishi hannu tana Fadin
“Kaine da sannu dube ni da kyau zaka gane bana tare da abinda za ayi min sannu ko ka ga Alamar ciwo ko gajiya a tare Dani ? haka ka zama Sani ? yadda Uwar yaron nan ta hana mana Rawar gaban hantsi shine shima zai zo ya hana Dija zaman lafiya a gidan ta? To karya kuke wallahi kai da shi don haka maza ka tattare yaron nan ka mayar da Shi can gidan garbati tunda uwar sa ta mutu ai dama itace kace an baka amana ko? To yaron nan ya Gama zama nan gidan tunda ya zama mai hada fitina har kana fifita shi akan su Salim . kuma ita wannan matar da ka ajiye me kake nufi da ajiye ta gidan ka? .
Dija tayi karab ta amshe zancen da fadin
“Nima abinda nake son Sani kenan haj in kishiya ta ce ai gara na sani in auren ta yake so gara yayi da dai a zaune min gida da sunan Raino da kula in Kuma itace matar da gida gara na sani ko ya sallame ni.
Sani ya dubi haj kaltume yana fadin
“Haj ta Yaya zan mayar da Al mustafa wurin garbati? Mune fa dolen Al Mustafa ba kawu garbati ba kuma in na mayar da shi ta yaya zai samu kulawa har ya ci gaba da karatun sa?.
“Kai ya ishe ka haka kaji ko? Uban sa ne kai ne da zaka kalawa kanka sai yayi karatun? Kar Allah ya sa yayi mana meye zai dame ka? .
“Kiyi hakuri Haj Al Mustafa dan uwa na ne ko bai zama dan uwa na ba yadda naga maraicin sa dole zan tausaya mishi don ban san yadda nima Rayuwa zatayi da nawa Ya’yan ba wata kil abinda zanyi mishi ya zama garkuwa ne ga nawa Ya’yan don haka kiyi hakuri haj Al Mustafa bashi da wanda yafi ni na zaci kece wacce zata zama madadi na haj ko bana Raye ashe kece ta farkon da zaki juyawa yaron nan Baya to haj in Dija ba zata iya zama da Al Mustafa ba ta tafi na yarje mata don ba zan takura ta ba kamar yadda ba zan yarda a takura Al Mustafa ba.
“Kenan ba zakayi yadda nace ba shine har kake korar Dija akan Ido na? .
“Ba haka bane Haj ai ta kawo karar Mustafa ne ko ? to mustafa Babu inda zaije matukar ina Raye .
“To shikenan tunda haka ka zaba Dija yi tafiyar ki gida ko don ya gane kina da amfani bar mishi Ya’yan don uban sa Al Mustafa kuma don Allah ka Rubuta shi a cikin kundun Ya’yan ka ni na gani idan ya Isa ya zama haka . kuma wanna matar dole ta bar gidan nan a yau matukar dai ba wani abu kuke nufi ba in kuma da wani Abu ne fada mana?.
“To Haj in dai ta tafi ba ni na Kore ta ba kuma gaskiya ba zan bi bayan ta ba in taga zata iya zama da Al Mustafa ta kuma dauke Shi kamar su Salim sai nace mata tayi hakan don ko babu komai yaron nan maraya ne ladar Rukon sa kawai Allah na iya mata wani tagomsshin amma matukar ba zata iya zama da shi ba tana kallon sa a makiyin ta to ba ma sai kince ta tafi ba ni da kaina zan sauwake mata.
Dija ta fusata tana fadin
“To ayi hakan mana Ina ce ba kaine karshen maza ba? wallahi ba zanyi hakan ba sai dai ko kafin na isa gidan mu ka aike min da takardar kawai.
Ta wuce su ta shiga Daki ta figo gyale zata wuce ne hanne ta rike ta tana fadin
“Don Allah tsaya Dija wallahi ban shigo gidan nan da nufin wani Abu ba baya ga kulawa da yaron nan Al Mustafa. Wallahi ba zan yarda ta Sila ta auren ku ya rabu ba Al Mustafa dai ya Isa yayiwa kansa komai a yanzu to kuyi hakuri don Allah ki rike yaron nan da adalci ko don maraicin sa .
Dija tayi mata wani banzan kallo kafin tace
“Da dai kin gyara farin sai bak’in ya sami shiga. In ba da wata manufar Kika shigo ba me kike jira tunda har kin san zai iya yiwa kansa komai? Don Allah kafin Rana irin ta yau hanne inji ke da sani kun zama kata da miji.
Ta wuce ta bar hanne da binta da Ido inda itama Haj kaltume ta ce
“Dama haka kike so kin kuma samu sai kije ki biya malamin ki amma kuma ni nayi miki alkawarin karya koma meye ki surare ni.
Hanne ta soma share tana fadin
“Alh dole na bar Aikin nan ina maka fatan alheri Ina wa Al Mustafa shima Allah ta ala ya tallafi Rayuwar sa yasa shi mai sa a da Alfarma a Rayuwa dama haka abin Yake yawan kalubalen ka s Rayuwa yawan nasarar ka yawan daukakar ka.
Bata jira komai ba tana gama fadar hakan ta fice tana dauke kwallar idon ta inda a bakin kofa taci karo da Al Mustafa wanda ya ganta tana kuka.
“Nani me ya same ki?.
Ta ruko shi tana shafa sumar kanshi tana fadin
“Al Mustafa zan tafi sai wata rana Allah ya tallafawa Rayuwar ka in sha Allah zan rika zuwa ina duba ka.
Da sauri ta sake shi ta wuce inda alh Sani ya buyo bayan ta yana kiran ta amma bata juyo ba dole ya bi bayan ta. Don biyan ta kudin aikin ta.
Tunda Dija ta koma gida ta sanar da iyayen ta abinda ya faru suka fada mata tayi kuskure shi D’a ai na kowa ne bare kuma maraya wanda Yake a matsayin dan uwan mijin ta meye faduwa in ta hada shi da nata Ya’yan ta Rike? amma Dija ta kafa ba zata koma ba inda mahaifin ta kuma ya zuba mata ido bai nemi Alh Sani ba saboda ya san nan dai shi akayiwa ba daidai ba yarsa ce tayi butulci kuma ya zuba mata ido ne don ya bata damar gane kuskuren ta in ta zaunu a gidan.
Kwana daya shiru biyu shiru uku hudu har zuwa Sati babu amon Alh Sani abinda kuma ya fara nunawa Dija kuskuren ta amma kuma taurin zuciya da nuna matanci ya hana ta wani motsi.
Sati biyu daidai da zuwan ta gida taji baban su yana fadawa babar su sati mai kamawa ne Alh Sani yake daura aure da wata matar . babar su Dija ta amsa da fadin.
“Yayi hikima wallahi malan yanzu don mace tace ba zata zauna da namiji ba ai itace a ruwa shi namiji in dai da kudin sa ai kuma managa ta kare sai dai in bai saka kanshi ba. Allah ya sanya alheri yasa mutuwa ce Rabaww.
Dija taji kanta na sarawa jin danyen sikin da sani yayi mata amma kuwa in dai har haka ne lallai haj kaltume ce ta cuce ta tunda itace ta bata shawarar hakan.
Ranar da Alh Sani yabi bayan hanne a ranar ne ya nemi izinin auren ta amma ta nuna mishi ba zai yuwu ba ba zata iya auren shi ba alhalin matar sa tana zargin wani Abu a tsakanin su idan hakan ta tabbata ai zata gasgata zaton ta ne .
Alh Sani kuwa bai tab’a Jin yana ra ayin wata mace ba amma abinda Dija tayi mishi yasa shi Jin lallai dole ya nemi aure kuma hanne ya kamata ya nema .
Hanne ta ja ta kafe akan ba zata aure shi ba amma kuma a tashi daya komai ya sauya sai ga magana ta kankama.
Haj kaltume da yazo yana fadawa maganar auren ta daki kirji tana Fadin
“Sannu namiji dama haka ka tsara ? To ana haka dama amma ka sani a yau din nan zaka je da kafar ka ka dawo da Dija don kai kanka ka san kayi kad’an wata mace tazo taka haye ta more ka fiye da Dija wacce ta jure komai akwai da babun ka sai yanzu ne zaka ce uwar ta Bak’a ce baka Isa ba wallahi.
“Haj ba ni na kori Dija ita ta tafi to nayi mata alfarma ta dawo a cikin cewar ki amma ni na gama da ita ne ba kuma zan bita ba in ta gaji da zaman zata iya dawowa.
“Ni sai naje na dawo da ita tunda ban Isa nace kayi kayi ba kuma duk abinda ka san ana yiwa mace in za ayi mata kishiya na kishin laifi sai ka hado su wallahi ka bawa Dija in kuma ka Isa kace ba haka ba kaga bacin Rai.
A Ranar Haj kaltume ta dawo da Dija Alh Sani kuma ya hadawa Dija kayan kishin laifi ya bata har da kudi duka ya bata
Ranar da hanne ta tare Dija kamar zatayi hauka saboda ganin wacce Sani ya kawo mata a matsayin kishiya.
Tuni ta kira Haj kaltume ta sanar da ita labarin auren Sani da hanne tana kuka tana fadin
An cuce ta ba zata zauna ba.
“Hanya ta fa a bude take Dija kuma shigowar hanne a gidan nan karo na biyu ta dawo ne ba don komai ba sai don shawarar da kika bada Kuma kinga Al Mustafa ya kara samun kafuwa tunda ya samu uwa in zaki yarda sai nace ke da hanne duka aure ya kawo min ku to bana son kunji kunji in kuma ba zaki iya ba kamar yadda kika ce wallahi ina maraba da mai zuwa ina wa mai tafiya fatan sauka lafiya don na Shirya akan Al Mustafa sai dai koma meye ya faru gaskiya bana shakka ni kadai ma zan iya tsayawa na kula da Al Mustafa don shi Amana ce daga mahaifi na zan Kuma tabbatar da na Rike mishi Amana.
Dija dai sai share hawaye take tana jin gara ta bar auren nan kawai tunda ba shine karshen maza ba amma kuma tana tunanin zaman gida don haka sai ta jirayi shawarar zuciyar ta.
Al Mustafa kam ya zama kafin ALLAH duk yadda Dija taso cutar da shi Allah ya tsare kayan sa yayin da hanne kuma take kula da dukkan Ya’yan gidan da zuciyar ta daya babu Ruwan ta da duk wani wulakancin Dija ta kawar da kanta ta bar komai a ba komai Rayuwa ce ke zuwa da komai.
Shekara daya da auren hanne ta haifi dan ta daya mai sunan malam yayin da Al Mustafa yake ta murna Dija Kam tamkar zata kama da wuta saboda bak’in ciki Haj kaltume ma tana bayan Dija suna nunawa hanne bakin hali amma dai tana ta kawar da kai bata biye musu hidimar gaban ta kawai take .
Watanni hudu bayan haihuwar mai sunan malam Al Amuran Alh Sani suka soma sauyawa kasuwa taja baya yayin da haj kaltume ce da dija suka fara dora hakan akan auren hanne wacce suke cewa farar kafa ce tazo musu da ita musamman ma haj kaltume da take takama da alh Sani to ga homar tata kaddarar Allah ta soma sauka akan sa.
Al wmarin ya samo asali ne daga abokan kasuwar Sani wanda Allah yayiwa nasibi kayan sa sunfi na sauran yan kasuwa arha don shi yau da gobe itace kasuwa a gare shi ba tarin kudade ba kadan mai albarka yake so.