Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Baba Dattijo Dan Bursin by Mukhtar Sipikin

Ko bayan na koma kashe gari ne, na tadda Baba Dattijo akan wani benci daidai wajen inda masu ziyara ke zama su tattauna da wanda ke tsare.

Bayan na yi masa sallama, mun gaisa, na dubi Baba na ce “Jiya mun tsaya a inda ka ce alƙali ya yanke ma shekara 25 a Bursin, akan zargin ka na kashe Mati, yanzu ni tambayata, ita ce shi Mati a ina ya ɓoye, sannan ya aka yi ka kashe Mati a karo na biyu har aka kawo ka nan gidan?

Baba Dattijo ya kalle ni, ya yi shiru, da alama dai kamar tunani ya ke, can sai ya kalle ni a karo na biyu, sannan ya ce “Wato na kewaya gidajen yari da dama na ƙasar nan, sai da na yi shekaru ɗai-ɗai har ashirun da biyu, rannan dai na ji an kira sunana, aka ce wai an duba fayel ɗina an gano wa’adi na ya cika, a zuciyata na ce ba su lissafa dai-dai ba, saura shekara biyu, amma nai shiru na rabu da su.

Bayan na fito daga bursin ne, na tsinci abubuwa da yawa sun canza, lallai duniya tana saurin canzawa, sai da tambaya sannan aka nuna mun tashar da zan samu motar ƙauyenmu, a tashar ne na haɗu da wani abokina da mu kai wasan ƙasa da shi, ya yi mamakin gani na, ni ma na yi mamakin ganinsa, a cewarsa, wai tuni an ce wai na mace. Har ya ke ba ni labarin yadda ƴan’uwan Mahaifi na su ka rabe dukiyata, da yadda kuɗin basu yi musu albarka ba.

A hirar mu ne ya ke faɗa mun cewa Mati yana raye bai mutu ba, hasali ma dai Mati yana ƙauyenmu, yana jiyya, wai ashe tunda fari sun haɗa kai da Ƴan’uwan Mahaifina ne, da ya tafi Ikko, bayan shekara uku abubuwa sun lafa, sai ya dawo a bashi ganimar sa ta dukiyata, shi kuma da ya tafi Ikko, sai ya yi zamansa can yana yawan bariki, yanzu ma abin da ya sa ya dawo saboda cuta mai karya garkuwar jiki ce ta ci lakarsa.

A yadda wannan abokin nawa ke faɗa mun shi ne, Mati yana can cikin wata bukka a gidansu, babu mai kula shi, kowa gudunsa ya ke, wai ana tsoron kar ya shafawa jama’a.

Ni kuwa da na ji yadda duniya ta juyawa Mati baya, sai na ci alwashin abin da zan fara yi inna je ƙauye shi ne, in haura gidansu in ɗau fansa.

Da isa ta ƙauye, jama’a su kai ta mamakin gani na, wasu murna, wasu tausayi, wasu baƙin ciki, ni kuwa ban kula ba, duk burina shi ne in haura gidan su Mati, in ga bayansa.

Ran nan da daddare na haura gidan su Mati, da nufin in maƙure shi, ina ta sanɗa har na kai ga bukkar da ya ke ciki, na shiga na ga yana ta nishi, na zo dai-dai kansa na tsaya, muka haɗa ido, na ce “Mati ka gane ni, ni ne Musa Ɗan Alhaji, da aka haɗa kai da kai, aka ce ya yi kisa, don haka na zo in ɗau fansa” Nan fa ya zazzare idanuwa, na sa hannu zan maƙure shi kenan, sai ya fara tari da ƙarfi, ƙila wannan ya sa ƴan gidan suka farka, aka shigo bukkar, na zabura zan gudu aka kama ni, aka danƙa ni ga hukuma akan cewa ni na kashe Mati bayan ko taɓa shi ban yi ba!

Da wannan aka kai ni kotu, a karo na biyu, cewar wai na kashe Mati a karo na biyu”

Sai dai na tambayi alƙali, cewar in har hukuncin farko da aka yanke mun, na kashe Mati ne, wanda kotu ta zartar mun da hukunci, yanzu kuma yaya kenan? Baba Dattijo ya yi murmushi ya kalle ni, ya ce ka ji labarina!

*Ranar 4 ga watan Disamba, na je kotu ɗauko rahota, na tarar ana shari’ar Baba Dattijo, alƙali ya ce “Musa Ɗan Alhaji kotu ta wanke ka, sannan ta tabbatar da cewar ba ka da hannu a mutuwar Mati a farko da yanzu, sannan kotu ta yi umarnin, a gurfarnar da wanda su ka kitsa maka maƙarƙashiya, sannan kotu ta na umarnin dukiyarka da aka raba gado, a dawo maka da ita.”

Karshe

© Mukhtar Sipikin

<< Baba Dattijo Dan Bursin 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×