Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Ba Kauyanci Ba Ne by Fatima Abubakar Saje (Ummu Adam)

Gidan Su Salma

Misalin ƙarfe takwas na safe Salma ta gama shirya karin kumallo akan teburi, maman salma da baban salma su ka sauko ƙasa dan cin abinci; cikin ladabi Salma ta gaida iyayenta suka amsa cikin farin ciki.

Maman salma tace “masha Allah, ina autan nawa take?”

Salma tace “Afra tana ɗaki tana shiryawa, au gata can ma fitowa. “

Bayan Afra ta iso kusa da iyayenta tamusu gaisuwa sannan suka zauna cin abinci cikin farin ciki da ƙaunar juna.

Baban Salma ya fahimci jikin salma haryanzu a sanyaye ya ke sai yace mata Salma ki saki jikinki mana, ai na hakura kinsan duk fushina baya wuce kwana ɗaya, kada ki manta wannan shine karo na farko da ki ka ɓatamin rai haka; ko dan haka na miki uzuri”

Salma tayi farin cikin jin haka daga mahaifinta, cikin murmushi tace “na gode baba, sannan taƙara da cewa”baba ina so in je sayayya anjima inka yadda”

“To ba komai, na yadda kuma zan bada kuɗi a mamanku in kunshirya sai ta baku” baban Salma ya faɗa.

Maman salma tace “idan ka amince zan raka su muje tare dan bana so suna fita su kaɗai sai driver”

Baban salma yace wai mai yasa ba kida yadda ne? Shekaru takwas kenan haladu yana aiki a gidanan amma baki yadda da shiba hajiya bilki?”

“ka yi hakuri ba haka nake nufiba kasan yaran yanzu da kuma yanda rayuwa ya canza dole mu sa ido mu kuka sosai.”

Baban salma yace “toh shikkenan, amma dai Hajiya ku dawo da wuri dan tuwo nake san ci da rana inkuma Sabira zata yi toh shikkenan.”

Maman salma tace “kaima dai Baban salma baka gajiya, ka san abincinka baya taba wuce hannuna.”

Baban salma yaɗanyi dariya sannan yace “hakane na gode da kulawa ta musamman, afra my girl sai kun dawo ko; ki kula da kanki.”

Afra tayi murmushi sannan tace “toh baba thank you.”

Jim kaɗan misalin ƙarfe goma na safe Hajiya Bilkisu da yaranta suka shirya cikin shiga ta mutunci da kamala suka nufi inda zasu je.”

Shigarsu shopping mall keda wuya su kai kiciɓus da Kamal da mamansa wato Hajiya Samira.

“Malama Bilkisu an jima ba’a haɗu ba, bayan haduwar ‘ya ‘yan mu kuma saai naji labari marar daɗi; Salma ashe kin yi girmanda za ki iya marin saurayi a tsakiyar taro?” Hajiya Samira ta faɗa.

Maman salma tace “Hajiya Samira kenan, ai ba Salma ba ce ta girma; Kamal ne ya girma tunda har ya iya kama hanun ‘ya mace a tsakiyar taro.  kodayake ba laifinsa bane wataƙila tarbiyarda aka koya mishi kenan.

kai kuma Kamal kafi kowa sanin me ya faru kuma kasan ba laifin Salma bane toh amma ance durƙusawa wada ba gajiyawa bane dan haka duk muyi hakuri kuma a kiyayi gaba.”

Kamal yaɗan sunkuyar da kansa ƙasa yace “na san laifi na ne kuma na yi nadama har cikin zuciyata dan haka Salma kiyi hakuri in sha Allah bazan ƙara yiwa ‘ya mace haka ba, kin san ɗan Adam tara yake bai cika goma ba.”

Hajiya Samira ranta ya ɓaci matuƙa tace “ashe abunda ka yi kenan Kamal?  haka na koya maka ka mu’amalanci mace!?”

Kamal yace “I’m sorry Mum na san ban kyauta ba.”

Hajiya Samira ta juya ranta aɓace ta futa daga gurin shima Kamal ya bita yanata bata hakuri amma ko kulashi bata yi ba.”

Bayan fitar Kamal da mamansa sai Salma “tace ina ma ace bamu futo sayayyar ba, na rasa me yasa maman Kamal take da faɗa sosai sannan bata ƙaunarki ko kaɗan Mama.”

Hajiya Bilkisu tace “ya isa haka mu bar maganan, kuje ku ɗauki abunda ku ke so mu koma gida.”

Bayan Kamal da mahaifiyarsa sun shiga mota sai yake lallashinta akan ta yi hakuri akan abunda ya faru, harma yake faɗim ai da ta yi hakuri sun gama sayayyan.”

Me zan yi a gurinda Bilkisu take? wato ashe abunda kayi kenan shine kaƙi faɗamun gaskiya gashi kasa naji kunya agaban mutane.”

Kamal yace “Mum ki bar maganan nan please nace kiyi hakuri sharrin shaiɗanne fa kuma kin san mu a can turai normal ne gaisawa da mata.”

Rufemun baki, ka duba handbag ɗina ka bani magani na nasha, sannan kuma ka kaini gidan Hajiya Aisha.”

Kamal yace Mum haryanzu baki bani amsar tambayata game da babanmu baba.”

Maman Kamal tace “ka tambayi babanka sauran labarin. Sannan kuma ranar juma’a zaka raka ni gidansu Safiya amma tafiyar ba tawa bace, taka ce.”

Kamal yace “kamar ya Mum, ni kuma?”

“Ina so zan kai ka, ka gaisa da Safiya yarinyar tana da hankali sosai; zan yi magana da babanta tana gama secondary school a bani ita awajena kaga daga nan sai ku fahimci juna ayi tuwo na mai na.”

Kamal ya dubi mamansa da sauri yace “amma Mum bance ina santa ba ai kuma yanzu an daina auren haɗi irin wannan kuma fa ƙawar Salma ce.”

“To sai meye dan ƙawar Salma ce?  ko dai akwai wani abu ne tsakanin ka da Salma?

Kamal yayi maza yace “no, ba komai Mum, but i need some time to think about it please.”

Maman Kamal tace “ba komai, zan baka lokaci kayi tunanin; amma fa bazan canja ra’ayi na ba.”

Gidan Su Zubaida

A hankali Zubaida ta shigo gida dan kar Inna ta ji motsinta, kai tsaye ta wuce ɗakinta sannna ta ɓoye kyautar da Ahmad ya bata; Motsin futowar Inna daga bayi Zubaida taji sai tayi maza ta futo daga ɗaki tace “Inna naji gidan shiru dana dawo ashe kina bayi?”

Inna tace “eh na ɗan shiga watsa ruwa dan yau ana zafi sosai, ya ki ka baro Khadija da mamanta?”

“Lafiya lau na baro su, harma su kace na gaida ki sosai.” Inna tace “to gaisuwa ya iso kuma na gode barin shiga ciki.”

Inna tana shiga ɗaki Zubaidan ma ta koma ɗakinta ta saki labule sannan ta ɗauko jakarta ta buɗe dan taga dubu nawa maman Khadija ta samata, aiko tana ɗauko kudin ta bude baki tace “yanzu dama ashe matar nan dubu biyar ta samun a jaka? Tabdi jam gaskiya duk san kudi na ta fini, amma in ba yau akwai wataran.
Gashi sai kiran wayar Khadija na ketayi amma shiru bata ɗaukan wayata karde abunda nake tunani ya zama gaskiya, “hm lalle ashe kuwa zasu gane shayi ruwane.”

Inna tana ɗaki amma tanatajin sambatu sai ta futo waje ta nufi ɗakin Zubaida tace “ikon Allah  Zubaida anya futanki kin yi addu’a kuwa?”

Zubaida tayi sauri ta ɓoye kayan da jakan sannna tace “eh Inna, na yi ai bana futa daga gida banyi addu’a ba; duk wani azkhar da kike koyamun ina yinsu, mai yasa ki ka tambaye ni Inna?”

Inna tace toh ai naji sai sambatu ki ke yi ne kuma ke kaɗai ce a ɗakin shine nake zaton ko gamo ki ka yi”

Zubaida taɗanyi dariya tace “haba Inna wani irin gamo kuma, ba komai kawai dai lissafi na keyi kin san mun kusa fara jarrabawar shiga aji biyar, kuma wannan litinin din zamu fara.”

Inna tace “ikon Allah kinga lokaci baya jimawa, toh shikkenan Allah ya taimaka ya baku sa’a, babanki ya dawo yana kiranki kije ku gaisa.”

Zubaida tace “to Inna.”

Bayan shigar Zubaida ɗakin mahaifinta sai ta nemi guri ta zauna sannan tace baba sannu da dawowa gaskiya kasha hanya.”

Baban Zubaida yace “yauwa, nace wa Innarki ta turomun ke dan akwai wata magana da nake so muyi dake, kin san dai na je ƙauye ko?”

“Ea baba, na sani” Zubaida ta faɗa.

Baban Zubaida yace “to bayan na je mungama maganar gona da sauran ‘yan uwana munsa gona a kasuwa sai mukai sa’a mai gari yaga gona yana so kuma muka sayar masa, to bayan an kammala maganar gona sai ya kirani yakemun wata magana akanki danganeda dansa Yarima.”

Zubaida tace “ni kuma baba?”

Baban Zubaida yace “ea ke, ɗansa Yarima ya ganki kuma ya ce yana sanki da aure kuma zai jiraki zuwa ki gama makaranta sai ayi bikinku, kinga shikkenan ciki lafiya baka lafiya kuma in bazaki manta ba ai dama can mai gari  dan uwanmu ne domin kuwa Adda Iyani kakarmu ta gurin uba sun haɗa dangi da ita yadikkon mai gari ta wajen kanwar mahaifiyarta. Kinga ai kuwa Yarima dan uwanki ne sai ayi tuwo na mai na musha biki abunmu.”

Zubaida taɗan gyara zama tace “Baba ɗan mai gari fa kac? kuma wannan kallen dangin da ko maimaitawa bazan iya yi ba shine za’ace tuwo na mai n! gaskiya Baba ni ban shirya aure yanzu ba akwai tanadi mai kyau dana yiwa rayuwata dan haka bazan iya auran wahala da zaman ƙauye ba.”

Baban Zubaida ya zabura cikin fushi ya dakamata tsawa yace “baki isa ba kin yi kaɗan ki watsamun ƙasa a ido,kuma ba shawararki nake nemaba umarni nake baki auren Yarima ya zama dole; ana nunamiki hanyar arziki kina rintse ido.”

Inna tana tsaya bakin ƙofa tana jin abunda ke faruwa a cikin ɗakin tsakanin Zubaida da baban ta ba tare da sun sani ba, cikin hanzari tayi wuf ta faɗa cikin ɗakin sannan tace “haba mai gida yanzu da bakinka kake faɗan wannan maganar? ca nake kwanakin baya mun/yi magana akan karatunta kuma ka amince?”

Baban Zubaida yace  “wato ashe kina laɓe kenan? ai ni bance ba zatayi karatu ba in ta gama karatun sai ayi auren.” Inna tace “ina nufin makarantar kwaleji fa ba sakandire ba.”

Baban Zubaida yace “ba zatayi ba, yanzu ke a irin wannan rayuwa ina mu kaga kudin biyan makarantar kwalej? kuma banda abunki mairo ai wannan kamar auren jari ne in fa akai aurannan wataran gonar da mai gari ya saya tamu ta gado zai iya dawo mun da abina; kinga ga kudi ga gona kenan.”

Maganarsa ya bawa Inna haushi sai kawai ta juya ta futa tabar ɗakin.

Baba in dai dan kuɗi ne ka ke so na auri Yarima to na maka alkawarin samun miji ɗan masu arziki wanda zan huta kuma ku huta sannan mu ji daɗi mu fantama a cikin dukiya.”

Baban Zubaida yaɗanyi dariya sannan yace Allah zubaida ƴata, da gaske ki ke yi?”

Zubaida tace “sosai ma kuwa Baba, daga sudan yake kamar ɗan barabe in ka ganshi ga wata mota kamar tayi numfashi; Baba na maka alkawarin sai ya zama sirikinka.”

Baban Zubaida yace “kaji ƴar albarka, to ke kin san da maganar mota kika bari ina ta maganar gona, to kwantar da hankalinki maganar yarima na soke ta.”

Zubaida tayi dariya sannan tace “yauwa Babana na kaina ai na san zaka fahimce ni.”

“Allah ya miki albarka, haihuwar kyakkawar mace jari; je ki abunki magana ya ƙare ki cewa Innar ki ta hadamun dambun nan yanzu na farafa jin yunwa.” Baban Zubaida ya faɗa.

Zubaida tace “toh baba.”

<< Ba Kauyanci Ba Ne 4

1 thought on “Ba Kauyanci Ba Ne 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×