Makarantar Su Salma
Malamin koyarda harshen turanci kenan a aji, wayewar garin laraba; bayan kammla darasi ya cike lokacinsa da bawa ɗalibai aikin gida kamar haka…
“Your assignment question is “write a letter to your friend telling him/her how you spend your last term holiday” not less than 350 words, to be submitted on Monday morning.”
Fitarsa daga aji keda wuya ɗalibai suka hau mita musamman ma Zubaida wacce ta fita zakka gurin fitina da rashin ji.”
Zubaida tace “hmm” nifa abun malamin nan ya fara isata kullum a rubuta saƙo sai kace sabon shiga a soyayyah.”
Khadija tace “ko kema kya fada, wannan shine karo na biyar kenan da ya bamu irin wannan aikin with different tittle.”
Safiya tace “umm kanku ake ji, nifa tun yanzu zan fara nawa aikin; dan muna da biki a gidanmu nasan bazan samu damar yi ba a gida saboda hayaniyar jama’a.”
Salma tace “kar dai bikin Anty Naja?”
Safiya tace “eh, kin san da yake hidiman bikin a zariya za’ayi shiyasa babanmu yace kawai baza’ayi wani fitina ba sai dai walima da wa’azi in munje can dangin mamanta dana angon zasuyi shagalin bikin.”
Khadija tace “tab kice bazamu jeba, biki ba shagali meye amfaninsa ki cireni aciki gaskiya.”
Zubaida tace “kinsan mu gurin casu muka fi ƙarfi inda za’a baje kolin samari muci ado da kwalliya mu bawa kowa a jikinsa in da bazamuyi asaran jan baki da hoda ba.”
Salma tace “Allah ya shiryeku ƴan wahala kawai, samarinda basu suke siyamuku kayan ƙwalliyar ba amma akansu kuke ƙararwa kuma abun haushinma ba’asan kunayiba!”
Zubaida ta ɗan juya ta rintse ido sannan tace “toh malama Salma muna godiya abar na gobe da safe, kinga khady zo ki rakani wajen zaman malamai.”
Safiya tace “wai ke zubaida mai yake kai ki gurin malamai ne kusan kullum sai kinje?”
Zubaida tace “Oh Allah ka rabamu da ƴan sa ido na fili dana boye na kusa dana nesa, In kina san sani sai ki biyoni muje tare ki ganewa idonki in yaso kyaji dadin bada labari.”
Safiya tace “mai ya yi zafi, adawo lafiya.”
Zubaida tace “amin, in da gaske ki ke yi”
Bayan fitarsu Zubaida da Khadija sai Salma da Safiya suka ci gaba da firarsu kamar haka…
Salma tace “kinga rabu dasu kawai mufara aikin da malamin nan ya bayar tun yanzu, dan kin san akwai rubutun da bamu gamaba. Hm dama haka matakin sakandiren yake? muna gaba yana kara wahala a yi ta tarawa mutum aiki kamar ba gobe?”
Safiya tace “ai gwarama ke Salma mamarki tana taya ki wajen koyan miki abubuwa dayawa, nifa da bani da ita komaina akaina yake wallahi Salma rashin uwa ba abinda ya kaishi zafi” ta fada tana hawaye.
Kalaman Safiya sun sosa zuciyar Salma, tausayin safiya ya kamata sabida Safiya marainiya ce kuma matar mahaifinta bata riƙeta a matsayin ƴa ba.
Cikin sanyin murya da alaman tausayawa Salma ta dubi kawarta Safiya tace “Safiya kiyi hakuri watarana sai labari haƙika kina cikin jarrabawa amma ki sani Allah yana tareda masu hakuri, mamarki kuma adddu’a take buƙata ba kukaba.
kuma ai abinda zaki duba babanku yana ƙaunarki sosai bayasan ɓacin ranki ko kaɗan, dan haka Ki godewa Allah da ya baki mahaifi mai sharemiki hawaye.”
Safiya tace “hakane kam Alhamdulillah ala kulli hal, sonda babanmu yakewa mamana gabaya ya dawo kaina bayan rasuwanta. kuma gashi nice mai sunan mamansa wannan dalilin yasa antinmu bata sona wai kishi take yi da ni kuma dai kin san halina bana mata rashin kunya wallahi ina bata girmanta kuma ina kula da kannena data haifa sosai.”
Salma tace “hakane na sani ki ƙara hakuri kin ji ƙawata kuma in ba damuwa ko za ki zo muyi hutun karshen mako a gidanmu sati mai zuwa tunda kince babanki zai yi tafiya? Safiya tace “tab wane ni, yanzu ina zuwa zata samu abun faɗawa mutane tace nafara yawo harda barin gida, kinga shikkenan abun nema ya samu.”
Salma tace “hakane kam, toh Allah ya rufa asiri.”
Safiya tace “Amin ya hayyu ya qayyum.’
Safiya yarinyar kirki ce halayenta da ɗabi’unta sunyi kama dana Salma hakan ya sa suka zama ƙawaye kuma aminan juna basa rabuwa, safiya ta rasa mahaifiyarta tun batada wayo sosai hakan yasa salma take ƙara janta a jiki.
Sannan akwai Hajiya Samira ‘yar uwar mahaifiyar Safiya wacce suka haɗa kaka ɗaya daga ɓangaren mahaifansu maza. Safiya tan kiranta Adda, itace take mata komai na abunda ya shafi gata na wajen uwa data rasa.
Adda ta kasance tana da ɗa guda daya tilo wanda bata kara haihuwa ba bayan shi saboda matsalar da ta samu a mahaifarta.
Mijinta Alhaji Sameer mutum ne mai kuɗi, ɗan kasuwa kuma dan siyasa ne mai gaskiya da amana mutumin kirki mai san taimakon al’uma, Adda tana da kishi sosai da kuma zafin rai shi kansa mijinta hakuri yake yi da al’amarinta amma duk da haka mutum ne tsayayye a gidansa kuma kishin Adda wato Hajiya Samira bai hana shi yi mata kishiya ba wato Hajiya A’isha.
Gidansu Salma
Cikin fushi Alhaji Abdulkadir ya shigo gida yana raɗawa matarsa Hajiya Bilkisu kira ɗaya bayan ɗaya ko damar amsawa baya bata. Hajiya Bilki tana jin haka ta san ba lafiya dumin duk sanda baban Salma ya shigo yana mata irin wannan kiran to tasan ba lafiya ba, sai dai bata san mai ya faruba. Hajiya Bilkisu ta bude kofar ɗakinta ta fito cikin hanzari sai taga Salma ta wuce ɗaki tana kuka wanda hakan ya tabbatarwa mata lalle akwai matsala.
“Barka da dawowa ranka ya daɗe” tana murmushi ta iso gareshi sannan ta ƙara da cewa “me ya ke faruwa naga duk ranka a ɓace haka?”
Baban Salma ya kalli Hajiya Bilkisu yaga irin kyanda matarsa tayi take hankalinsa ya fara kwanciya amma sai ya yi kamar ba hakaba ya ɗaure fuska ya fara mata faɗa.
“Au, tambayata ma ki ke yi ko? toh barin fadamiki yau kinjamun baƙin jini a idon duniya a karo na biyu, ko danma laifina ne nayi zaton Salma wayayya ce ashe dai ‘yar ƙauye ce wayewarta a gida ya ƙare; kuma ai dama “barewa bazata yi gudu danta yayi rarrafe ba” toh daga yau da ke da “ƴarki Salma ba zaku sake halartan wani taro daya shafeni ba.
Shekara goma sha biyar baya kin kunyata ni a cikin taron ƙarin girma dana samu, ki ka ɗauko wani ƙaton hijabi kika saka, kuma abokai na suna miƙa miki hanu dan su tayamu murna amma ki kai biris ki ka ƙi gaisawa dasu wai ke malama sai kace ke kaɗai ce musulma agurin gashi yau ma ‘ƴarki ta sake mai-maita hakan!”
Hajiya Bilki ta san hakan zai faru shiyasa tun farko ta so ta hana Salma zuwa amma tace tana so taje.
Hajiya Bilkisu sai ta riƙe hannun mijinta ta zaunar dashi akan kujera ta dauko ruwa ta zuba a tambulan ta bashi da hannunta a baki, take kaso saba’in na ɓacin ran ya tafi.
Bayan yasha ruwa sai ta kalleshi tace…
“kayi hakuri dan Allah, na san baka ji daɗin abunda ya faru ba sannan dole ranka ya ɓaci kuma na fahimci ɓacin rannaka amma ka san Salma yarinya ce ƙarama taron mutane dayawa zai bata tsoro sannan ka santa bata son hayaniya shiyasa amma batayi hakan dan ta baka kunya ba, amma dai duk da haka ina baka haƙuri a madadinta kuma itama yanzu zankira ta, ta zo tabaka hakuri”
“Ba sai kin kirata ba” baban Salma ya faɗa.
“Hajiya Bilkisu kin kasa wayewa kinƙi cire ƙauyanci daga rayuwarki, yanzukuma kin maida ‘ƴarki “ƴar ƙauye a idon duniya. Can you imagine wai Salma ce abokaina suka mika mata hanu a matsayinta na “ƴata amma ta ki gaisawa dasu kuma abun haushinma harda Kamal ɗan gidan sanata yazo da abokanshi dan suga Salma amma ta disga shi kuma dan ya rike hannunta kawai ta tsinka mai mari a gaban iyayensa; kuma sanin kanki ne Alhaji sameer shine silar arziki na a duniya.”
cikin sanyin murya Hajiya Bilkisu tace yanzu dai abunda ya faru ya riga ya faru dan haka ina mai baka haƙuri dan bani da abun faɗa da ya wuce haka. Yanzu tashi muje ciki ka huta idan ka tashi anjima sai muyi maganar.
“Babu wani magana da zamu yi Hajiya Bilkisu,kuma banasan kowa ya shigo ɓangarena yau ku barni, ni ka ɗai”
Maman Salma tace “shikkenan in dai hakan ka keso zanbi umarninka your Excellency.”
Duk da yana fushi amma yaji daɗin kalmar excellency data faɗa sai yace “wannan innocent face ɗin naki shi yafi komai bani haushi, duk yanda na so nayi fushi dana ganki sai naji zuciyata kamar dalman da aka sawa wuta! Yana faɗin haka ya juya ya tafi ɗakinsa.
Tana masa magana ya yi tafiyarsa ko juyowa bai yi ba, daga nan sai Maman Salma ta nufi ɗakin salma.
Bayan shigarta ɗakin sai taga hankalin Salma a tashe tana kuka sai ta zauna a gefenta sannan ta jata a jiki tace “Salma ‘ƴata mai yasa ki ke kuka haka? nasan bakida laifi kuma ai abunda ki kai shine dai-dai dan ba’a biyayya ga abun halitta akan saɓawa mahalicci dan haka kada ki damu shima babanki zai fahimcimu watarana in sha Allah.”
Salma tace “mama kiyi hakuri na jawo miki faɗan baba alhali ba laifinki bane, wallahi mama ban yi niyan marinsa ba shi ne ya tilastamun dan sau uku ina janye jikina amma yana kokarin taɓani akarshe wai sai dai na cire hijabina muɗau hoto dan naƙi shine yayi kokarin ciremun hijabina sai ni kum na mareshi, shi kuma baba bai san me ya faru ba kawai yayi fushi ya jawoni muka dawo gida.”
Maman Salma tace “yau tabbas ina alfahari dake kuma “albasa tayi halin ruwa” Salma aduk lokacinda muka zabi mu yiwa Allah biyayya to tabbas sai an yaƙemu, kuma hakan jarrabawa ce dan Allah yana jarabtan bayinSa musamman idan sunce sun yi imani kuma da haka ne ake ban-bance masu imani na gaskiya da kuma munafukai.
Dan gaka abunda ki kai yau ba ki yi laifi ba kuma ina tabbatar miki kinci kyauta daga gare ni, dan haka ki faɗamun abunda ki ke so ni kuma zan siyamiki in sha Allah.”
Salma ta rungume mamanta sannan tace “naji daɗi mama kuma na gode amma bana buƙatar komai in dai ina da ke mama. Amma mama naji kina ta bawa baba haƙuri bayan ba ki yi laifi ba ko me ya sa?”
Hajiya Bilkisu ta yi dariya tace “yaro dai yaro ne, toh banda abunki Salma ai shi haƙuri ba sai anyi laifi ake bada shiba, hakuri riga kafi ne ga fushi kuma maganine ga fushi idan ana yawan bada hakuri to baza’ana yawan fushi ba idan kuma anyi fushin to bada hakuri sai ya magance shi musamman tsakanin ma’aurata amma ba lalle ki gane hakan yanzuba sai zuwa gaba kaɗan idan kin yi aure.”
Salma ta rufe ido alaman jin kunya tace “mama ni dai ina tare da ke bazan yi aure ba” Salma ta faɗa. Hajiya bilkisu “tace nima na fadi hakan a baya”
“Yanzu dai ki je ki yi wanka ki yi alwala magriba yayi in kuna jin yunwa kuci abinci zan hau sama gun babanki, Kuma ki faɗawa afra ta dawo ciki banaso ana yawo a tsakar gida da magriba”
Salma tace “to, amma ai yace bayasan ganin kowa yau”
Maman ta tace “dan ya faɗa baya nufin hakan, duk abunda ya faɗa cikin fushi ne kawai.”
“Gaskiya mama kina da hakuri kuma ke jarumace!” Salma ta faɗa.
Hajiya Bilkisu tace “bakiji ance aure yaƙin mata ba? Ai ba mai zuwa yaƙi sai jarumi, idan ban sauko da wuriba kuyi tilawa ku kwanta bacci” Salma tace “to mama, mama ina san aron wayanki.”
“me za ki yi da shi?”
Salma tace “Assignment” Hajiya Bilkisu tace “ok, gashi karki karar min da data” Salma tace “to mama, in na gama zan ajiye wayan a parlour.”
Hajiya bilkisu tace “to shikkenan sai na dawo.”