Skip to content
Part 92 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Aliya ta Kara kaduwa Jin wannan zance na wanna mutumin Wanda mahaukaciya ta fafaka da duwatsu tabi shi a guje inda Kuma Aliya ta mike da sauri zuwa mota muka ja muka tafi kafin ta juyo kanmu.

Muna tafe Aliya tana kallon yarinyar Nan tana zubar Mata da hawaye har muka iso bauci ta siya Mata Madara da kayan Yara muka iso gida ta hada Ruwan zafi tayi Mata wanka ta dama Madara ta Bata  aka Kuma yanke Mata cibi yarinya ta Zama mutum sosai sai bacci ya kwashe ta.

Ko da mahaukaciyar Nan ta dawo Raka wancan mutumin da jifa sai taga Babu Yar ta sai ta soma dube tana Fadin

“Ina yarinya ? Ina yarinya?

Sai ta soma guje guje tana neman yarta Amma Bata ganta ba Dole ta koma ta zauna tana sambatu in Kuma ta tuna da yarta ta mike a guje tayi Nema har dai ta manta da babin ta.

Kwalo ya shigo gidan tukuro Yana Fadin

“Kai mutumi na wallahi fito kaji kayan ka ta haihu yanzu na biyo ta hanyar na ganta da jaririya wacce kana kallon ta kasan yarka ce.

Shaid’an ya mike Yana Fadin

“Kai kwalo da gaske kake?

“Ba na fada maka dama yarinyar Nan ciki ne da ita ba kace ba Haka bane? To Yasin ta juye shi baby girl na Nan sai dai fa Naga tana nuna hauka akan ta don Naga ta kaita cikin Rana ta ajiye tayi tafiyar ta Saman bola tana tsince tsince.

Tukuro ya kunna wiwin sa Yana Fadin

“Can Allah zai kawo Wanda zai dauke Yar Ni Kam Ina son yarinyar Nan Dole tasa na kyale ta dubi inda ta kwartsa min rotsen dutsi Haka  na taho jini na mini yoyo har da dinki kuma bana ko shakka abinda nayi Mata ne ya sa ta wannan rotsen shiyasa ma ban Kuma komawa ba Amma tashi muje kwalo na Kai Mata abunci kafin tayi arba in mu mayar da mahaifa don ba Zan iya kyale ta ba .

Kwalo ya tare shi Yana Fadin

“Ka Rufawa kanka asiri In ba so kake duniya ta Gane Kaine Wanda Yake haikewa matar Nan ba in wata gareka ma gara kawai ka kaita gidan masu hankali ko ka nema Mata magani ta warke sai ka aure ta kawai.

“Ba Zan iya auren ta ba kwalo don Ni Babu ajandar aure a tsari na yanzu  me na Rasa ga Mata ne da Zan jawowa kaina Aiki Wai aure? Meye a cikin auren ban da ciwon Kai da dorawa Rai damuwa? Barni kawai Naga wacce tayi min na biya ta na kawo gida in na kashe fitilar na sallame ta  da kudin ta .

Haka shaid’an ya dauki kwalo suka tafi inda mahaukaciyar Nan take amma Basu Tara’s da ita ba Dole suka dawo tukuro na Fadin ko dai Yan uwan ta sunji labarin ta haihu ne suka biyo suka dauke ta? To Allah dai masani

Al Amarin Ubangiji sai y zamo a yanzu Ya’yan Marigayi Alh Sani ne suke Kan Sharafin su arziki ya yadu sosai wato Salim da muhd da Mai Sunan malam. Sai suka zamo kamar yadda Uban goyon su ya zamo wato Al Mustafa. Suna taimaka wa matuka Gaya musamman ga Yan Uwa da Kuma mabukata har da tunawa da marigayi Al Mustafa shima da kason ADDU AR da suke sakawa ana mishi duk juma tare da iyayen su alh Sani da Dija wacce Bata da Rabon ganin wannan Rahamar wacce Al Mustafan da ta Raina ne ya zama ja gaban ta

Alh Rabi u da su Haj kaltume Kam a inuwar bayin Allah suke su Salim Wanda basa Rike Sharri sai Ramako da alheri dama Haka ake son mutum ya zama ya manta sharrin da akayi mishi Amma Kar ya manta alherin da akayi mishi shiyasa ma suke ta gaba Gaba.

Shekaru suka tura lokaci zuwa lokaci Ina shigowa Jos don ziyara ga kashewar Al Mustafa har wata Rana na biyo ta makarantar da mahaukaciyar Nan take kwana na Kuma tambaya ko tana Ina? Ake sanar min wallahi Babu Wanda yasan inda take Amma wasu sunce sun ganta a garin bauci wasu kuma suka ce Gombe suka ganta to Allah dai shi Kadai ya barwa Kansa Sani

Aliya kuwa ta Rike yarinyar Nan tamkar itace ta tsuguna ta Haife ta don tana cika kwana bakwai da dauko ta tace a Rad’a Mata suna inda ta zaba Mata sunan Nadiya aka Kuma yanka Mata hakikar suna.  Aliya tana son yarinyar ta Nadiya Kuma na santa da son Yara Amma son da take musu baya Hana ta Basu cikakkiyar tarbiya don Haka bani da haufi Akan Aliya tun daga Kaisar har alabo da shima Yake karatu a waje shima na kaishi don alabo nawa ne Yaya halilu ma yace nawa ne Halal malal

Shekara biyu cur na je duba Kaisar na kuma same shi cikin nasara da koshin lafiya don makarantar da Yake su ne suke kula da Rayuwar Yara kasancewar garin misra na yarda da musuluncin su da Kuma tarbiyar su . Kokari sosai Kaisar Yake a karatun Boko da na Islamic ya Kara Wayo sai dai Yana Nan Babu kiba sai Hankali da nutsuwa Kai da ka ganshi ka San lallai jinin Al Mustafa ne Kuma jikan Rabi baiwar Allah

Duk karshen shekara nake kaiwa Kaisar ziyara na kuma biya kudin makarantar sa da abinda duk Yake so Wanda yake bugo min waya ya fada min wani lokacin Ni da Aliya muke zuwa wani lokacin kuma Nazo Ni Daya Amma duk zuwan da muke da Aliya Bata tab’a zuwar mishi da Nadiya ba Bai kuma San labarin ta ba.

Shakarar Nadiya hudu a hannun Aliya Allah ya azurta Aliya da ciki Wanda mu Duka bamu San da bayyanar sa ba sai da ya Shiga wata na biyar

Munyi murna ba kamar Aliya da tayi ta suduja ga Ubangiji Ni Kam na San farar zuciyar ta ne Allah ya duba yayi Mata wannan baiwar . Allah ya Bata hakuri da juriya ta Rike Ya’yan da ba nata ba bil hakki Bata tab’a damuwa da ita Bata samu ba sai gashi Allah ya dube ta da Rahamar sa . Allah ka dube mu da Rahamar ka muma don mutuncin manzon Allah

Lokacin da Aliya ta haihu sai Yaya Hajara tace Allah ya kashe ta ya bunne yarta ce Aliya ta Haifa tunda ita Aliya kowa ya San Nadiya ce Yar da take so kamar me? Don Haka Yaya Hajara itace ta sakawa Fati suna Kuma da ta Isa yaye Aliya ta Mika Mata ita ta yaye ta a Hannun ta sai dai ta Kan kawo ta lokaci zuwa lokaci Amma Bata jimawa don ita kanta fatin tafi sabawa da Yaya Hajara duk da tana son zuwa wurin Mama wacce Bata nunawa Fati komai ba sai kulawa wacce take irin ta da da mahaifi. Sai dai kuruciyar Nadiya an Sha fama da ita Domin kuwa tun tana Yar kususuwar ta ta iya gori da tsiwa. Da Rashin ta Ido duk kokarin Haj Aliya na saita ta Amma batayi nasara ba Ashe yarinya jinin Uban ta ne ke gudana a tare da ita.

Ganin yanayin kuruciyar ta ne ya Hana na kaita waje karatu Amma naso hakan ita da Fati Amma na Gane idan nayi hakan kuskure ne babba tunda a gaba na ma Nadiya tana tsanar Fati da Mata gorin talauci da nace musu Amma na zaci kuruciya ce zata daina Ashe tun ran gini tun ran Zane. Halin Al Mustafa ne na son Yan Uwa ya tabbata ga Kaisar Wanda yaso Nadiya bil hakki itama jinin Uban ta na bakin Hali da mugun Abu yasa ta kasa yiwa Kaisar Al farma duk d yafi karfin ta a matsayin sa na ZINARE ita Kuma AZURFA.

Na soma fama da takaicin yarinyar Nan tun daga Yan Aikin gidan Nan daga wanda zata zage tas Babu Ruwan ta da tsufan mutum zata zage shi tas wani ma in ta Raina shi hat da Duka . A Nan kam Aliya ta soma nadamar abinda tayi Amma Ina ta Bata hakuri da yiwa yarinyar Nan uzuri . Ashe zata bani Mamaki fiye da Haka . Zuwan Kaisar da abubuwan da suka biyo baya duk Mai sauki ne akasin mugun Aikin da yarinyar Nan tayi na son kashe Dan gidan distinguish Mukhtar Biro gashi Wanda su dyka kuruciya ce ta hada su Yana son ta ita kuma tana takamar gadara da Uban ta wani ne shima Yana takamar nashi Uban wani yasa a dauko mishi ita don ya nuna Mata iyakar ta ita Kuma ta soka mishi wuka har muna zaton ya mace uban sa kuma yace Bai yarda ba akayi ta tafka Shari a har aka Yankee Mata hukuncin kisa Amma yaron Nan Kaisar yayi Uwa yayi makarbiya ya wanke ta da hikimar shi ya fanshe ta a kisa abinda ya kusan yin ajali na don Ina ganin banyiwa kaina adalci ba idan na Bari aka kashe dan Al Mustafa musamman da na san Yadda Uban sa Yake son sa Da irin Amanar sa da ya bar min. Ashe Allan Bai nufi akashe Kaisar ba har Allah ya Tayar da Dan gidan distinguish Mukhtar Biro Wanda doguwar Suma ce yayi Amma Allah ya aikowa Kaisar mafita Amma abinda ya bani Mamaki duk wannan sadaukarwa da Kaisar yayiwa Nadiya ta Rayuwar sa Wai Bata ji ko godiya ya kamaci tayi ba sai ma da yace Yana son auren ta tace tafi karfin matsiyaci fakiri irin sa abinda Bata sani ba dukiyar da take homa da takama ta Kaisar ce Ni din da take gani ban mallaki wani Abu da zatayi homa da Barazana ba arzikin da take gani na gidan su na Kaisar ne . N jima Ina Mata Hannun ka Mai sanda da cewa ita AZURFA ce Kaisar ZINARE ne Amma da Yake mahaukaciya ce da tayi gadon hauka a uwar ta Bata gane hakan ba. Ban San yarinyar nan zata Shayar da Ni bakin ciki Mai yawa ba sai da ta kalawa Kaisar Sharri Wanda Banda Allah da yanzu an Rufe babin sa sai Kuma yarsa da taso kashewa ta jefa a tanki ta Kuma tsallake k’asa ta tafi ta Shiga gasa a can ne Allah ya nuna mata iyakar ta ta fada hadari har ana Shirin yake Mata hukuncin kisa Amma ta game da wannan yaron Dan gidan distinguish Mukhtar Biro Wanda shi kuma suke son wata dama a kaina da zasu karbi Yan buyun Nan shine ya fanso ta yazo da ita Wai ni din na fanshe ta da Yan biyu Bai San ni din na zo dab da inda zan kai Nadiya can dab da garin Jos na ajiye ba sai gasu Wai anzo in Ina son ta na bayar da su Sha aban to har abada  Ramadan sun haramta gareku ba zan iya bada su sai dai kuje da Nadiya kun Kuma ji ko wacece a wurina kema kinji kowaye Kaisar a wuri na don har zargin neman jinsi yarinyar nan tayi min wai Ina neman Kaisar Bata san cewa Kaisar uban gida na ne ba Kuma Uban gidan ta wannan shine farkon farawa da kuma abinda Nadiya Bata sani ba da tabi abinda nake so da har duniya ta tashi b zata tab’a sanin wannan labarin ba amma dole ne na fito da shi ko don Fati da ita kanta Nadiyar da wannan yaron abdulhameed da Uban sa  na Kuma Sanar sai kuje d Nadiya ku Rike ta ko ku mayar da ita baiwar ku tayi muku Aikin kudin ku .

Nadiya ce ta toshe kunnuwan ta tana zubar da hawaye tana fadin

“Daddy? Nice Yar mahaukaciyar nan? Wannan shaid’an din da yake bibiyar ta da son ya lalata Ni  shine Uba na kenan? Na Shiga uku na lalace Ashe duk abinda nakewa Fati nice ya kamata tayi min amma ban sani ba? Da wane idon zan dubi mama? Da wane idon duniya zata kalle Ni? ni kam a yau Daddy ban Kai matsayin AZURFAr da ka kaini ba. Daddy Dole ma na matsa daga gareku domin kuwa na zame muku annoba.

Kaisar ya mike Yana Fadin

“Daddy? Shaid’an din da ysso kashe mahaifi na shine Uban yarinyar nan da nayiwa soyayyar mutuwa? Daddy in na fahimta ma yarinyar Nan daga tsatson ahalin da suka cutar da mahaifi na suka cutar da kakata Rabi ta fito? Wallahi ko ban sake ta a baya ba a yanzu zan sake ta.wallahi na tsani yarinyar Nan na so ta ne Daddy da zaton jinin ka ce . Na wulakanta Fati da take min soyayyar gaskiya ina ganin yarka ce kswai ta dace dani . Daddy Nadiya ta bar gidan nan in ba haka ba wallahi nine ajalin ta Daddy har uban yarinyar nan sai na nemo shi don Sai na daukarwa mahaifi na fansa.

Nadiya ta dubi Kaisar tana zubar da hawaye tana fadin

“Zan so Kaisar ka zamo ajali na domin kuwa Ni da Wanda ya ke Amsa sunan Uba na mun maka abinda zakayi mana komai ma Ni da kaina Kaisar na san na cancanci kisa daga gareka Ashe ma jinin mu Daya.

Ya yi saurin daga mata Hannu yana fadin

“Har abada Babu jini a tsakanin mu ko da akwai shi na Raba shi kiyi maza ki bar nan in ba haka ba kuwa nine ajalin ki.

Distinguish Mukhtar Biro ya mike yana fadin

“Yanzu kudin da yaro ya kashe wurin fanso yarinyar Nan Yaya za ayi kenen?

Ya fada yana duban Daddy iro.

“To biro ba kace in ban Baku Ya’yan ta ba Zaku Rike ta har sai na Baku Ya’yan ta? To kuje da ita ai kaji dai irin jihadin da nayi kaji Kuma irin sakamakon da tayi min. ? To na bar maka Nadiya in kaso ka aurawa Dan ka dama nacin da yake kenan .

“Allah ya sauwake na aura mishi Yar mahaukaciya ai Kuma ko Mata sun kare abdulhameed ba zai auri yarinyar Nan ba Kai dai da kayi jihadin kaci Gaba da yi Amma yaro fa sai an biya shi kudin da ya kashe.

“Ka kaini kara sai na karbi sammaci tunda Dama mun Riga da mun saba .

Distinguish ya fuce yana kumfar baki yayin da Abdulhameed ya mike shi kam baiji Yana k’in Nadiya ba sai ma wani sabon son ta da Yake ji shi kam Yana son auren ta a hakan ma ai shi real so Yake mata.

Yabi bayan uban sa  yayin da Kaisar yake kuka Yana tuna wannan labarin na Daddy Ashe haka mahaifin sa ya sha wahalar Yan uwan sa? Ashe haka kakar sa Rabi tasha wahala a haular su?.

Nadiya ta mike cike da tashin hankali tana zubar da hawaye a yau din ta zama abin tausayi matuka gaya  tana Fadin

“Daddy? mama ku yafe mini don Allah ku yafe mini. .Haka kukayi jihadi a kaina Amma na Zama.

Tayi ta maimaita kalmar a yafe mata din tana tafiya da baya da baya har ta juya ta fice da gudu daga gidan inda Yaya halilu ne yake fadin.

“Kai kar fa yarinyar nan taje tayi wani Abu marar kyau ku kiro min ita don Allah.

“Kyale ta Yaya halilu duk inda zataje ma taje.

“A a iro ai abinda ya wuce ya wuce kunyi abinda kukayi don zatin Ubangiji to kar ku zubar da ladar ku Aliya ku Kira yarinyar Nan kafik tayi mugun Aiki.

“Yaya halilu ni yanzu matsalar alabo itace gaba na tunda na gama gane ladidi tayi mishi sihiri ne to in sha Allah kuwa ba zata ci nasara ba auren Fati da Alabo dai ya lalace don haka zanyi madadi da Fati Yaya halilu ba zanyi muku fin karfi ba amma tuni na gama zana Fati a muhallin Kaisar don na San itace kawai daidai shi don Haka Fati tana hattama idda zan aura Mata Kaisar alabo Kuma Ni na San yadda Zanyi mishi dama haka Allah ya shirya Ina fatan Ranku ba zai baci ba.

Yaya Hajara tace

“Kayi mini daidai iro wannan yaron fa ko da asiri to da Halin sa gara Haka ni da ka bar shi ma ya auri ladidin Naga tsiyar da zai tsinta a auren nata .

“Ba zai yuwu ba Yaya Hajara in na barshi ai na cuce shi allah kadai yasan irin makircin da aka shirya mishi .

Kaisar ya sunnar da kanshi kasa yana fadin

“Daddy banyi farin ciki da abinda ya faru da su Fati ba Amma me yasa tun farko Daddy baka sanar Dani Fati ce yarka ba? Na Rantse maka da girman Allah da Fati ce matata Amma na dauka Nadiya ce taka shiyasa na zabi nayi Mata komai don darajar ka amma a yau ba zance banyi Farin ciki da auren Fati da ka bani ba sai dai ba xan so Baffa Halilu yaga .

“Kaisar ai kai da alabo duk daya ne a wuri na Kuma Ni hakan ma yayi min dadi tunda har yaron nan ya iya zuwa gaban Dan uwa na ya bashi takardar sakin yarsa kana zaton Yana da wani sauran girma a wuri na? Nima da iro zai yarda sai nace ya bar Alabo da wacce ya zaba kawai.

Cewar Baffa Halilu

Fati kam tana a tsakanin damuwa da bakin ciki. Ba komai take tunawa ba sai Rayuwar da suka shimfida ita da alabo har da albarkar yaron su amma wait yau ta zama labari .alabo mijin kaddara ne amma kuma ta san ya so ta ya Bata kulawar da yayi wani irin samun wiri a zuciyar ta  tuni ta Rufe babin soyayyar Kaisar a ranta ta rungume mijin ta amma Allah ya saka musu wannan zaluncin da ladidi tayi musu .

A Haka su Baffa Halilu suka wuce Misau inda aka bar Alabo nan gidan Daddy iro tare da fati wacce take kula da Halifa da Siyama yar Nadiya yayin da Yan biyu Kuma syke wurin Haj Aliya.

Tafe Nadiya take tana kuka . Sai a yau ne ta tabbatar da akwai bakin ciki a duniya. Ashe Gayen Nan da yake bibiyar ta Uban ta ne basu Sani ba? Shine ya haikewa mahaukaciyar uwar ta har yayi Mata cikin ta? Lallai ta gaji shaid’anci shiyasa ta zama abin da ta zama Amma kuwa shine zai shaida Aikin shaid’ancin Don ya haifi wacce ta Fi shi shaid’ancin.

Kai tsaye Nadiya ta zarce hostel din su keena inda Kuma ta Samu keena Rike da mujjallu na showing up Venus da Nadiya tayi.

<< Azurfa Da Zinari 91Azurfa Da Zinari 93 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×