Son Banza
Yau Yaks a fusace yake, duniyar gaba ɗaya ta yi mishi zafi. Babban abin da ya fi ɓata mishi rai shi ne irin yadda ya yi ta ɗawainiya da sabuwar yarinyar da suka haɗu yau a gidan gala, amma daga ƙarshe wani ya yi gaba da ita. Ga shi har wasu abubuwa ya je ya sha masu yawa saboda ya fanshe ladar wahalar shi, amma yarinyar nan ta kwafsa mishi.
A haka dai ya dawo gida rai a ɓace, can wajen ƙarfe ɗaya na dare. Ya buɗe ƙofar ɗakin shi da ke ƙofar gida. . .