Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Kunama A Cikin Takalmi 

Sanda ya makara ƙwarai yau bai je gona ba. Matarsa Harira rigima take jin yi. Babu irin yadda bai yi da ita ba kan ta huce amma ta ƙi. Tun daren jiya ake abu guda ɗaya amma an kasa cimma mafita guda. Ita so take da safe a yi ɗumamen tuwo shi kuma ya nace sai an yi kunu. Wannan shi ne asalin rikicin.

Da gari ya waye, nan ma wani sabon rikicin ne ya ɓalle, domin cewa ta yi ba za ta girkin ba. Duk abinda yake so sai dai ya tashi ya girka da kansa. Shi kuma ga shi ba shi da ko asi balle ya fita waje ya ci wani abu. Abun duniya fa duk ya bi ya ishe shi. Haka nan ya je gindin murhu ya yi goho yana hura wuta. Kafin ka ce wani abu tuni ya fara hawaye. A haka dai da ƙyar ya samu ya haɗa abinda zai karya. Ita kuwa ja’irar sai masifa take balbala mishi.

Haka dai ya yi banza da ita har ya gama karyawa. Ko da ya gama, sai fa ya juyo kanta yana tambayar dalilin da ya sa ta ƙi haɗa mishi kayan kalaci kuma take masa masifa. Dama ta saba da irin wannan hali, ba yau ta fara yi masa hakanan ba. Da ya fusata, ya samu miyar tsanya yai ta ce mata karɓi. Ita kuwa sai ihu take tana ta tuba amma bai daina bugunta ba har sai da ya tabbar da ta yi laushi.

Gama bugun nata ke da wuya kuwa maƙwafcinsa Halilu ya yi mai sallama ya zo ga wani aiki ya samu ya fito su tafi tare. Ko da jin wannan batu sai ya yi maza ya fara shiri. Cikin hanzarinsa ne ya ɗauki takalma ya sa ba tare da ya kakkaɓe ba. A hanzarce ya tura ƙafa cikin takalman nan sau ciki . Ashe wata kunama ta kwana ciki bai sani ba. Nan fa ta dinga ba bashi abin. Shi kuwa sai tsalle yake yana ihu. Garin tsalle-tsallen ne ma ya ƙare ya faɗa rijiya. Da ƙyar aka tsamo shi. 

<< Bakar Kaddara 22Bakar Kaddara 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.