Skip to content
Part 10 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Jinkirin Taimako 

Yau ma kamar kullum, Hashim ya ɗebo ‘yan takardunsa zai je majalisin Malam Tsalha ɗaukar karatu. Sai faman sauri yake yi kamar zai tashi sama. Babu abinda ya tsana irin ta ga ya makara, saboda ba ya so a fara karatu ba tare da shi ba. Hashim irin mutanen nan ne da Allah ya wadata su da son karatu sosai. Hakan ce ma ta sa ya fara zuwa majalisin Malam Tsalha ɗaukar karatu.

Tafe yake yana tunanin irin girman rashin da zai yi idan Malam Tsalha ya bar garin. Domin ya ji yana ce musu zuwa ƙarshen wata mai kamawa zai koma ƙauyensu kacokan da zama domin ya ci gaba da yaɗa ɗa’awa. Shi dai Hashim ba don kar a ce yana da son zuciya ba da sai ya ce bai kamata malam Tsalha ya koma ƙauyen nan da zama ba, saboda tarin ilimi da Allah ya ba shi ya fi ƙarfin na mutanen ƙauyen.

Yana tafe yana wannan tunani ne sai ya ji kamar ana yi mishi magana ta baya. A nutse ya waiga domin ganin ko wa ke magana. Wata matashiyar yarinya ya gani wadda ba za ta haura shekara goma sha huɗu ba. Sanye take da hijabi har ƙasa, sai dai da alama ba cikin kwanciyar hankali take ba. Domin kuwa fuskarta da idanuwanta sun bayyana hakan ƙarara.

“Malam don Allah ko kana da ₦100 ka taimake ni da ita?”

Yarinyar ta tambaya tana mai haɗe hannayenta waje guda da alamar roƙo.

Tsananin mamaki ne ya sa Hashim sakin baki kawai yana kallon yarinyar ba tare da ya iya ce mata komai ba. Babban abinda ya bashi mamaki kuwa shi ne irin yadda yarinyar ta tambaye shi kai tsaye. ‘Kai matan wannan zamani dai kunyar su ta yi ƙaranci.’ Ya faɗi a cikin zuciyarsa a dai dai lokacin da yarinyar ta kuma cewa,

“Don Allah ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka. ₦100 kawai, don girman Allah.”

Wani abu da ke tattare da yarinyar da yanayin yadda tai maganar sun taɓa zuciyarsa sosai. Bai san lokacin da ya saka hannu a aljihu ba ya zaro duk kuɗin da ke aljihunsa ba. Sai dai me zai gani? Gudar ₦500 ce sai kuma gudar ₦10. Su kenan mishi gaba da baya. Duk da ya yi niyyar taimakon yarinyar ba zai iya miƙa mata ₦500 ɗin sukutum ba. Ga shi kuma babu ko masu irin shagon nan a unguwar balle su nemi canji. Kallon yarinyar ya yi ya ce,

“Kin ga gudar ₦500 ce da ni sai kuma ₦10, kina da canji in ba ki ₦200?”

Girgiza mishi kai ta yi alamar ‘a’a’

“To kin ga layin babu masu shaguna balle mu nemi canji. Ni kuma yanzu sauri nake yi zan je makaranta. Ki yi haƙuri in ina dawowa zan nemi canji a hanya in mun haɗu sai in baki. Yanzu sauri nake yi.” ya faɗi yana mai ganin yadda kalamansa suka yi mata nauyi.

“Na gode, Allah ya ba ka ladar niyya.” kawai ta faɗa sannan ta wuce.

Shi kuwa Hashim har ya kai makaranta babu abinda yake tunani face wannan yarinya mai abin mamaki.

Suna tasowa kuwa ya tsaya ya samu canji sannan ya nufo hanya yana kalle-kalle ko Allah zai sa ya ga yarinyar amma bai ganta ba. Can bayan ya wuto daidai inda suka haɗu ɗazu sai ya ga dandazon mutane kusan su ɗari sun zagaye wani abu ana ta hayaniya a wajen. Da kamar zai wuce dai sai ya je wurin wani mutum da ya gani mai alamar kamala ya tambaye shi lafiya ya ga mutane sun taru haka a wurin.

Sai mutumin ya ba shi amsa da cewa,

“Wani ne ya kashe wata matashiyar yarinya. Sai dai ya ce ba kashe ta ya yi ba, kuɗi ta nema a wurinsa shi kuma ya ce ba zai bata ba har sai yayi lalata da ita. A garin hakan ne yarinyar ta mutu. Yanzu haka ma jami’ai ake jira su zo su tafi da shi kafin matasa su halaka shi…”

Ai Hashim bai ko tsaya ma ya ƙarasa jin jawabin wannan mutumin ba ya fara tutture mutane domin ya kai ga mai laifin da ke zaune a tsakiya. Bayan ya sha turmutsitsi da mutane can sai ga shi ya fito tsakiyar fili. Yana zuwa kuwa yai arba da mutumin da ya aikata laifin, ga kuma wannan yarinya da ta tambaye shi ₦100 kwance a kusa da shi ba ta numfashi.

Nan take Hashim ya fara sambatu yana cewa, “laifina ne. Da na bata kuɗin nan da haka bai faru da ita ba. Laifina ne!

Haka ya ci gaba da yawo yana faɗa. Sanadiyar haukacewarsa kenan.

<< Bakar Kaddara 9Bakar Kaddara 11 >>

2 thoughts on “Bakar Kaddara 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.