Kafin Karima ta isa gida, mu ji wainar da za a toya, bari mu koma baya kadan don jin waye Hafiz da danginshi, wacece Karima da danginta.
Jihar Kano jiha ce mai tsohon tarihi, mai fadin gaske, wacce ke dauke da Local Government 42, kaso tamanin cikin dari na mazauna jihar Kano da ma kananan hukumomin Kano ƴan kasuwa ne kuma manoma , jihar Kano na daya daga jihohin da suke riko da addini, sannan suka fi fifita harkar addini a kan ko wace harka.
A wannan jiha aka haifi Hafiz, a unguwar Wazirai abin da yasa ake kiran unguwar, wazirai. . .