Duka Biyu
Halima mace ce kyakkyawar gaske. Irin matan nan ne da ba kasafai ake samun irinsu ba a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Kyawun da take da shi da kuma hasken fatarta suka sa maza da yawa ke rububinta. Sai dai ita kuma babu abin da ta sa a gaba face son kuɗi.
In dai ta ganka da 'yan kuɗaɗe, to ba za ta rabu da kai ba har sai ta ga bayansu. Hakan ya sa ta yi ta sharholiyarta. Su kuwa maza 'yan ashana suka yi ta yi mata ruwan kuɗi. . .
Nice
Thanks