Skip to content
Part 12 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Tsohuwa Da Barawo 

A daddafe tsohuwar ta samu ta miƙe tare da taimakon bangon ɗakin nata wanda a ƙalla ya kai shekaru arba’in da biyar da ginawa. Gidan kawai za ka kalla ka tabbatar da tsufan ba na wasa ba ne. Ita kanta tsohuwar, wadda ake kira Kande mai ƙuli, shekarunta za su kai kimanin tamanin da bakwai a duniya. Don har ta kai ga ma a ta wani gani sosai. Ba don lalura ta jiki ba ma, me zai kai ta yawan zaune tashi haka nan kawai da tsakar dare.

Kai hannu ta yi inda sandarta take, bayan ta ɗauki sandar sai ta nufi banɗaki domin ta biya buƙatarta. A daidai lokacin da ta shiga banɗakin ne wani gabjejen matashi ya shigo gidan kansa tsaye.

Yau dai kam lamarin ya kai mishi maƙura, jikinshi har ƙaiƙayi yake mishi saboda bai samu abinda yake so ba. Ƙwayar da ya saba wa kan sa da sha yau ta gagare shi samu. Ya bi duk wata hanya da zai iya bi domin ya samu kuɗin da zai siya ƙwayar ya sha amma abu ya faskara. Abokinsa Tillu ne ma da ya ga irin halin da yake ciki ya ce su raba ta wurinsa, ya ba shi guda ɗaya ya ɗan afa. Maimakon ta san ya ɗan ji dama-dama, sai ma ta ƙara haukatar da shi.

A yadda yake jin kansa, zai iya aikata komai in dai zai samu kuɗin da zai siya ƙwayar nan ya sha. Ta riga ta zame masa jiki, ba zai iya rayuwa babu ita ba. Tafiya yake yana tunanin yadda za a yi ya samu kuɗi kawai sai ya gifta da ƙofar gidan Kande mai ƙuli. Ya tabbatar ba a rasa ta da kuɗi, saboda duk layin wurinta aka fi zuwa siyan mai da ƙuli. Kuma da ma ita kaɗai ce a gidan, kuma ya saba shiga tun yana ɗan ƙarami. Don haka kawai sai ya yanke shawar shiga gidan ya yi mata sata.

Ɗakin da Kande ke kwana ya shige, kansa tsaye ya nufi inda take ajiye cinikin ƙuli da man da take siyarwa. Nan fa ya fara ‘yan lalube lalube. Ba a jima ba ya ga lalitar da take ajiye kuɗinta a ciki. Ya duba ya ga kuɗaɗen kuwa da ɗan dama, sai murna ta kama shi, domin ya tsinci dame kenan a kala. Daga nan sai ya juya da nufin ya yi tafiyarsa. Ai kuwa yana juyawa sai ya yi arba da ita. Ba kowa bace face Kande mai ƙuli. Hannunta na dama na riƙe da ‘yar sandarta, na hagu kuma na riƙe da fitilar ƙwai mai amfani da kalanzir.

Mamaki ne ya hana ta yin magana. Kuɗin cinikin ƙuli da mangyaɗarta ne wani ke shirin fita da su. Ko da yake ba ta gane ko wanene ba, ta tabbata dai ba kawo mata wasu ya yi ba. Kuɗin ta take burin siyan buhunan gyaɗa biyu gobe a kasuwa. Kuɗin da ta daɗe tana ba ta tara kamar su ba sakamakon ciniki da aka samu a ‘yan kwanakin nan da ya wuce tunani. Kayan nata har sun kusa ƙarewa ma, kwalbar mai ɗaya ta rage sai ƙuli ƙulli biyar.

Shi kuwa wani irin baƙin ciki ne ya turnuƙe shi, domin ya tabbatar da cewa yadda tsohuwar nan take da surutun tsiya tabbas tona mishi asiri za ta yi. Don haka sai ya yi wuf ya fisge sandar da ke hannunta sannan ya ce,

“In ki ka sake ki ka yi ihu sai na rafke ki da wannan sandar.”

Ko da jin muryar sai ta gane mai ita, don haka sai ta ce,

“Ai Bashari har ka fara buge mutane kana ƙwace abin hannunsu, yaushe lalacewar taka ta kai haka?

Ai ko da ya ji ta ambaci sunan shi, sai nan da nan ya shaƙe ta yana cewa,

“Tona min asiri za ki yi? Na ce tona min asiri za ki yi? Iye?!

Wata zuciyar ta ce mishi kawai ya kashe ta zai fi, amma yana ganin da wuya fa ya iya kashe tsohuwar nan. Can sai wata dubara ta faɗo mishi. Yarɓar da tsohuwar ya yi a ƙasa ya nufi inda kayan nata suke ya ɗauko kwalbar man. Ko da ɗauko ta sai ya dawo wurin Kande ya ce sai ta shanye kwalbar man nan. Tsohuwa kuwa ta ce atafau ba za ta sha ba. Nan fa ya sake shaƙo ta, tana tsinuwa da zaginsa yana ɗura mata man nan da ƙarfi da yaji har sai da ya duddule mata shi gaba ɗaya.

A wannan lokaci tuni man ya fara fito mata ta baki, hanci da wasu ƙofofin da basu ambatuwa. Nan take ta yanke jiki ta faɗi matatta. Shi kuwa ya yi gaba da lalitar kuɗin.

<< Bakar Kaddara 11Bakar Kaddara 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×