Skip to content
Part 24 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Mugun Miji 

Adamu na tsaka da barci ƙarar wayarsa ta tashe shi. Wani irin bacci yake yi ne mai daɗin gaske. A cikin wannan barci nasa kuwa, wani irin mafarki ne ya ziyarce shi mai ban sha’awa. Cikin tsananin takaici ya kai hannunsa ya datse kiran ba tare da ko dubawa ya ga wanene ke kiran ba. Sabon ruri wayar ta ɗauka tana mai neman agaji. Dogon tsaki ya ja sannan ya ɗauko wayar ya duba. Ƙanwar matarsa ce Lubabatu, takaici ne ya rufe shi a karo na ba adadi tun bayan lalacewar wayar matar tasa. Shi dai kam ba zai iya cire kuɗi a wannan marrar da ake ciki ya siya mata waya ba, amma irin wannan yawan kiraye-kirayen da ‘yan uwanta ke damunsa da shi tun bayan da ta roƙe shi ta sa layin wayarta a cikin tashi wayar ya fara isar shi haka nan. Wani tsakin ya ƙara ja sannan ya danna maɓallin ɗaukar wayar.

“Assalamu Alaikum. Don Allah yaya Adam Anty na kusa?” Luba ta faɗa hankalinta a tashe, da alama ma dai kuka take yi.

“Bacci take yi. Lafiya dai ko?”

Ya ba ta amsa tare da tambayarta a ƙagauce.

“Ma… Manmu… Ce.. Ta… Rasu ya… Zu!”

Ta faɗi tana mai fashewa da kuka.

“To shikenan zan faɗa mata.” ya faɗa a taƙaice tare da katse wayar. Wani dogon tsaki ya ƙara ja sannan ya koma ya kwanta yana ƙunƙuni a cikin ransa. Don wata tsohuwa ta mutu kawai shikenan sai ya zama dalilin da zai sa a hana shi bacci? Mtsww! Ya sake jan wani tsakin.

Kashe gari da safe bai faɗa wa matarsa cewa mahaifiyarta ta rasu ba. Ko da ya yi wanka ya karya kawai sai ya fice abinsa. Bai ko kira su ya yi musu ta’aziyya ba. Ita kuwa Mairama da wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ta tashi. Komai a dagule take jinsa. Ta so ta kira gida ta ji ya lafiyar mahaifiyarta wadda ke ta fama da jinya, amma ganin irin yadda Adamu ya yi kinini da fuska ne ya sa ta haƙura. Ta san halinsa sarai, ba wani abu bane a wurinsa ya yi mata shegen duka da safiyar nan. Ita ba abin ta ce za ta je ba. Ba wani nisa ke tsakaninsu da gidansu ba, amma sai ya ga damar barin ta ta je. Addu’a ta yi ta yi na Allah ya kawo ɗaya daga cikin ƙannenta gidan ta ji lafiyar mahaifiyar tata.

A daddafe ta samu ta yi wanka. Sai dai ko ruwa ta kasa sha. Ji take jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wadda aka yi wa sata. Tana nan zaune ta rasa abinda ke mata daɗi sai ga ƙanwarta Lubabtu ta shigo gidan a firgice tana kuka. A nan ne take faɗa mata rasuwar mahaifiyar tasu, ta kuma sanar da ita cewa ta kira Adamu tun daren jiya ta sanar mishi da rasuwar. Mairama babu abinda take yi face kuka tun da ƙanwarta ta fara maganar.

Wani irin gululun baƙinciki ne ya zo ya tsaya mata a wuya. Ta rasa da wanne za ta ji. Da baƙincikin rasuwar mahaifiyarta ko kuma da baƙincikin rashin adalcin mijinta. 

Ba ta gama tantance halin da take ciki ba ta ga mutane sun shigo cikin gidan da sallama ɗauke da gawar mijinta jina-jina. Ai ba su ma kai ga faɗa mata yadda aka yi ba ta faɗi ƙasa sumammiya. 

<< Bakar Kaddara 23Bakar Kaddara 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×