Saifu bai fito kitchen din ba sai da ya tuka tuwon ya kuma sanya a leda kamar yadda ya ga tana yi, sannan ya dakko na shi ya fito zuwa dakinshi, a lokacin Karima tana ɗakinta.
Fitarshi ba jimawa ta fito zuwa kitchen din, komai da ya yi amfani da shi wajen tuka tuwon a nan ya bari.
Cike da jin haushi ta ce "Maza sun iya fadin mata basu da hankali, yanzu don Allah ina hankali a abin da yaron nan ya yi, kalli muciyar tuka tuwo, kalli tukunyar ma. Don jibi saman electric ɗina, Kai Allah ya kyauta. . .