Skip to content
Part 9 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Mamaki bai bar mutanen nan ba sai faman neman tsohon nan suke a dakin asibitin amma da suka tabbatar da babu shi dole suka hakura suka fito jiki a sanyaye kowa na fadin albarkacin bakin sa.

Jiki a sanyaye daddy ya  biyo bayan su shima don wucewa gida amma sai yaji daya daga cikin Wanda suka kawo tsohon yana fadin, “Yo ku ai ga tsohon nan can a bakin kofar yaushe ya iya motsawa har yazo nan? Daddy ya jiyo da sauri inda mutumin ke nuni da hannun shi inda ya hango tsohon zaune akan dandamali. Da sauri suka nufe  shi da mamaki suna fadin, “Baba ya kazo nan ka zauna baka tsaya an gyara maka ciwon ba?

Ya dube su yana murmushi kafin ya ce “ku yi hakuri bayin Allah ai bana son maganin asibiti ne shiyasa na tafi Amma har na tafi dana yace bai kamata na taho banyi muku godiya ba har da bawan Allahn da ya biyo ku don taimako na shiyasa ma na dawo. Nagode muku Allah ya gode muku kaima alh iro nagode maka Allah ya biya ku.

Suka cika da mamaki musamman alh iro amma kafin su fita daga wannan mamakin ya kuma shayar da su wani mamakin ta hanyar juyaww ya wuce abin shi har ya karya kwana. Alhaji Iro cika da mamaki bare kuma wanda suka kawo shi da suka tabbatar da a some suka kawo shi amma wai har ya iya tashi wai har yaje gida ya kuma dawo.

“Muje mu kai shi gidan shi babu adalci ace an barshi ya koma shi kadai.

Da sauri Alhaji Iro ya fita daga asibitin sauran ma suka fita don daukar shi amma suna fita ko mai kama da shi basu gani ba duk da doguwar hanyar da bata da kwana bare lungu sama ko kasa babu tsohon babu dalilin shi.

Daddy tafe a mota yana mamaki musamman rashin kirkin Nadiya na banke mutum kuma ta wuce abinta yanzu inda an Kone ta kamar yadda matasan nan suka so me yafi wannan?

Yana zuwa gida ya haye saman sa bai tsaya a falon ba yayin da mama ta kula kamar ba daidam yake ba don haka ta bi bayan shi a saman benen. Ta tura kofar dakin ta shiga tana fadin, “Daddy lafiya kuww naga kamar akwai wani abu a tare da kai?

Ya cire hular ya ajiye ya kuma cire babbar rigar sa yana fadin

“Aliya wannan yarinyar bata tab’a bata min rai irin yau ba. Ta dube shi tana fadin

“Wacece?

“Wacece banda Nadiya? Haka yarinyar Nan take gudu a mota? Kuma ta banke mutum amma ko a jikin ta? In har haka take tuki Anya bata yi sanadin kashe rayu ka Da yaww ba? Anya banyi gangancin bata mota ba? Na soma Jin wani Abu mai kama da nadama wulakancin yarinyar nan ya soma damu na.

“To Daddy ya za ayi? Ayi addu’a sai dai gaskiya a san abinyi ba zai yuwu a barta hakan ba dole a dauki mataki.

“Ya zama dole kuwa Aliya ya kwashe komai da ya faru na bankar da Nadiya tayi ta kuma gudu da biyowar da matasan sukayi mata zasu kone motar ta.

Haj Aliya ta rike baki cike da takaici ta kasa cewa komai sai mamakin halin nadiya da ya gama isarta.

“Allah shi kyauta. Abinda kawai ta iya cewa kenan ta mike ta sauka kasa inda ta iske nadiya na zagin Ade wacce ta saka ta dafa mata ruwan zafi.

“Shegiya matsiyaciya ni zaki bawa wannan abun kamar zaki bawa uwar ki? meye wannan kamar an wanke kan uwar ki? Ta kyarawa Ade tafasasshen ruwan zafin a jikin abinda ya saka tsohuwa Ade sakin kara saboda konewar da fatar ta tayi.

Ade tsohuwa ce wacce ta girmi haj Aliya ma in ma bata heife ta ba amma Nadiya bata kunyar kuxa mata ashar wani lokacin ma har da mari.

Hajiya Aliya ta kame cike da tsoro ganin yadda jikin Ade ya kwaile ta sale tun daga sangalalin hannun ta har zuwa kafadar ta da wani sashi na fuskar ta ya zama farar fatar kunar wuta.

Ade sai kyarma take irin ta kaduwa da tsoro ga kuma radadin ruwan zafi yana ratsa ta. Jin karar da ade ta fasa ne yass daddy fitowa daga dakin shi inda yaga abinda ke faruwa jikin Ade ya kone nadiya kuma sai auna mata asher take shima sai ya daskare kasa motsi kamar yadda haj Aliya tayi. Fati ce ta taho da sauri ta kama Ade tana fadin, “Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un haba Nadiya ya zaki zubawa tsohuwar ruwan zafi don Allah? dubi yadda kika kone ta don Allah? Da sauri Nadiya ta kifawa fati mari tana fadin

“An kone ta din shegiya matsiyaciya idan uwar ki ce ki rama mata Ni da gidan uba na ta nemi Yi min Isa da gadara na kasa nuna mata iyakarta na almajirar gidan mu?

Da sauri Haj ta sauka daga kafar benen tana kama Ade da jikin ta yake ta b’ari saboda tsoro da raza na tana fadin, “Fati dauko makullin motar ki mu tafi asibiti Yi sauri don Allah.

Da sauri fati ta dauko makullin motar suka fice da Ade wacce hawaye ya gama wankewa fuska. ba kukan kunar wuta ne dalilin hawayen ta ba sai zagin da yarinyar nan tayi mata wacce ko a jikoki tayi ta goma sha da ita ita kam me take nema a cikin wannan aikin da bazata bar shi ba? amma albasa ce batayi Harlin ruwa ba.

Alhaji Iro ya koma dakin shi yana yana laluben mataki don ba zai yuwu ya bar yarinyar nan tana wannan wulakancin a rayuwa ta yayi zaton abinda take kuruciya ce zata bari amma Al amarin nata kullm sai kara lalacewa yake. Kwanaki uku Ade na kan gadon asibiti yayin da fati take tsaye akan ta har aka basu sallama suka dawo gida a ranar ne kuma Ade ta tattare kayan ta ta isko mama a falo ta duka tana fadin,

“Haj zan koma kauyen mu jama are don Allah ki yafe mini idan na tab’a sab’a miki na hakura da aikatau .

Mama ta kamata tana fadin

“Ban san da wane baki zan baki hakuri ba Ade na kuma san abinda akayi miki ne yasa zaki tafi amma don Allah kiyi hakuri kar ki tafi tunda ba ni ko mai gidan nan suka kore ki ba Ade nayi Miki alkawarin irin haka ba zata sake faruwa.

“to haj ba zanyi Miki gardama ba saboda na san da kana haifar mutum ka haifa mishi hali da yarinyar nan ba ta  zama yadda ta zama ba amma Allah ya sani na gaji da hadiyar wulakancin ta tunda Allah bai wulankata ni ba don ina Aiki ne yass take min hakan.

“Ba zan bari ta kuma ba Ade nayi miki wannan alkawarin kiyi hakuri don Allah ni kam bana son rabuwa da ke .

to shikenan haj nayi hakuri .

Mama ta kama Ade ta Kai ta har dakin su ta kuma tsaya akan ciwon ta har ta samu sauki kuma tunda Nadiya tayiwa Ade wannan wulakancin babu wanda yace Mata ko uffan tsakanin mama da daddy bare suce Mata baki kyauta ba ko kar ki kuma

Motar kirar high land ta shigo cikin gidan alh iro GIDAN KUDI inda aka bude mata kofar get ta sulala tamkar macijiya . Katuwar mota ce irin ta masu kudi irin su iron

Sulele ya fito daga motar ya mayar ya rufe ya nufi cikin gidan inda mama da fati da nadiya suke zaune a falon fati tana yankewa mama farce yayin da Nadiya kuma take cattin da wayar ta sulele ya shigo da sallama mama ta amsa tana fadin

“Kai sulele mai motoci kwana da yawa .

Ya zube a gaban mama yana gaishe ta  ta amsa tana tambayar shi ya kasuwa yace  sai godiya ya mika mata key din motar yana fadin

“Haj ga key mai gida yace a kawowa daddy jiya aka gama hada ta yace a bashi hakuri tun shekaran jiya yaso a kawo ta amma don ya tabbatar da lafiyar ta yasa ba a kawo ba.

Haj ta karbi key din tana fadin

“To zan fada masa in Sha Allah sulelen male na yaro dogo.

Mama ta Kare da zolayar sa don duk motocin gidan wurin su ake siyen su

Yayi murmushi yana mikewa da shirin tafiya haj taja jakarta ta fito da kudi tana bashi sukayi sallama inda Nadiya ta karbi key din tana fadin

“Mota ta iso  dama na san Daddy ba zai wuce week din nan ba zai sauya min wata don waccen dai wallahi na gama da ita ko an sauya mata gilasai ba zan kuma hawan ta ba gara ya kyautar da ita ko can misau a bawa alabo ita tunda uban shi ya gaza siya mishi mota kullum sai ya roki daddy a siya mishi mota kai tsiya dai batayi ba wallahi .

Fati ta dago tana fadin

“Ai ba tsiya bace samu da rashi duka na Allah ne ni da na san yaya alabo yana son motar ai da tuni na bashi tawa.

“A gidan uban wa ta zama taki? daga aro shikenan har ta zama taki? to ai kin san nan ba gidan uban ku bane ki bari sai gidan naku sun siya miki mota da arzikin su sai ki bayar amma nan ai kin san gidan mu ne kuma cin arzikin kike in ma kika bayar da motar nan sai kun biya ta wallahi.

ta dauki key din motar tana fadin

“Bari magani babbar harka daddy ya dauko min ko wacce za aji kunya?

ta fice mama ta bita da kallo bata ce musu ko uffan ba sai ma hawaye da taji yana bin gefen fuskar ta amma cikin hikima ta share su ba tare da fati ta gani ba.

Katuwar mota wacce ta zarce ta daddy da mama ita nadiya ta gani fara tas mai manyan tayoyi da bakaken gilasai don haka sai ta dakka tsalle tana shafa motar kafin ta bude ta shiga tana Yi mata key

Yadda karar motar yake fita a slow shi ya tabbatar mata da girman motar don haka sai ta taka ta ta zagaye shatale talen da yake tsakiyar farfajiyar gidan ta sha kwana ta mai do motar ta ajiye tana nemo keena a waya tana fada mata motar da suka gani a aljaxeera gata daddy ya siya Mata su jira ta zata zo su fita .

tana fitowa ta nufi dakin kaisar wanda yake zaune shi da king da wani abokin king din mas ud sai kawai ganin Nadiya sukayi ta shiga babu ko sallama tana fadin

“Kai zo nan ka wanke min mota zan fita yanzu minti sha biyar na baka idan baka kammala a minti sha biyar ba wallahi sai na sallame ka ka bar gidan nan tunda na lura ka soma zama dan iska sai kace ka manta da matsayin ka na house boy ko don kaga an kawo ka nan na bari an dauke ka shine kake jin kan ka a wani shege wata tsiya? to tashi da  sauri  ka wanke min mota wallahi ka wuce minti sha biyar sai ka bar gidan nan ka komaww fakiran iyayen ka matsiyaci da kai kawai.

ta jefa mishi key din motar ta juya abinta yayin da king da mas ud suka shiga kallon kallo Wai akuya kallon kura saboda jin irin wannan wulakancin marar tsarki.

“Wacece wannan?

cewar mas ud wanda yayi tambayar a fusace

“Yar gidan ce

cewar king wanda yayi k’asa da kanshi yana Jin ba zai iya jurar wannan wulakancin ba ko waye uban yarinyar nan matukar shi tayiwa hakan zai nuna mata kuskuren ta sai dai ya san kaisar ba zai iya nuna kwanji ba tunda zuciya ta mika mata kambun sarautar so.

“Dama aiki kake a gidan nan ?

cewar king Wanda ya rutsa kaisar da ido.

Kaisar ya mike yana daukar key din yana fadin

“To king ai dole nayi musu aiki tunda ba gidan mu bane? ko ba aiki nake ba zan kasa yiwa ya’yan gidan da sukayi ana alfarma?.

“Ba dai zaka wanke motar ba kaisar?

cewar mas ud.

“To me zai hana mas ud? In ta Kore ni kamar yadda tace fa?

Ya dauki key din ya fice da sauri ya barsu da bin shi da kallo suka mike suka rufa mishi baya don ganin da gaske wankin motar zai yi?

<< Azurfa Da Zinari 8Azurfa Da Zinari 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×