Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Ba Kauyanci Ba Ne by Fatima Abubakar Saje (Ummu Adam)

GODIYA

Bismillahirrahmanir-rahim

Ina mai miƙa godiya ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai daya bani ikon fara wannan rubutu mai albarka in sha Allah. salati marar adadi ga fiyayyen halitti manzon tsira annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.

Godiya ta musamman ga iyaye na tare fatan rahama a garesu duniya da lahira.

Bazan manta da miji na ba wan da kulawarsa, taimakonsa tare da sadaukarwan sa gare ni ya zama silar kasance wata a wannan matakin da nake a halin yanzu. Tabbas duk wani ci gaba da zan sanu a rayuwa ko mataki da zan taka yana da kaso mai yawa cikin nasarata, ina masa addu’a Allah ya azurta shi, ya kare imaninsa ya azurta shi da duk abunda zai zama alfanu a rayuwasa. Amin.

‘Yan uwana da dangi na tare da ‘yaya na, ina muku fatan alkairi tare da addu’a Allah ya kare ku ya ƙarawa rayuwa albarka da dankwan zumunci tsakaninmu.

Bazan manta da ɗaukacin al’umar musulmi ba, ina fatan Allah ya mana gafara, ya jiƙanmu, ya yalwata mana arzikinmu sannan ya haɗa kan ahlus-sunnah a duk in da suke.

Allah ya sauƙaƙa mana tsadar rayuwa, ya bamu aminci da nitsuwa, ya yaye mana musiba da bala’i, ya azurtamu da tsaro ya rabamu da tsoro ya bamu lafiya da zaman lafiya, ya shiryar da mu da ‘ya ‘yan mu da zuriyarmu baki ɗaya. Amin.

GABATARWA

Bin dokar Allah ba ƙauyanci bane labari ne ƙirƙirarre dana rubuta dan faɗakar da kaina da kuma sauran ‘yan uwa musulmai baki ɗaya.

GARGAƊI

Ni nake da hakkin mallakar dukkannin rubutuna ko littafina, ban yarda ayi amfani da shi dan wata manufa ba sai da izini na.

BAYANI

Idan wani sashin labarin yayi dai-dai  da labarin ki/ka to an samu kamanceceniya ne kawai amma ba da niyyar cin mutunci ko tonon asiri ba.

Ina maraba da gyara, ƙorafi ko shawara daga gare ku, kuma ina fatan wannan littafin ya amfane ni da ku baki ɗaya. Amin.

ABUNDA LABARIN YA ƘUNSA

Babban abunda littafin “Bin dokar Allah ba ƙaunci bane” ya ƙunsa wayar da kan mutane game da kallon ƙauyanci da ake yiwa bayin Allah masu ƙoƙarin bin dokar Allah a duk abunda ya shafi rayuwars. Abu na gaba shine tarbiya a kowani fanni na rayuwar ma’aurata, ma’ana ya shafi tarbiyyar yara, iyaye, da sauransu.

Littafin ya taɓo wasu ɗabi’u ko halaye na wasu iyaye da rawar da suke takawa, wajen gyara ko rugujewar tarbiyyarya’yansu.

Littafin ya sake taɓo haƙiƙanin ma’anar ƙawance/abota daya dace da cikar kamala. Labarin ya haskakawa mutane illan dake cikin tara samari da wasuyammata ke yi da yawan karɓan abun hannunsu. Wani sashi na labarin ya kantamo kuma ya ɗebo daga kogin soyayya, menene ma’anar so?

Wa ya kamata a so?

Kuma wani irin so ya kamata masoya su yiwa junansu?

Ku kasance tare da labarin soyayyar Kamal, Safiya da Salma a cikin wannan littafi dan fahimta ko samun amsoshin dukkannin tambayoyin da suka gabata.

Kamar dai yanda na saba faɗa, Ni ba ƙwararriya marubuciya bace, koyo nake kuma ina fata zaku yi hakuri da kurakurai na.

LITTAFIN YA ƘUNSHI LABARAN GIDAJE KAMAR HAKA

1- GIDANSU SALMA
2- GIDANSU KAMAL
3- GIDANSU SAFIYA
4- GIDANSU ZUBAIDA
5- GIDANSU KHADIJA
6- GIDAN KAMAL, SALMA DA SAFIYA

MUTANEN DA KE CIKIN LABARIN

1-SALMA
2-HAJIYA BILKISU
3-ALHAJI ABDULƘADIR
4-AFRA
5-SAFIYA
6-MALAM ABDALLAHI
7-KAMAL
8-ALHAJI SAMEER
9-HAJIYA SAMIRA
10-HAJIYA AISHA
11-SALIFA
12-ZUBAIDA
13-HANIFA
14-KHADIJA
15-MAMAN KHADIJA
16-AHMAD
17-ZANNURAIN
18-INNA
19-MALAM
20-KHALIFA
21-AMNA
22-ASMA
23-SAUDA
24-MAMANYAN BIYU
25-ABDUL
26-MALAM SHARIF
27-HALADU (DIREBA)
28-MAI GARI
29-YARIMA
30-ƊAN IYA (BOKA)
31-SULTAN
32-ALHAJI KABIR
33-ABDULJALAL
34-SAMHA
35-DR. JABIR

(GIDANSU SALMA)

“Nifa na fara gajiya da makarantar nan mama, gaskiya kawai ki canza mun wata “cewar Salma kenan ga mahaifiyarta wacce take zaune a bakin gado ita kuma salma na kwance akan cinyarta.

Cikin murmushi Hajiya Bilkisu ta dubi Salma tace “haba Salma yaushe muka dawo garinan harda za ki canza makaranta sau biyu a shekara? Kin manta sai da ki ka yi wa mahaifinki alkawarin zaki zauna a makarantar kafun ya saki?, Babu amfanin yawan canza makaranta dan karatunki ba zai zama a kan saiti ba; kuma naga ai kin fara sabawa da mutane ko?”

“hakane, amma mama rayuwarsu ne yake bani tsoro dan akwai wasu abubuwa da yawa da bana son gani ko in ji amma dole nake hakura dan bayadda zanyi. Mama kin san ni bana san hayaniya kuma bana san in fara koyan wasu dabi’u wanda banawaba, Allah ya gani kina iya ƙokarinki wajen tarbiyar mu ni da Afra kuma mama bana so na baki kunya shiyasa.

Cikin murmushi Hajiya Bilkisu tace “Salma kenan, to ai dama rayuwa cike take da ƙalubale kuma duniya cike take da abubuwan ruɗu da ban mamaki sannan kuma babu inda aka taru aka zama ɗaya dole asamu na kirki da akasin haka kuma ki tuna zamanin annabawa ma an samu mutane gurɓatattu azzalumai ballantana wannan zamanin namu da sai dai adddu’a kawai.

Amma abunda na ke so dake shine duk runtsi duk wuya kada ki sake ki kama wata hanya wacce bata dace da koyarwan addinin musulunci ba, ki sani cewa bamu da wani gata da ya wuce musulunci kuma duk abunda za ki yi toh ki yi shi dan neman yardan Allah shi kaɗai hakan zai sa ki kasance akan dai-dai kuma koda Bayan raina ne.”

A tsoro Salma ta rufe bakin mamanta san nan tace “mama dan Allah bana so kina kawo maganar mutuwa yana ɗaga mun hankali, mama samun mahaifiya irinki sai an duba, kin zamamin uwa, ƙawa, kuma abun koyi ina alfahari da ke mama; kuma na miki alkawarin zan kula da kaina da Afra ba za ki taba korafi da ni ba in sha Allah.”

Hajiya Bilkisu ta dubi ‘ƴarta Salma tace “naji daɗin wannan maganar, Allah ya muku albarka gaba ɗayanku.” Salma ta amsa da “amin mama.”

Firarda ya kasance tsakanin Salma mai kimanin shekaru goma sha biyar da haihuwa da kuma mahaifiyarta Hajiya Bilkisu mace mai dattaku da hakuri ga kuma cikar kamala.

Salma yarinya ce karama amma akwai ilimi, nutsuwa, da kuma hangen nesa.

Tana matukar kama da mahaifiyarta sosai kuma ba iya kamannin ba harda hali da ɗabi’a, sai dai kash mahaifin su Salma wato Alhaji Abdulƙadir mutum ne mai san biyewa rayuwar turawa da bin ɗabi’unsu a fahimtarsa hakan shine wayewa.

Afra ita ce ƙanwa ɗaya tilo gurin Salma yarinya ce kekkyawa mai halin kwarai kamar dai ‘yar uwatta, sai dai ta fi Salma surutu kuma shekara biyu ne tsakaninsu.

Ba Kauyanci Ba Ne 2 >>

2 thoughts on “Ba Kauyanci Ba Ne 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×