Gidan Karima bai yanke da jama'a ba sai wajen karfe tara na dare, ya rage saura ƴan'uwanta ma fi kusanci da ita, wadanda za su kwana, su kuma yi mata gyaran gida da safe.
Zaune take gefen gado tana ba Jiddah nono, Aunty Teemah kuma na kwashe kayan da ke saman gado zuwa cikin wardrobe "Karima Wai wacece matar dazu?" Aunty Teemah ta tambaye ta idanunta a kanta
Wani murmushi ta yi, sannan ta ce "Matar Admiral Mukhtar Gabasawa ce."
Baki bude Aunty Teemah ke kallon ta, kafin ta ce "Ke a ina kika santa?"
Aunty Teemah ta. . .