Tukuro ya dubi Alh Rabi u yana zare idanu Yana fadin,
“Wai wannan shegen saboda mutuwar matar nan ne ya mimmike a gadon asibiti haka yana ma alufa da son nuna Mana jimami yake? Ni fa na fara lura da mutumin nan yaya Rabi u wallahi ya fara gajiya da mu tun ranar da yayi muku Rashin kunyar nan.
“Kai ba wannan ba tukuro wai matar can tashi da ta mutu ta haife cikin ta ko kuwa da shi ta mutu? matukar fa ba tashi tsaye mukayi ba to zai zama wahalar banza mukayiwa yaron nan mu Kuma tashi a tutar maho tunda ya san ya kwaso dangin uwar sa da na matar sa ai kuma shikenan mu mun tashi daga aiki wallshi gara mu gane mai fisshe mu.
Tukuro ya jawo molin tabar wowi wacce ya bugawa wuta yana jan hayakin yanab fesarwa ya dubi Alhaji Rabi’u yana fadin,
“Ni fa sai yanzu da ka yi maganar haihuwar matar nan tasa na tuna tana da ciki amma na fi zaton ace ita da cikin ne suka margaya.
“A a tukuro in ya zama ta haihu ta bar dan ko diyar ai yanzu ne muka Shiga matsala don dan Al Mustafa ko yar sa kalubale ne a cikin Rayuwar mu ko da kuwa Al Mustafa ya bar duniya don komai xai tattara ne akan dan sa ko yarsa da sunan gaje dukiyar mahaifin mu kuma muna nan a wofi.
“To mu je mana mu tambaye shi sai mu samu cikakken bayani.
Almustafa yana kwance yana tuna Amina da irin rayuwarsu wai a yanzu shikenan shi da ita sai dai a kiyama ko ya tuna ta a zuciyar sa ko ya kalli taswirar ta a hoto.
Hawaye suka soma zarya a fuskarsu yana Jin ina ma zai Samu shima ya Mara Mata baya a yanzu? Sai Kuma ya tuna da Dan su Kaisar wanda shine kawai abinda ya mallaka a duniya kaf din ta a yanzu in ya mutu Kuma waye gatan Kaisar Al Mustafa? Sai yaji tamkar Amon sautin muryar Amina Yana dawo mishi tarwaa kunnuwa lokacin da yayi Mata tambaya Mai shigen wannan ta ga wa ta bar su ? Ta Kuma ce mishi a Hannun Allah su Duka suna karkashin inuwar Ubangiji ne sai yayi maza yayi istigifari.
Tukuro ya turo kofar Dakin Suka shigo shi da Rabi u inda Suka Tara’s da idanun Al Mustafa suna zubar da hawaye.
“Wai kukan Nan na lafiya ne Al Mustafa? In don mutuwar matar Nan taka ne har zuwa yanzu baka Gane Allah ne yayi maka Rahama da ya Yankee kwanan matar Nan ba? Shiyasa fa aka ce mu Roki Allah alherin da Yake wurin sa kaga Ubangiji ya karba ADDU AR ka yanzu ne zakayi Rayuwa Mai albarka tunda Allah ya Raba ka da janhuru.
Bai tanka musu ba don wannan maganar ta Yaya Rabi u jinta Yake kamar saukar Ruwan dalma a zuciyar sa
“Allah ya baka lafiya Amma Ina ganin Yaya Rabi u me zai Hana a fara nema mishi Mata wata kil ya warware da wuri don na kula har da kewa ke damun sa.
“Eh to ai ka San Halin sa tukuro Ni da zai yarda ma kawai ga jummai jarka Nan ta gidan Baba dauda kanin hajiyar mu ne na Isa nayi komai in har zai yarda.
Ya fada suna zuba mishi ido da son Jin me zai ce Amma Bai ce komai ba Sai ma takaici da ya kulle shi Yana tsaka da alhinin Rasuwar matar sa suke Masa wannan wulakancin? Shi yanzu akwai wata mace ne da zata burge shi,? Babu ita wallahi ko da Allah ya tsawaita Rayuwar sa to zaiyi ta ne daga shi sai Kaisar Amma ba wata mace ba.
“Kana ji dai Al Mustafa Yaya Rabi u zai shige gaba ya nema maka jummai jarka ta gidan Baba dauda kayi na am ko kuwa a saurara har ka fito daga asibiti?
“Don Allah Yaya tukuro ku fita a sabga ta ki barni da abinda Yake damuwa ta Ni nace muku Ina son wani aure ne? Duka Duka ko kwana biyar Amina batayi ba kuke min zancen aure? Wacece Kuma jummai jarka? To bana son ta Kar ku Kuma yi min zancen aure don Allah ku kyale Ni tunda na Rasa Amina ai Kuma na Rufe kofar aure Zan Rayu a Haka na har Ubangiji yasa na cimma ta Amma a yanzu Babu wannan a Gaba na.
“To shikenan mun daina Al Mustafa amma ai Zama ba zaiyi maka a Haka ba. Wai Amina da cikin Nan ta tafi ko kuwa ta haihu ne?
Tukuro ya Fadi maganar Babu azanci bare balagar zance,
Almustafa ya dube shi kafin ya yi wani murmushi mai ciwo ya gyara kwanciya Yana Fadin
“Sai yanzu ne ya kamata kayi min wannan tambayar Yaya Tukur? Hakan ya nuna min Baku halarci janazar Amina ba duk me yayi zafi? Har yanzu da baiwar Allah Nan ta bar muku filin duniya Baku saduda ba? A me duniyar Nan take ? Wallahi Bata Kai ko ga Aikin banza ba Amma Bawa ba zai Gane hakan ba sai Ranar da ya Amsa Kiran Ubangiji a Ranar ne zai Gane duniya Aikin banza ce Bata Kai ko ga wofi ba.
Ya juya musu Baya Yana barin su da bin shi da idanu suna ganin ya fara sabunta wulakancin sa .
Yaya tukuro ya yafito Yaya Rabi u suka fice zuwa kofar waje inda tukuro ke Fadin
“Kai Yaya Rabi u wannan Gayen fa ya fara Gallo wulakanci sabo gal a leda in muka bari ya mike Lau lafiya to zaiyi Mana mazaunin makiya a Ran sa Amma kafin hakan ya kamata mu Zaunar da shehe gu Daya don ya Gane ALLAH Daya ne.
“Me kenan tukuro? Yaya Rabi u ya tambaya a rude don ya San shaid’ancin tukuro ya wuce duk yadda yake Zaton.
“Mutumin Nan yaya Rabi u idan ya dawo Kan Doka da oda zai Gane mu a cikin Yan Uwan sa to gara muyi wani Abu na yadda zamu zaunar dashi gu Daya bani minti talatin zanje na dawo zaka ga abinda nake nufi.
Tukuro ya wuce da sauri ya bar Yaya Rabi u da Yi mishi Rakiya da idanu Yana tunanin me Yake nufi?
Bai Gane komai ba sai da mintuna talatin suka cika tukuro ya dawo dauke da wata kwalba Mai Kama da kwalbar injection wacce tukuro ya nunawa Alh Rabi u Yana Fadin.
“Ka ganta? To wannan itace zata tsugunar da mutumin Nan ta yadda zamu Zama sai abinda mukayi a kamfani.
“Ba dai guba kake nufi ba Tukuro?
Rabi u ya tambaya a Rikice.
“Haba dai ba guba bace kawai dai Dan sinadari ne Mai karfi .
Ya juya ya nufi office din Likitan Al Mustafa inda Yaya Rabi u ya Mara mishi baya don hankalin sa Bai kwanta da tukuro ba musamman da Bai Fada mishi kowane irin sinadari bane.
Likita Abu ammar ya bawa tukuro kujera ya zauna inda Rabi u Kuma Yake tsaye Bayan kujerar tukuro din.
“In ce dai ba jikin Mai gida ne ya motsa ba?
Cewar likita Abu ammar don yayi zaton ko jikin Al Mustafa ya tashi ne.
“Jiki fa da sauki likita sai dai wata allura ce da ake mishi a gida yace na dauko ta na kawo maka kayi mishi ita kasan Yana da ciwon gyambon ciki to Ina Jin ta gyambon cikin ce.
Cewar tukuro wanda ya mikawa likitan kwalbar injection din inda kuma Likitan ya karba Yana dubawa da son ya Gane ko ta mecece Amma sai ya ga ta allurar zazzabi ce kwalbar Amma kuma abinda Yake ciki yayi daban da kalar maganin da kwalbar take fitowa da shi idan ya fahimta daidai dai an juye maganin asalin da Yake cikin kwalbar an zuba want da son ayi dodon bango da kwalbar don gashi nan Alamar an bude bakin kwalbar Alamar dai akwai wata a k’asa.
Ya dire kwalbar Yana Fadin
“Amma Babu wani ciwo a yanzu da Yake damun sa sai shock da jimami Don a dazu na duba shi Babu komai sai shock in Sha Allah zai dawo normal ko kuwa Yana son ayi mishi allurar ne?.
Tukuro ya yi maza yace
“Eh to tunda yace na koma gida na Dauko allurar Yana son ayi mishi ita tunda shi kadai yasan yadda yake ji .
“Ok to Babu matsala ya fada Yana duban agogon hannun sa Yana Fadin
“Yanzu time din da Zan aje Aiki ne Amma Bari sai na Bawa Wanda zai Karbe Ni yayi mishi kawai.
Tukuro ya mike yana Fadin
“Babu komai likita bokan turai
Suka fice shi da Rabi u likitan Kuma ya dauki kwalbar Yana Kara duba ta inda yaji Yana son auna koma meye a cikin ta don Haka Yana fita sai ya zarce Lab ya bada kwalbar a auna mishi sai ga sakamakon abinda ke cikin kwalbar poison ne Wanda Yake tafiya Kai tsaye ga zuciya ya Mata illar da jini ba zai iya harbawa ba daga Nan kuma sai jiki ya dauka in da karar kwana Kuma sai tafiya.
Rabi u ya dubi tukuro Yana Fadin
“Meye hikimar hakan ? Kuma meye dalilin Hakan?
Tukuro yayi murmushi Yana Fadin
“Ka cika garaje yays Rabe bani Nan da zuwa gobe kawai Amsar ka zata bayyana idan kaga yaron Nan bugun zuciya na tsayawa kasan tafiya ta taho abinda Yake fata ne na bin Bayan matar sa kaga ya huta.
Na iso garin Jos cike da tunanin Al Mustafa don Haka ina isowa asibiti na same shi jiki yayi kyau Amma Kuma yanayin sa ya bani tausayi.
“Ibrahim Haka wannan kaddarar ta sauka gareni na Kuma godewa Allah Ina wa Amina fatan Aminci ko Babu komai tayi shahada ta Rasu sanadin haihuwa Allah kayi Mata Rahama ka yafe Mata Allah ka shaida na yafe Mata duk tsayin zaman mu Bata sab’a min a sane ba sai dai kuskure irin n Dan Adam Allah kasa tana cikin dausayin Aljanna tare da dukkan mumunai bayin Allah.
Tausayin sa ya Kama Ni matuka Gaya na soma bashi hakuri tare da nuna mishi I’manin kenan Bawa ya yarda Samu da Rashi Duka na Allah ne wata Rana muma za a wayi gari mun wuce Kuma babban tashin Hankalin Bawa Yana Nan a yadda ya mutu to Amina tayi mutuwar shahada ko Babu komai Kuma kayi Mata kyakkyawwr shaida ka Kuma yafe Mata Allah ma zai yafe Mata Ashe muyi fatan mun samu Mai kyau fiye da tata.
Haka muka kasance inda Kuma Al Mustafa ya cewa su tukuro su koma bakin Aikin su Kar a samu matsala tunda ya samu Sauki in Sha Allah yau ko gobe zai CE a bashi sallama.
Da Haka ya sallami su Yaya Rabi u da tukuro suka koma office da nufakar son daka warwaso su kwashi Rabon su
Malam Musa da ya iso asibitin a yau kwanan shi biyar a garin Jos don Haka yayi nufin tafiya gida shiyasa yazo ya duba shi
Kuka Al Mustafa Yake ganin mahaifin Amina shi Kuma sai magana Yake bashi tare da misalai na I’mani da kaddarar Ubangiji da Kuma matashiya Akan dukkan Mai Rai mamaci ne duk wanda ya mutu Kuma iyakar wa adin ne
Sunyi sallama da Mal Musa Yana mishi fatan alheri shi Kuma Yana zubar da hawaye
Da safe Al Mustafa na son ganin zuwan likita don ya nemi sallama sai ga likita Abu ammar Wanda yazo mana da abun mamaki na kwalbar injection din da tukuro ya kawo
Dr abu ammar ya dubi Al Mustafa Yana Fadin
“Hakika wadan Nan mutanen kayi hattara da su don sun nuna komai ma zai iya faruwa na Kuma auna Naga abinda Ruwan maganin Nan Yake nufi Wanda Yake tsayar da bugun zuciya to Kar ka yarda da kowace irin allura ce Haka Kuma abun duk da ya fito daga hannun su kayi nesa da shi Allah ya Shiga tsakanin ku ya tsare ka daga dukkan sharri
Al Mustafa yayi shiru Yana Rike da kwalbar Yana juya ta Ni kaina sai naji tsoron Yan uwan Al Mustafa Amma sai nayi ADDU AR Allah ya Kare shi daga dukkan sharri
Kwana biyu aka sallami Al Mustafa daga asibitin inda Kuma wata mace katuwa ta soma zuwa wurin shi da sunan taxo duba shi sai daga Baya na Gane Wai itace jummai jarka wacce su tukuro suke son ya aura .
Jummai jarka Yar duniya ce Mai Ido a bude Kuma katuwa ce ta sosai don tayi biyun Al Mustafa. Ta soma zuwa da wani irin salo na son Sai ta Shiga Rayuwar Al Mustafa Wanda yayi saurin taka Mata burki don da gaske Babu wata mace a tsarin sa a yanzu
Ranar da aka sallamo shi gidan nashi cika yayi da yan dubiya da gaisuwa har da su kawu garbati da ahalin sa duk da Baya gani kuma kana ce mishi makaho kaji tsifa da warwara
Sai ta ko ina aka Shiga yiwa Al Mustafa kyautar Mata Amma hankalin sa kaf Yana ga Kaisar Wanda tuni ya amsa Sunan sa Ranar da aka zana mishi suna a Ranar ne Kuma Al ya dauko Ni muka iso bauci ya dauki Kaisar ya Rungume Yana zubar da hawaye Aliya Kuma ta tausaya musu inda Al Mustafa ya fara yiwa Aliya kyauta da kujerar makka ya kuma Bata Kaisar Amana tace ta Dauka
Gatan da Kaisar ya samu mahaifiyar ce kawai ya Rasa Amma Aliya Bata barshi da komai ba Haka mahaifin sa Wanda ya lullube komai Akan Kaisar don ya Gama Gane Yan Uwan sa Kam dukkan kiyayyar da sukayi mishi shi da mahaifiyar sa Rabi to kiyayyar Kaisar ta dame ta kowa don Haka sai ya bar dangin sa da Fadar cewa Amina da cikin ta ta Rasu sai dai shi duk satin duniya Yana shigowa garin bauci ya duba Kaisar
Yays Rabe kuwa da ya matsa lambar sai jummai jarka ta shigo gidan Al Mustafa tuni jummai jarka ta Shiga ta Kuma fita da son mallakar Al Mustafa ko ta karfin tsiya ne shiyasa ake ta zaga mayakan Zaune ( bokaye da Mara’s tsoron Allah?)
Sai ya zama duk inda Al Mustafa Yake jummai jarka zata iso da tagomsshin kayan abinci ko na makulashe da nufin ta kawo mishi Amma daidai da Rana Daya Bai ji Yana son kusantar jummai jarka ba don Haka suka soma shiga taitayin su don kudin dai Kan sai narka su ake Amma Babu nasara Dole aka hakura Amma fa a can office din su tukuro da Rabi u babu abinda suke sai tafka mugun Abu don Haka Al Mustafa ya ce min a duba komai da Yake hannun su don Haka dubawa kuwa Bata zo da sakamako Mai kyau ba domin kuwa an tafka asara Mai yawa Babu kaso uku a cikin biyar don Haka sai Al Mustafa yace ya Zama Dole ya karbi kamfunna daga hannun tukuro da Rabi u gara ya sauya wasu tunda Haka suke so.
Nayi maza nace mishi
“Ba Haka za ayi ba Mai gida Kar ka karbi komai daga garesu ka bar su Rike da kamfunna Amma hikimar da zakayi ka bar zuba komai naka sai dai su juya abunda yayi saura a kamfanin in yaso tunda Basu San da kamfunna Lagos ba ka mayar da komai can Lagos tunda Wanda baka Sani ko ka hada jini da su ba sunfi wadan Nan din tunda su dubi Ribar da suka kawo ? To tunda warwason dukiyar suke abunda yayi saura ma zaka neme shi sun kwashe kaga idan suka karar da komai ai Babu abunda zaka ce musu tunda sun karar da komai Amma yanzu kana cewa ka Karbe komai daga su sai a fara ga zance ga magana Amma yi kamar baka San suna yi ba Ranar da suka karar da komai sai ka siyar da kamfunna ka Kara siyen wasu a wani wurin in son samu ne ma a bude a bauci can ma muga irin nasarar da garin namu zai kawo.
“Hakikatan kayi gaskiya ibrahim na Kuma gode da wannan shawarar Haka ya kamata in na fidda su a yanzu komai ma zai iya faruwa Amma idan duniya ma ta shaida sune suka karar da komai Babu Mai bakin magana. Nagode sosai da wannan hikima taka bar su kawai suci Karen su Babu babbaka.