Skip to content
Part 21 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Duka Biyu

Halima mace ce kyakkyawar gaske. Irin matan nan ne da ba kasafai ake samun irinsu ba a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Kyawun da take da shi da kuma hasken fatarta suka sa maza da yawa ke rububinta. Sai dai ita kuma babu abin da ta sa a gaba face son kuɗi. 

In dai ta ganka da ‘yan kuɗaɗe, to ba za ta rabu da kai ba har sai ta ga bayansu. Hakan ya sa ta yi ta sharholiyarta. Su kuwa maza ‘yan ashana suka yi ta yi mata ruwan kuɗi. Yau wannan ya ja ta nan, gobe wani kuma ya ja ta can. Babu otal ɗin da ba ta sani ba, balle kuma gidan rawa ko kuma wurin cin abinci na alfarma. A haka dai har ta samu wani hamshaƙin mai kuɗi suka yi aure. 

Bayan sun yi auren, sai ya zamana hidimar daban, ta gobe daban, ta jibi ma da ban. Mutumin nan yi yake, amma kamar baya yi. A kwana a tashi dai har ya fara gajiya. Daga nan ne fa suka fara samun matsala. Rikici dai ya kai rikici, abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa har ya kai ga ta yi yaji. Bayan sati biyu ya dawo da ita. Sai dai duk da haka bata canza zane ba. Hakan ya sa daga ƙarshe dai dole ya sake ta. 

Bayan ta koma garinsu mai suna garin zawarawa, sai ta ci gaba da tsula tsiyarta. Ana nan dai har ta samu wani matashin mai kuɗi da take yi wa so na fitar hankali. Shi kuwa ya dinga watangaririya da ita. Amma ta nace mishi. Da sannu dai har ta shawo kanshi aka sa musu rana.

Ana saura kwana biyu biki ya yi hatsari ya mutu. Tashin hankalin da Halima ta shiga ciki ba zai misaltu ba. A sanadiyar mutuwar wannan miji nata ne ta kamu da cutar hawan jini, daga ƙarshe ma dai ta samu cutar shanyewar ɓarin jiki. Tun daga nan duk samarin nata suka guje ta. Ta koma abar tausayi. Ruwa ma sai an bata. Wannan lamari ya sa ta yi nadama sosai a rayuwarta. Sai dai kuma nadamar ta zo mata a daidai lokacin da ba ta da amfani. Domin kuwa lokaci ya ƙure mata.

A haka dai ta ci gaba da rayuwa, ta yi magiyar duniya mijinta ya maida ita amma ya ce shi ba zai iya ɗawainiya da ita ba. Haka dai ta rayu har zuwa lokacin da rai yai halinsa. Abun ya zama mata duka biyu. Ba ta ga tsuntsu, ba ta ga tarko.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 20Bakar Kaddara 22 >>

2 thoughts on “Bakar Kaddara 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×