Akshay Kumar
Na gaida gwani na gwanaye
wajen aiki ka wuce jaki,
Namijin duniya kake
sha-kundum kai ne tafki.
Majaujawar nasara ku ji
Wannan ai shi ne Akki,
Balbela da farinta
Kun san bata biɗar wanki.
Gwarzon maza sannu
Da ƙara shekaru nawa,
Tabbas ka yi mun gani
Kuma dole mu yo tafawa.