Koda ya koma gida komai bai cewa Karima ba, kamar yadda ita ma ba ta ce mar ba. Illa dai ta gabatar mishi da abinci, bayan ya gama ci suka taɓa yar hira jefi-jefi.
Suna tsaka da hirar ne kira ya shigo wayar Hafiz, bayan ya daga "Ok" kawai ya fada tare da dire wayar yana fadin "Usman ne."
Komai ba ta ce ba, har Usman din ya turo kofar shigowa, fuska a tamke kamar yaki ya riga shi kofar gida, haka Karima ma ta daure tata fuskar ko kallon inda yake ba ta yi ba. Usman na. . .