Sai da sukai wata biyu kafin aka maida Safiyya da Fatima boko yayyen Safiyya ne sukai masu komai saboda shakuwar dake tsakaninsu, basu yima Saddiqa ba hakan yasa karatun ta ya tsaya, gashi Baba har yanzu baya magana kuma baya sai da fari bare baki, ƴan kuɗin da mukazo da su sun ƙare don dama ba wasu masu yawa bane, kuma ko suna da yawa ai zara bata barin dame yau da gobe bata bar komai ba.
Baban su Safiyya malan Sufiyanu shine yake taimakama su Fatima da abincin sa zasuci kafin zawan wani lokaci ya dai na don shima. . .
