Baba Dattijo ya yi gyaran murya, ya yi kaki ya tofar, sannan ya ce;
“Yaro ni da ka ke gani a mokaɗe haka, da ɗan gata ne ni,mahaifina attajiri ne, duk ƙauyenmu ba mai arziƙinsa, kuma ni kaɗai ne a wajen mahaifina, sai dai mahaifina yana da ƴan uwa da yawan gaske, masu ƙulaficin dukiyar mahaifina, kullum a cikin neman wata hanya su ke da za su wawashe dukiyarsa, ana haka ne mahaifina ya rasu”
Ya haɗiyi yawu sannan ya ɗora “Nan fa yunwar dukiyar mahaifina ta fito fili, in a da suna ɓoyewa yanzu a fili su ke bayyanawa. A haka ne wani ƙanin Mahaifina wanda ya fi kowa nuna maitar dukiyar mahaifina, ya haɗa ni da ƴar sa, wai a haɗa auren zumunci. Abu kamar wasa, magana tai ƙarfi, har na kan je zance jefi-jefi, rannan na je zance na tarar da wani saurayi Mati suna zance da ita, kamar in koma, sai wata zuciya ta ce je ka dai ku gaisa.”
“Ban yi ƙasa a gwiwa ba na je nai musu sallama, su kai banza da ni, nan na juyo a fusace, sai na ji Mati ya ja dogon tsaki sannan ya ce “Lusarin da ke son maso wani” Ni ko na mayar da martani, mu ka hargitse da rigima, da ƙyar aka raba mu”
“Bayan kwana biyu da wannan taƙaddamar, rannan da safe ina ƙailula, sai na ji ana buga mun ƙofar ɗaki. Na ce “waye?” aka amsa da “Mai gari ne” Ko da buɗewa ta sai na ga ashe shi da ƴan sanda biyu ne, kan na ce kwabo, ƴan sanda nan suka cacume ni, ina tambayarsu lafiya, suna amsawa da in mu ka je caji ofis ka ji”
“Ko da zuwanmu aka cilla ni sel (cell), sai yamma aka fito da ni, a ka kai ni wani ɗaki, wani Ɗan sanda mai buzu-buzun gashin baki a zaune kan kujera, ya ɗago kai ya kalle ni, ya kalli Ɗan sandan da ya ɗauko ni, ya ce “wannan shi ne ya yi kisan?” Ɗan sandan ya amsa da “eh, ranka ya daɗe” Ni kuwa na ce ” Ranka ya daɗe ni fa ba wanda na kashe” Ɗan sanda da mu ke tare ya dakan tsawa ya ce “Wa ya tambayeka? Nan ba a magana sai an baka izini”
“Ni ban ma san wanda ake zargi na kashe ba, sai da aka je kotu, wai ashe zargi kashe Mati ne, wanda mu ka yi faɗa da shi a kwanakin baya.Wai bayan mun yi faɗan ne, aka shiga ɗakinsa da daddare aka kashe shi, sai dai wai ba a ga gawarsa ba har yanzu, don haka bayan zargi na da kashe shi, sannan a lokaci guda ana zargi na da ɓoye gawarsa”
“Abu kamar wasa kamar almara, haka akai ta kawo shaida ana kafa hujja da faɗan da mu ka yi kwanaki, akai ta shari’a ana kawo shaidu, ƴan’uwan mahaifina su ka haɗa kai su ka na da shaidar ni na aikata abin da ake zargi na, kai har wannan yarinyar da mu kai faɗa da Mati akan ta, sai da ta bayar da shaidar cewa da kunnenta ta ji ma wai na ce zan kashe shi.”
“Daga ƙarshe dai aka haɗo baki da wani lauya, ya ce in amsa laifina, alƙali ya ce zai yi mun rangwame, haka aka yi, na amsa aka yanke mun shekara 25 a kaso.
“Wannan shi ne hukuncin farko da aka yanke a kotu, na kashe Mati”
Na ce “Na ji wannan to shi me ye gaskiyar labarin Mati, ina ya ɓoye, tsawon shekaru ba a gan shi ba, zan so in ji labarin yadda ka kashe Mati a karo na biyu har aka kawo ka nan gidan”
Baba Dattijo ya ce “In ka dawo gobe na ƙarƙare ma labarin yadda lamarin ya kasance, da kuma halin da ake ciki yanzu.”