Skip to content
Part 99 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ranar da aka daura auren sumayya da Abdulhameed a Ranar ne kuma Baffa Usman da Baffa Abu suka dauko ta a mota zuwa gidan Yayan su Mukhtar inda Haj laila ta Karbe su da mutunci tana sauke musu Ruwa da lemu kafin Usman ya nuna Mata sumayya Yana fada Mata auren su da abdulhameed aka daura in Yaya Mukhtar yazo ta sanar mishi kome kenan zai iso daga baya.

Suka barta cike da mamaki ta dafa sumayya dake cikin jar lafaya tana Fadin

“Masha Allah sumayya Allah ya tabbatar da alheri ai dole ne ma muyi Shirin shirya muku dinner taso muje daga ciki Amarya guda da zaman dab da inda za a ganta?.

Suka wuce uwar dakin Haj laila tana sauke mata kayan tabawa tana tambayar kawayen Amarya ita kuma tana sanar mata abun yazo ne Babu zato shiyasa bata gayyaci kowa ba.

Zuwa yamma sai ga Nadiya itama an lullubo an kawo ta gidan distinguish Mukhtar Biro mamaki ya cika Haj laila wacce ta karbi Nadiya da mamaki ta kaita daki inda sumayya take kafin ta Kira Abdulhameed ya iso take fada mishi abinda Yake faruwa .

“Alhamdulillahi momy ki taya ni murna nine yau Allah ya mallakawa mata biyu ina godewa Allah ya bani ikon Rike su bisa adalci yasa zan iya ya Kuma iya mini me ake so a kawo ne momy?.

Ta zuba mishi ido tana Fadin

“Babu komai ina dai tunanin yadda uban ka zai karbi auren nan naka .

“To momy ya ya zaiyi ? Nine mai yi kuma Ina yi. Sumayya yar uwa ta ce Nadiya kuma bugun numfashi na ce kowace tana da matsayin ta a zuciya ta .

Motar distinguish ta iso gidan daga Abuja yake wurin zaman mitin din su na siyasa sai yanzu ya iso inda kuma yayi Karo da Yan matan biyu Nadiya da sumayya Amma yafi Jin takaicin ganin sumayyar don kuwa da gaske ko ahalin Sufi baya son gani .

Suka zube su duka suna gaishe shi amma shi laila Yake kira wacce ta taho da sauri tana Fadin

“Sannu da zuwa.

Bai Bari ta karasa ba ya katse ta yana fadin

“Kema duk cikin Rainin da kikayi min ne kika gayyato min ahalin Sufi gida na? ban gaya miki ko kwanon gidan Sufi bana bukatar gani a gida na ba shine har kike kawo min Ya’yan sa masu kama da k’iri k’u?.

“Kayi hakuri amma ni ban raina ka ba su Usman ne suka kawo sumayya suna ce min auren su aka daura da Abdulhameed ita sumayya Ina Ruwan ta da abinda Yake tsakanin ku da Uban ta ?.

Yaja baya da sauri yana Fadin

“Kika ce me? Aure? wane irin aure? shi Usman din ne yayi min wannan wulakancin? ke kuma sai kika saka hannu kika karbe ta saboda kina Jin Dadin kiga ana min wulakanci?.

“Don Allah ka gane wani Abu mana,? Gaban surukai fa kake wannan maganar? Itama wannan ai ka gane ta ko? Usman ysce min itama an daura auren su da yar gidan Alh iro ina ganin fatan alheri kawai ya kamace ka distinguish.

Ya zaro Ido yana fadin

“A me Usman yake dauka ta ne wai?

Ya fada yana jawo wayar shi ya dokawa Usman kira kara biyu ya dauka Yana fadin

“Waye Kai da kake keta min iyaka har kayiwa abdulhameed dukan kirji kana min over talking? waye kai ? nace waye kai ? To ban shirya karbar auren kowace shegiya ba Babu kuma shegen da ya Isa yayi min over talking ni da Dana abin mallaki na yadda kuka kulla shi kuje ku kwance shi wallahi ba gara min Yar gidan iron ba da dai yar gidan Sufi.

“Wallahi babu daya da za a kwance Mukhtar kuma amsar ni waye  kuma gata Nan ta fito tunda nayi abinda kake tambayar ni waye ? To ka gane mana ko Ni waye in bai kai ba zanyi abinda nayi? Nine Uban Abdulhameed na hakika da sumayya na kuma zartas ta kuma zauna lafiya wallahi Yaya Mukhtar tunda abdulhameed yana son matan sa babu mai Raba shi da su . na yarda ni da Sufi ka zana mana jar biro da duk irin Sunan da kake so Amma aure sai in Allah ne ya Raba shi amma dai ba mutum irin ka ba.

Ya katse wayar shi ya bar distinguish da fidda hawayen takaici.

Ya lalubi wayar Abdulhameed wanda ya dauka yana fadin

“Don Uban ka da Kai aka hada Baki Don wulakanta Ni ? Kana sane da auren munafuncin da Usman ya hada maka ko kuwa baka Sani ba?.

“Ina sane Daddy ya fada min ni da sumayya ne zamu gyara musu zumunci na Kuma yarda da lallai Haka ne shiyasa na yarda don Allah Daddy ka Aje komai ka manta da abinda ya faru wa ya  San gobe banda Allah ? Idan ka mutu a yanzu Daddy kacewa Allah me tunda ka san halin da Mai gaba yake shiga idan ya mutu bai tuba ba?.

“Kai zan ci Uban ka idan kace wannan hanyar suka Dora ka maza maza kazo yanzun Nan a gabau na ka sauwake musu auren ka har ita waccan Yar mahaukaciyar dukkan su ban yarda ba ban kuma ga ban da y Isa yayi min over talking ba .

Ya soma zarya yana jiran zuwan abdulhameed yazo ya saki Nadiya da sumayya inda Kuma tuni Abdulhameed din ya Shirya mishi hikima bai zo gidan ba sai ma kiran Haj laila da yayi yace ta tura mishi Nadiya da sumayya gashi a kofar gida. ta kuma tura su inda distinguish yake zaton ko sun fice zuwa gidan iyayen su ne Bai Sani ba Ashe an mishi ta Yan duniya.

Har sha buyun dare yana jiran isowar abdulhameed da ya kira wayar sa ma sai yaji ta a kashe sai da safe ya same shi a wayar Yana auna mishi Ashar yana Fadin

“Wato ban Isa nace kayi kayi ba ko? shine kaki zuwa kiran da nayi maka don kana ba da goyon Bayan a wulakanta ni ko?.

“Kayi hakuri Daddy Allah ya Sani ba zan iya sakin auren kowace ba shiyasa ma na dauke Mata na bar nigeria.ba Kuma zan Kuma dawowa ba har sai Ranar da na sami labarin ka shirya da Yan uwan ka in ma Baka shirya da su ba to ni Ina tare da Yan Uwa na ba zan tab’a Bari wani kuskure ko sab’ani ya hada mu ba don Haka Daddy ka yafe mini smma ba zan iya zama Ina ganin kana zagin ubana ba kuma uban matata ba in yanzu na kira Baffa alkali yace min ka saki komai kun daidaita da yan uwan ka wallahi s gobe zan dawo Amma in dai nufin ka kace na saki sumayya don ka kuntatawa Baffa alkali to gaskiya ba zaka kuma saka ni Ido ba sai dai zan Rika kiran ka ina gaishe ka.

Ya sauke wayar yana mamakin yadda aka yi nasara akan sa . Ya Rasa ta ina kuma zai kamo?.

Alabo kam ya samu matar sa ana ta soyayya yayin da fati kuma ta kasa karbar soyayyar Kaisar wanda shi kuma bil hakki yake jin ta ga kuma Ya’yan su Siyama da yan biyu sai khalifa . Babu abinda ke ran Fati sai kishin Alabo da ta kasa mantawa tana tunanin ya za ayi ta iya manta hakan? Innar ta Hajara ce taxo take fada mata yadda alabo ya kama matar shi ya rike Gam.

“Ahaf yo su maza ma wata kunya ce da su ? Ba Nan yake ta turjewa ba Wai shi baya son zainab ba? to jeki ki gano yadda yake mats tamkar zai duka tabi bayan shi kece dai in bakiyi sannu ba zaki Kare a Babun Badu lahu gara ki manta da shi ki Kama mijin ki yafiye Miki kinji ko?

Tun daga wannan rana kuwa Kaisar yaga canji daga gareta ta Rike auren ta da daraja tana wa mijin ta biyayya.kwanaki kad’an taji mama na fadin zainab bata da lafiya wai ance ciki ne .tun daga Nan Fati ta yarda maza Yan garari ne shiyasa ma ake cewa wacce ta Rike shi Uba zata mutu da maraicin sa don Haka ta Kama mijin ta ta Rike Gam Wanda ya soma fita kamfani don Daddy yace Dole ya fara futa don ya ga Halin da ake ciki don Haka a yanzu Kaisar ya kama Aiki amma Babu abinda ya mishi shamaki da yaran sa da matar sa musamman yan biyu da Siyama sai kuma khalifa wanda mama take son karbe wa har ta yaye shi Yake a hannun ta.

Tukuro ya zama abin tausayi domin kuwa kudin da za ayi mishi gashi ma sun soma gagara dole aka taitaye shi aka mayar gida wurin mahaifiyar sa Haj gaji yayin da tafiya ma sai a keken guragu ga Hannu da kafa basa Aiki Baki ma ya jirge gefe . amma Dole aka siyar da konannen gidan shi don siyan magani da abinci  inda akayi gwanjon kamfanin shi a ka siyar a wulakance.haka gidajen man fetur shima dai a wulakance aka siyar da su don sun zama kufan wuta .

Haka aka ganganda aka siya mishi gida mai daki biyu inda sabe karamin kanin su ke kwana tare da shi shi kuma sabe ya soma lalube yan kudaden da suke jikin shi in kuma ya shilla ya tafi Sai dare don Haka a Nan tukuro zai wuni Akan keken nan zai yi tutu da futsari sai sabe ya dawo yayi ta mishi tijara tamkar zai kai mishi Duka sai dai tukuro yayi hawaye y share wai yau shine akewa tijara ? Lallai duniya maganin mai kokari kuma alheri kawai ake shukawa a girbi alheri amma komai ka shuka zai fito ka girbi kayan ka shi kam lokaci ya kure mishi .

“Allazi wahidun Allah da GIRMA yake.

Kaisar ya juyo da sauri saboda jin muryar dattijon sai ya ganshi Rike da Robar barar sa da kuma sandar sa.

“Sannu baba Ina wuni?

“Lafiya lau dan samari ya Rayuwa?

“Mun godewa Allah baba .

Ya fito da kudi masu yawa ya miko mishi yana Fadin

“Kai na gode yaro kaji a dai dage ayi ta sadaka kaji? kar ka nufi kowa da sharri Kuma ka maye Aikin alherin da mahaifin ka Yake amma sai an daure kuma kake zuwa dangin uban ka suma ka na Basu tallafi smma ka tsaya kawai da taimakon su Kar ka yarda su Shiga jikin ka don gudun cutarwa Allah ya kara sutura kaji?.

Ya soma tafiya har ya bacewa ganin Kaisark

Tun a Ranar kuwa ya soma ai tallafi asibitoci da gidan marayu da dukkan wasu ayyuka da ya San mahaifin sa ya tsayu akan su.

Wata biyar kenan Rabon distinguish Mukhtar Biro da Abdulhameed damuwa Kam Yana cikin ta amma karfin hali ya Hana ya nuna .  wani matsiyacin zazzabi ya Kama Mukhtar wands suka nufi asibiti aka bashi gado

Ciwo wasa wasa sai ga distinguish Yana cewa matar sa Haj Laila ta Kira mishi Sufi su yafi juna mutuwa zaiyi.

Ta kira Sufi ta sanar dashi suna asibiti sai kuwa ga shi bawan Allah ya dubi Mukhtar yana Fadin

“Yanzu har wannan lokacin kana asibiti yaya Mukhtar amma bamu Sani ba?.

“Sufi don Allah ka yafe mini wallahi mutuwa zanyi kar na zo na mutu da nauyi a kaina na san baka da laifi nine mai laifi don Allah ka yafe mini ka Kira mini Usman da abubakar don Allah Kira min su.

Suka iso asibitin inda suka samu labarin abinda ke faruwa.

“Alhamdulillahi Yaya Mukhtar mu dama wannan ne fatan mu in Sha Allah ba zaka mutu ba ciwo ba mutuwa bane sai kwana ya Kare.

Ana shirin fita waje ne sauki ya samu sai ga distinguish ya mike cikin Yan uwan sa ana wasa da Raha.

Kyauren ya bude sai ga Abdulhameed shi da sumayya sun bayyana sumayya na cike da Jin kunyar Baffan.

Abdulhameed ya zube a gaban Daddy tare da sumayya suna gaishe shi ya Amsa Yana saka musu albarka inda Yake ta neman yafiya ga abdulhameed da sumayya har yana tambayar sa Ina Nadiya take,? Yace ta na wurin momy don bata jin dadi ne .kafin ya dubi distinguish Yana Fadin

“Daddy albishir zan maka ?

ya nuna sumayya yana Fadin

“,Wallahi Daddy ciki ne da ita itama Nadiya muje asibiti ance ciki ne kaga MAFARKIn ka zai tabbata in Sha Allah sai kun dauki Ya’ya na daddy kaga silar auren Nan ya zame Mana alheri.

Wata irin murna da farin ciki suka kama distinguish yayi ta sakawa auren albarka har zuwa lokacin da ya karbi takardar sallama suka wuce gida inda Abdulhameed yace ya dawo gida inda Kuma ya Rabawa su sumayya gida kowace da sashin ta gida daya ne Amma sashi sashi.

Zainab din alabo ce ta fara haihuwa ta haifi Mai sunan Daddy kafin sumayya wacce ta haifi twins duk Mata Mai sunan Haj Safiya da Laila kafin Nadiya wacce ta haifi Mukhtar wato distinguish kenan inda su Tero ma da Tsagera su daddy suka nema musu aure a cikin dangin suka Kama aiki yayin da Al Amarin su Sufi da Mukhtar ya tafi daidai Babu sauran wani tuntube ko ya tsso ma zasu bawa abin Baya.

Yayin da Nadiya kuma ta Rike su daddy da Mama a matsayin iyayen ta na Rai da Rai yayin da mutanen jama are Kuma suke kallon Nadiya a makwafin uwar ta Mai Rasuwa inda Nadiya duk juma a tana dafa abinci ta Raba sadaka ga almajirai hadiyya ga mahaifiyar ta da dukkan mumunai bayin Allah. Soyayya tsakanin ta da Abdulhameed ba a magana tini ta Gane so Daya yske Mata son da bashi da gami.

Fati ma ta haifi dan ta wanda aka sakawa sunan Alh sule yayin da Kaisar aka hada kan zuri a Amma kuma wani ikon Allah da ya saukar Akan Yan biyu yanzu kamfani ke daukar su suyi mishi talla a buga hoton su a banner inda suka fara yiwa dangote tallar magin sa sai kuma Madarar pick itama sai ga yaran sun zama Milt miloniya abinda yake baiwa kowa mamaki wato shi Allah a barshi da ikon shi duk abinda yayi Yana da hikima yau ga yan biyu sun zama wasu a duniya don hatta karatun su kamfanin da sukayi wa talla ne ya dauki nauyin karatun har su kare .

Sai dai kunya da ta Hana Nadiya da Abdulhameed su ce wani Abu ko su tanka Daddy iro ma yace Babu mai su sai Kaisar don har gobe fuskar shanu ce tsakanin sa da Nadiya bare kuma Siyama da ta zama yan Mata kana ganin ta fuskar ta sak ta Mai irin sunan ta wato mahaifiyar Kaisar Amina. soyayyar Siyama daban take ga Kaisar don Gaba Daya kallon mahaifiyar sa yske Mata sai akayi sa a yarinyar Babu hayaniya a tare da ita sai ta zama the best don haka bai Bawa Siyama damar sanin Nadiya na sosai ba ta San dai goggon su ce Amma bata san ta a uwa mahaifiya ba mama kuma tace ai abinda ka shuka shi zaka girbe.

Hakuri kan babu irin wanda Nadiya bata bawa Kaisar ba har a yau da suke da Ya’ya Rututu a gaban su amma kalmar daya ce ya yafe amma bayan haka ko fuskar sa Bata gani in ma Yana dariya ta iso zai gintse Babu yadda Fati batayi ba amma ya take mata burki in ma tana son ganin gizagon sa to ta saka mishi baki a lamarin Nadiyar.

To dama dai duk abinda ya fara Dole zai Kare wata Rana yau dai tsayin tafiyar AZURFA DA ZINARE ya zo karshe duk da jarumai da yawa sun Sha wuya wasu ma sun Rasa Rayuwar su to dama Haka Al Amarin Yake muna Rayuwa ne kafin mu cimma lokaci wasu ma munzo duniya ne sun wuce don Haka mu ma zamu Tara’s da namu lokacin Allah kayi Mana kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma don mutuncin manzon Allah.

A Nan ne Nazo karshen littafin AZURFA DA ZINARE fatan Ubangiji ya yafe Mana kuskuren ciki ya hada mu s cikin abinda Yake daidai . Har kullum a gare ni rubutu ba don Nishadi yske ba sai don mu Ankarar da juna wani Abu da ke bukatar gyara Allah yasa Al amarin ya zama mai amfani a garemu duka sai mun sake haduwa a wata firar in Sha Allah GIDAN IKO ke muku fatan aminci Aminci har a gidan Aljanna

<< Azurfa Da Zinari 98

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×