Skip to content
Part 5 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Rakul Preet Singh

Mai kyawun ido ce Rakul ɗina

Murmushinta ke yaye duhun raina. 

Rakul pretty mai kyau a idon kowa

Laɓɓanta masu taushi da jan hankalin kowa. 

Rakul taho gareni mu yi soyayya

Bahaushe da ‘yar Indiya. 

Idanuwana sun gaza ƙiftawa

Ƙwaƙwalwata ta gaza jurewa. 

Zuciyata ko ta gaza daurewa

Ruhina ya gaza jurewa. 

Rakul ke kaɗaice a idanuna

Sanyin raina abar sona. 

Ga ta gwana ƙwararra a fagen kafce

Ta yi zarra a fagen kyau an tantance. 

Kumatunta a koyaushe suna haske

Idan tana tafiya dole ka miƙe. 

Wutar kyau ake ce miki kyakkywa

Matar manya kin wuce wawa. 

Kai mai gigiwa kar ka je ga Rakul ɗina

Kai mai hanzari kar ka nufo Rakul ɗina. 

Kai mai tinƙaho kama kanka ka bar Rakul ɗina

Akul-akul ka matso ga Rakul ɗina. 

Ko kuma in sheƙe mutum babu batun sauƙi

Tunda motar so nake tuƙi. 

Rakul Preet a-ci-bal-bal na kyawawa

Rakul Preet sha kallo a gun kowa. 

Rakul Preet ke ce mai burge kowa

Ba kya faɗa ko rigima da kowa. 

Rakul Preet shalele a cikin mata

Na gaisheki jaruma a cikin mata.

Ni ne Haiman gwanin baiti 

Na Kaduna gwanin rero baiti. 

Nake waƙar akan titi 

Jikina ya ɗauki sitati. 

Ranar Litinin da sassafe 

Watan shida ne da sassafe. 

Shekarar dubu biyu cif 

Da ashirin da biyu cifcif. 

<< Ba’indiya 4Ba’indiya 6 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.