Lokacin da Hajiya ta koma gida falon nata cike yake da zuriyarta, saboda tuni ta basu umurnin duk su baro gidan sunan.
Shigar ta falon ya sa suka yi shiru daga hirar da suke yi, wacce kaf din ta a kan Karima ne, su har yanzu ba su ga aibun abin da ya faru ba, ba haka suka so abun ma ya tsaya ba, sun so a yi mata shegen duka kuma a bi ta da takardar saki.
Kai tsaye Hajiya dakinta ta wuce, Aunty Sa'a ce ta fara bin bayanta "Sannu da dawowa Hajiya" ta fada lokacin da. . .