Skip to content
Part 19 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Son Banza

Yau Yaks a fusace yake, duniyar gaba ɗaya ta yi mishi zafi. Babban abin da ya fi ɓata mishi rai shi ne irin yadda ya yi ta ɗawainiya da sabuwar yarinyar da suka haɗu yau a gidan gala, amma daga ƙarshe wani ya yi gaba da ita. Ga shi har wasu abubuwa ya je ya sha masu yawa saboda ya fanshe ladar wahalar shi, amma yarinyar nan ta kwafsa mishi.

A haka dai ya dawo gida rai a ɓace, can wajen ƙarfe ɗaya na dare. Ya buɗe ƙofar ɗakin shi da ke ƙofar gida ya shige da nufin ya kwanta ya yi bacci. Amma bacci ya gagare shi. Can sai ya ji kamar ana kuka a ƙofar ɗakinsa, kuma muryar mace ce. Nan da nan kuwa ya fito. Yana fitowa kuwa sai ya yi arba da wata tsaleliyar matashiyar budurwa zaune a ƙofar ɗakin tana kuka. Nan da nan ya fara yi mata ‘yan dubaru irin nasu na ‘yan zamani da suka goge a harkar neman mata. Bai ko tsaya ma ya ji dalilin da ya baro ta da gida ba kawai ya ja ra’ayinta har suka shige ɗakinsa da da ita.

Cikin salo irin na wanda ya ƙware matuƙa a yaudara ya samu ya lallaɓi wannan yarinya har sai da ya keta mata mutunci. Da sassafe kuwa, ya fita siyo mata kayan karin kumallo saboda ya ji daɗin kasancewa tare da ita. Ko da ya dawo niƙi-niƙi da kaya a hannu kamar me sabuwar amarya. Sai ya ga wayam, babu wannan budurwa babu dalilin ta. A gefe kuma sai ya ga wata ‘yar ƙaramar takarda a ajiye. Nan fa ya ɗauko ta ya buɗe tare da fara karantawa kamar haka:

Zuwa ga Yaks sarkin yaudara da lalata ‘ya’yan mutane. Labarin irin ta’asar da ka ke yi na lalata da matan mutane babu inda bai kai ba wannan ne ya sa na yanke shawarar gwada ka. Ni sunana Suzy, kuma gogaggiyar ‘yar bariki ce ni. Kuma zuwa yanzu na kashe mazaje irinka sama da mutum biyar ta hanyar shafa musu cutar ƙanjamau. Cutar ƙanjamau ɗin da ke jikina ta kai matakin da da zarar mutum ya kwana tare da ni sau ɗaya shikenan ya kamu da ita, nima don ina shan wani magani ne ya sa har na kawo zuwa yanzu. Ba don komai nake yin hakan ba kuwa sai don saboda in hallaka mutane irinka da yawa ko na samu na rage mugun iri, saboda wani mai hali irin naka ne ya saka mini cutar. Na barka lafiya. In za ka ji shawarata, ka fara istighfaari tun yanzu ko za ka ɗan ji dama-dama. 

Ko da Yaks ya zo nan a karatun wannan wasiƙa, nan take ya zube ƙasa sumamme.

<< Bakar Kaddara 18Bakar Kaddara 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×