Skip to content
Part 84 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Habiba ta shimfida Mata tabarma ta Zauna ta kawo Mata Ruwan Sanyi Tasha tana Fadin

“Habiba ya na same ku Ina Yara Ina Rabi u?

Habiba tace

“Duk muna lafiya Haj ya Saudi kun shige makka zaman ku Haj.

“Ke Bari habiba Ni yanzu kudi Nazo nema na Samu nayi cuku cukun komawa na baro kaf tarin dukiya ta a can askar sun Dama min salalar tsiya habiba ban iso Nigeria da komai ba sai kayan Nan na jiki na hatta da suturu na suna can ga gwala gwalai na da Riyalai na na baro a Dakin mu ina tsoron cima da yaduwa don dama ba wani zaman Dadi muke ba me kike zato idan suka Gane askar sun Danko ni? Ni wallahi bana ma ko shakka akwai tsamin munafunci a cikin Al Amarin Nan ta yuwu ma jono min askar din Nan akayi  Don wulakanta Ni gashi Kuma magauta sunyi nasara a kaina in ma sunyi don in muzanta to sunyi nasara sai Kuma ta fashe da kuka Alamar abun Yana cin Ranta .

Habiba ta zuba Mata ido tana kallon ta da Mamakin Halin da take ciki Wanda Babu ko tantama Amana ce take matsar ta koma ace hakki na bibiya.

Kuka Haj kaltume take kashirban bil hakki da gaskiya kuma a Ranta Babu abinda take fata da buri irin ta harhada kudaden da zata koma Saudi Arabia ta dauko dukiyar ta.

Habiba tayi shuru ta kasa tankawa Haj kaltume da ke Kuka don Bata San me zata ce Mata ba .

Haj kaltume tana cikin kukan ne Rabi u ya shigo indo yayi turus Yana kallon Haj kaltume tana kuka ya Kuma kasa matsawa bare ya tambaye ta dalilin kukan ta abinda ya zo a Ran shi shine ADDU AR da yake ta aikawa ce ta askar su Danko mahaifiyar tasa gashi Kuma ADDU AR sa  ta  karbu.

Haj kaltume ta dago idon ta taga Rabi u tayi maza tace

“Rabi u ? Taho don Allah ku Rufa min asiri kamar yadda Allah ya Rufa muku Kai da matar ka ko Rance ne ku Samo min wallahi da na kwaso dukiya ta Zan biya ku.

“Yo Haj ya akayi Haka ne?

Ya tambaye ta ta Kuma Rusa kuka tana zayyana mishi yadda akayi Mata kamun Wanda a yanzu ma take cewa saka hannu ne magauta ne  .

“To Haj da wane kudin Zan Rufa Miki asiri Bayan duk kin siyar da komai? Nima fa ban jima da dawowa da gudun hijirar da nayi ba sanadin balakin da Kika saka Ni.

“Kar ka tona komai Rabi u dukiyar ku da na dauka Kai da Al Mustafa da Ya’yan wurin Sani duk bashi ne na dauka Zan biya ku Kuma ka San adadin yawan dukiyar da na Samu a Saudi ? To har Kai ka warke kuma Zan biya kowa don Allah ko Bashi ne ka ciwo min Zan biya wallahi ina tsoron cima da yaduwa suyi min sama da Fadi don in suka Samu dukiya ta sun Gama da zaman tukaranci kowace k’asar su zata koma.

“Ni Kam Babu inda zanje na Samo Miki bashi Haj ki barni da Wanda Kika Dora min ma Banda Allah ya hada ni da Al Mustafa da ban San Kuma Ina Zan saka kaina ba.

“Wane Al Mustafa? Ta fada tana duban Rabi u Wanda ya Bata Amsa da Dan wurin Rabi.

Anan ya sanar da ita irin daukakar da Ubangiji yayiwa Al Mustafa har ya zama a karkashin sa Yana aiki.

Ta mike da sauri tana Fadin

“Al Mustafa dai wannan Dan wurin Rabi? Yau Ni na shiga uku .

“Muje muje ka kaini wurin shi ai in dai jinin Rabi ne ba zai Rike Ni a Ranshi ba don uwar sa har mukayi kishi da ita Bata tab’a gardama da Ni ba bare ta mayar min da magana Kai Ashe dai abinda ka Raina.

Rabi u ya zauna maimakon ya tashi su tafi sai ya zauna Yana Fadin

“Ni Kam ba Zan iya kaiki gaban yaron Nan ba don na san kunya kawai Zan Sha Kuma ko kin nemi taimako ko Rancen kudin Allah Haj zance Kar ya Baki ba biya zakiyi ba .

“Na fa Gaya maka dukiya ta a Dakin su cima da yaduwa makiya na ne wallahi da su kwashe Rabi u ba gara na turo muku hakkin ku ba? Don Allah kayi hakuri na San ban kyauta maka ba Amma da niyar na biya ka kudin ka na tafi in naje na Samo taimaka mini Rabe dube Ni mana ko lafiyar kirki bani da ita wallahi hankali na kaf Yana Kan dukiya ta idan na Rasa ta har Raina Zan iya Rasawa taimaka min Rabe don girman Allah.

Wani Abu ya tab’a zuciyar sa Jin irin Rokon da mahaifiyar tasa   take Masa Dole ya tashi suka tafi wurin Al Mustafa Wanda ya Karbe ta da mutuntaww Yana gaishe ta ta soma kuka tana Rokon shi yafiya da afuwa Akan abinda tayi mishi yayi maza ta tare ta yana Fadin.

“Haj abinda ya wuce ya wuce a daina Tayar da shi Naga kamar ba kya jin Dadi ko anje asibiti?.

“Kayya Al Mustafa lafiya fa Babu ita Amma ba itace a Gaba na ba na baro dukiya ta a Saudi shine nake so a taimaka min da Rancen kudi In koma in Dauko.

“An Gama Haj shikenan abinda kike so? Al Mustafa ya fada Yana kallon ta tayi maza tace shikenan wallahi Al Mustafa nagode maka Allah ya jikan lahirar iyayen ka da Rahama hakika ka nuna jinin Rabi ne baiwar Allah matar Nan har ta komawa Ubangiji Bata tab’a Saba Mana ba.

Al Mustafa ya dubi Alh Rabi u Yana Fadin

“Yaya Rabi u Aje ayiwa Haj Visa da passport da sauri ko nawa ne Zan biya Kar ta wuce gobe ba a Gama ba.

Kan kace me? Aiki da kudi ba ya Wahala sai ga komai an yiwa haj kaltume inda aka badda kudade masu daraja Kan kace me? Har asibiti an kaita an duba ta an Bata magunguna Tasha ta samu Sauki sosai Ranar asabar jirgin su haj kaltume ya Daga Saudi Arabia don zuwa Kai Haj kaltume ta kwaso dukiyar ta shin Yaya zata Kaya tsakanin ta da su cima da yaduwa? .

Tukuro ya zuki tabar sa ta iblis Yana fesar da yakin Yana ganin wulakancin da ake Shirin yi mishi na nuna mishi yay Rabi u ya fishi Boko shi Bai San komai ba Sai Rabi u Wanda ko wani dogon Rubutu za ayi ko wakilci Sai ace Rabi u ne zaije ya Kuma je ya Samo alheri shi Yana Nan Zaune sai in anyi albashin wata a Bashi Kuma a yanzu ma Rabi u ya kusa fin shi albashin don Haka Yake ta saka yadda zaiyi da Rabi u.

Al Amarin Al Mustafa Kuma a yanzu yayi girman da Yake hurda da kamfunna Kai tsaye ba Wai ta Hannun Yan kasuwa ba sai dai yayiwa kamfani magana Yana son Abu kaza adadin yawan da Yake so Haka za siyar mishi motocin sa su Dauko mishi su kawo mishi Rumbun ajiyar sa

Har zuwa wannan lokacin Haj Amina matar Al Mustafa Bata ko yi batan wata ba bare haihuwa idan akwai masu damuwa da Rashin haihuwar to Baddo ce mahaifiyar Amina sai Kuma malam Musa Amma Al Mustafa da Amina Basu da damuwa don sun dayanta Allah sun Kuma San komai lokaci ne in lokacin yayi sai dai kawai su Gani.

Sirrin da Al Mustafa ya Gane na ciyarwa da taimakon mabukata shine ya Kara daga martabar sa da ta dukiyar sa don Haka abinci ake dafawa Mai yawa sama da buhu biyar kullum ana Bawa almajirai da masu bukata don Haka sai Al Amarin Al Mustafa ya zama gagara badau

Tafi tafi sai ga maganar bude kamfani Daga taskar Al Mustafa Wanda zai fara bude kamfanin takin zamani na farko a Jos a Nigeria don Haka Al amarin Mai ban Kaye ne sosai musamman ga Al ummar garin Jos Wanda suka tabbatar da dubun dubatar Al umma ne zasu karu da Samun Aiki a kamfanin Dan kyana

Tuni kuwa komai ya tabbata kamfani ya fara Aikin fidda takin zamani cikin nasara takin Kuma ya karbu matuka Gaya har fidda shi waje ake Kuma maido da kudin sa mafiya daraja

Samun wannan daukakar sai aka Dauki Alh Rabi u ya Zama manajan kamfanin takin zamani abinda Kuma ya Kara harzuka tukuro shaid’an Yana kallo Rabi u ya zarce shi a matsayin da Baya son a zarce shi. Kaji Dan Adam.

Al Mustafa ya soma tunanin leka gidajen marayu musamman da Yake ya dandana d’acin maraicin yaji Yadda duniyar maraicin take don Haka sai Yake zuwa gidan marayun  Yana ganin yadda suke Rayuwa wasu Ya’yan tsintuwa ne wasu Kuma marayun da basu da gaba da Baya ne Dole ake Mika su gidan marayu tunda Babu Mai jibantar lamuran su sai Al Mustafa ya kallafawa Kan sa zama Uwa Kuma uba a garesu wadan Nan marayun ta hanyar yi musu riguna da sutura da abincin Basu har da daukar takalifin karatun su na Arabi da Boko

Haka gidajen masu lalurar tab’in Hankali da asibitocin da suke dankam da dubun dubatar Al ummar da take cike da zafin Rashi da Babu ga ciwo ga Babu  ga kuma kudin magani Suma Babu Sai Al Mustafa ya tsaya ganin Mai ciwon da Yake bukatar magani a bashi da biya mishi kudin asibiti har sarki Mai yawan Rahama ya wanzar da Sauki . Wanda Kuma za ayi wa theater Babu kudin Aikin da na magani Duka Al Mustafa ya dauke wannan nauyin yayin da dukkan kafatanin garin Jos da Gombe da bauci Babu abinda kake ji sai ADDU AR Aminci ga Uwa da Uba na Al Mustafa Dan kyana domin kuwa ya wanke zukata da yawa daga kunci da damuwa da yunwa da fatara sai Allah Ubangijin Yake ta yauka’k’a arzikin Al Mustafa inda har aka Kuma bude kamfanin sumunti na Dan kyana sument tare da kamfanin fulawa itama ta Dan kyana fulawa.

Rabi u Kam da ya ga Al Mustafa ya soma kawo wasu Daga cikin dangin mahaifiyar sa wasu daga ahalin kawu garbati da Kuma wasu daga cikin dangin Haj Amina matar sa sai Rabi u Yake ganin Al Mustafa yaso yaci mutuncin su saboda me zai Bawa wasu can da basu Zama Dolen shi ba ya Basu Rukon manyan kamfunna irin wannan Wanda sukafi nasu daraja? Me ake Samu a kamfanin takin zamani ? Ga inda ake samun kudi Nan kamfanin sumunti da na fulawa Amma don ya nuna musu yafi son dangin matar sa da na Rabi shine ya Kai su inda Madarar take shi kuma aka bar Shi Yana wahala.

Tun daga wannan lokacin Rabi u ya kullaci Dan kyana Wai Yana nuna musu bangaranci.

A Ransa Yake tunanin abinda zaiyi ya zama mafita Amma ya Gane Dole sai ya samu wanda zai Goya mishi baya ya Kuma Zama mataimaki don Haka yaga Babu kowa sai tukuro shaid’anin Haj don Haka ya tsallaka ya samu tukuro Yana koka mishi Halin da ake ciki ya kuma haska mishi cewa lallai AZURFA DA ZINARE suna nan damfare a kamfunna biyu din Nan kamfanin sumunti da na fulawa Amma Al Mustafa ya Rasa Wanda zai saka daga dangin matar sa sai na Uwar sa amma su na Uban sa ya mayar da su jikkar Bayan sirdi don Haka Yake neman Wanda zasu tsaya don ganin Basu yi Aikin banza ba gara su lalubo mafitar da zata fisshesu tun wankin hula Bai Kai su dare ba.

Tukuro ya kyalkyale da Dariya har Yana buga kafa Alamar ya Samu abinda Yake so ko kuwa Dariyar sa ta mecece?

Shi Kan shi Alh Rabi u sai da Dariyar tukuro ta bashi haushi to meye na Dariya? Shi kuwa turkuro wani shaid’ancin ne ya hararo shine Yake Dariya don dama a cikin Shirin  kullawa Alh Rabi u mugun kullin Yake sai ga shi ya Fado a arha don Haka zaiyi amfani da wannan damar don ya turbude hancin Rabi u yayi biyu babu don har wancan kamfanin da Yake rainawa sai ya baro shi Yasin karshe ma yazo yana dama ya Sani don za a nuna mishi shaid’ancin ganin idon sa.

Shaid’an yayi dariya kamar wanda ya dauki hanyar Zaria.

Abinda kuma ya harzuka Alh Rabi u Wanda yaji kamar ya kifawa tukuron Mari amma sanin ya San in yayi hakan ba zasu kwashe da marar arziki ba yasa yaci gaba da hadiyar zuciya yana kallon tukuron da son yaga iyakar wulakancin sa

Tukuro ya gama dariyar sa Yana share hawayen dariya ya dubi Alh Rabi u Yana fadin

“Wallahi da kayan haushi kake Yaya Rabe. Ashe ko a bokon ma akwai gaba da gabanta kaima Ashe akwai inda baka zo ba? Nifa ba karamin dadi naji ba da aka samu wasu tsinannu da suka kafa kungiyar voko haram don ni in fada maka gaskiya karatun Boko ko na wankan tsarki ban sani ba shiyasa ma nayi tayiwa malaman bokon ta adi don akwai malamar da na kwale wando na zan bi ta kanta da Naga tana neman watse ni don kawai ta bada aiki ban iya ba take ce min jakin aji shine na nuna mata jakanci . Shine fa da ta ga tsayi na ta soma kwara ihu yana neman mafita da aka zo aka ganni aka kore ni tun daga Ranar ni na tsinewa Boko amma ku da kukayi ta har kuka dire da kazo Nan ba har wani hura mini hanci kake ba kai ga dan Bokon da Yake tari ABCD su sauka sai yanzu ne da kaga maza a gaban ka kake tuna Allah? Ni fa na kawo ka wurin nan Yaya Rabi u smma kawai daga an Kaika kamfani ka soma daga min kafada yanzu me kake so ayi to da ka tuna ni naka ne? Wai shi dama dan Adam haka yake baya tuna dan Uwan sa sai Ranar bukata?.

Alh Rabi u ya share zufar sa Yana Jin ashe tukuro ya kullaci yar daukakar da ya samu?

“Kar ka saka jahilci mana tukuro Akan abinda Allah ne Yake yi? Ni ma ban San kaji ciwon hakan ba da nace mu tafi tare da Kai tunda dama tare muke.

“Ok Kai yanzu me ka saka a Nan ? Nine kawai na saka jahilci da ka zarce Ni daukaka Kai meye sunan abunda kayi a yanzu da kake fadar an Bawa wasu Aikin da ya zarce naka ? Kai ilimi ne ka saka ko kuwa dabbanci?.

Alh Rabi u ya dubi tukuro kafin yace

“Kaga tukuro Ni da Kai ne ya kamata ace mun Zama gagara badau a dukkan kamfunnan dan kyana tunda damu komai ya hab’aka mu bar duban daukakar juna duk Wanda Allah ya Bawa sai ya samu Ni Yanzu so nake mu samu wata hanya da muma zamu Zama wasu a duniya kafin yaron Nan ya nuna Mana mu bare ne kamar yadda ya fara a yanzu ya dauko dangin matar sa da na Uwar sa  ba ka ganin Nan gaba zai mayar damu baya ya ja wasu ya Kai gaba mu muna Nan mun Kare a banza wofi wata Kil ma Ni ko Kai bamu Aje komai ba?.

Shaid’an ya zaro Karan tabar sa ta iblis wacce ko. A gaban Uban wa zai bugawa abar sa wuta

Ya Kuma buga wuta Yana Jan hayakin cike da gwanancewa ya soma fidda hayakin tamkar salansar mashin ya Kuma hada Dan karamin hadari a gaban Rabi u Wanda ya toshe hancin sa saboda kaurin tabar da yake Shiga hancin sa har makoshin sa.

“Ah yaya Rabi u Kai sai yanzu ne kayi wannan tunanin na ka tashi ka mallaki wani Abu saboda kerewa talauci? Ai Ni tuni na kafa indararon tattare Rabo na in Kai baka fara ba Ni na Dade da yin nisa malam Rabe.

“Lallai kaci Sunan ka tukuro shaid’anin Haj kace nine na farka a yanzu? To Yaya za ayi Ni ?.

“Ai yadda za ayi tana hannun ka Rabe tunda Ni ban San Yaya kake Rayuwa a inda kake ba Ni da na San yadda nake Rayuwa a Nan ai kaina baiyi murfin da Ya kulle na kasa Gane gaba da Baya ba don Haka kaje ka yi nazari ka Samu hanyar da asusun ka zai San kazo shine kawai mafita a gareka in kayi hakan ka tsira in Kuma ka saka I’mani to sai nace maka sannu .

Tun daga Ranar da sukayi wannan maganar da shaid’an ya kasa samun hanyar  da zai soma dankar Rabon shi Amma harka tana can kamfanin sumunti da na fulawa Amma na takin zamani sai a hankali duk abinda zai fita ma ogan ne ta turo koma ya dafe kudin sa babu ta inda wani Abu zai fita ba tare da sani ba

Tuni ba tun yau ba tukuro Yake wawasar dukiyar Al Mustafa da son a karewa talauci Dama da wannan manufar ya shigo ya Kuma yi sa a shiyasa ma yaji haushin Alh Rabi u da aka hada su don Kar ya Gane allon shima yace zai dafa

Shima Alh Rabi u sai ya samu wata barauniyar hanya wacce Yake fidda Kaya ayi BLACK MARKET ya auna kudin sa cikin account din banki

Samun wannan hanya sai Rabi u ya soma fitowa shima Yana Hawa manyan motoci da manyan Riguna Yana homa da bada Fadi

Kan kace me? Wadan Nan mutanen biyu tukuro da Rabi u sunyiwa Al Mustafa illa matuka Gaya Amma da Yake Allah ya kafa Kaya sa Bai ko girgiza ba Kuma Bai fasa abinda Yake ba na alheri sai ma karawa da yayi Kuma Suma din mabanbantan NASA Yana Kan yi musu ya Kuma yiwa iyayen su da Yan uwan su Amma suna mishi zagon kasa Wanda suke cutar da kansu suna zaton sun zalunce shi ne basu San bokiti Mai yoyo bane.

A lokacin da Haj kaltume ta fito daga gidan su dake bene Hawa na takwas da nufin zuwa bakin harami Ashe gari ba kyau askar sun fito kamun Kan Mai uwa da wabi saboda cikin wannan lokacin ajnabai sun fiye tafka mugun Abu a kasar shiyasa duk lokacin da irin Haka ta samu ake Kamen Kan Mai uwa da wabi shiyasa da askar sun danka sai su watsa mota Babu Ruwan su da abinda zaka fada bare su saurari uzurin ka.

Babu zato Babu tsammani Haj kaltume taji ta a Hannun askar din Saudi sun cika Hannu da ita tuni Kuma suka auna a guje suna kamo sauran

Ta  baro Saudi Arabia Babu zato askar suka yi Mata kamun garin ku yayi Kiran ki inda take ta kukan dukiyar ta a Daki Amma babu Mai kula ta har suka Kai ta Lagos suka watsar

Lokacin da cima ta falfalo aguje tana mayar da numfashi don ta Samu ta Sha da kyar daga gujewa kamun askar din da yau din garin na Saudi Babu sauran walawar ajnabai bakar fata tunda aka tashi da wannan ta asar da akayi a garin

Ta Fado gidan Nasu tana mayar da kofa ta Rufe har da saka sakata inda ta jiyo yaduwa tana Fadin .

“Ke cima ya akayi ne ko askar sun matsa lamba ne?

Cima ta Shiga tana Fadin

“Wallahi Babu lafiya yaduwa dubi fa duk na zubr da kayan miyar garin gudu har da Yan sauran Riyalai na inda wani shege ya Kai min caffa har da kokarin dankar kugu na na kaiwa shege mangari Babu arziki ya sau Ni na auno aguje yau Kam Babu sauran wali ince dai Babu Wanda yayi Nissan kiwo a gidan?.

Yaduwa ta cabe da Fadin

“Kai kamar fa Naga kaltume ta futa kin santa da shegen ki Fadi bata ce min zata fita bare najiyo Mata motsi .

“Ke bar tsohuwar wofi Ni wannan matar na Rasa da tsiyar me take takama har tana hura hanci ke da Kika baro k’asar ku Kika zo tukaranci Amma kike ta nunawa mutane ASALI? Bar kafura ma tayi tuntube da askar din su danki Yar Banza ta koma garin su muga ta tsiya.

“Ai ba a biyewa mutum cima musumi Dan Uwan musulmi ne Babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi tsoron Allah Bari na bi bayanta in batayi nisa ba na sanar Mata gari ba kyau.

Da sauri yaduwa ta mike zata fice cima ta Ruko ta tana Fadin

“Ana garin Babu kyau kike kokarin fita? Kina Zaton idan itace Kika fita zata iya sanar da ke? Kyale ta ita ta juyo wallahi in ma an kama ta ai ta huta da .

“Ba zai yuwu ba cima muna kallo ta fada halaka ai Babu Dadi Allah ma sai ya tambaye mu abinda nayi Kuma don Allah nayi ba don ita ba .

<< Azurfa Da Zinari 83Azurfa Da Zinari 85 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×