Abinda Ka Shuka Shi Za Ka Girba
An yi wata mata mai suna Rakiya. Inda fuk inda ake neman masifaffiyar mace to Rakiya ta wuce wannan wuri. Saboda masifarta ne ma ta kasa samun mijin aure da wuri. Ana nan wata rana sai kuwa ta ƙyallara ido ta ga wani mutum, ta kuwa kamu da sonsa. Don haka ta ce ida duniyar nan ba ta auren kowa sai shi. Nan fa ta yi ta ƙoƙarin ganin ta shawo kansa domin ya aureta. To shi kuwa wannan mutumi yana da mata ɗaya da yara biyu namiji da mace, kuma suna zaman lafiya sannan bai shirya ƙara aure ba. Don haka sai ya yi bata haƙuri domin dai su rabu lafiya. Ko da Rakiya ta fahimci cewa ba za ta samu abinda take so ba, sai ta shiga bin bokaye har sai da ta samu bokan da ya yi mata asiri ya kashe waccan matar ya kuma shawo mata kan mijin. Ba tare da ‘yan uwanshi sun so ba, haka ranar bakwai ɗin uwargidan da ta rasu ita kuma ta shigo gidan a matsayin amarya.
Ba a ɗauki wani lokaci ba komai na gidan ya sauya, domin sai abinda ta ce ake yi. Bayan wata biyu da auren ne ta kama ƙaramar ‘yar mai gidan ta jefa rijiya da gangan ta rufe har sai da ta mutu sannan ta fara kukan a kawo mata ɗauki ‘ya ta faɗa a rijiya. Namijin zai yi magana ta make masa baki ya har sai da yai jini. Daga nan ta ci gaba da gana mishi azaba iri-iri. Saboda dukan da take masa in mutum ya ga jikinsa sai ya ɗauka jakin daji ne saboda roɗi-roɗin kwailewar dukan da yake sha kullum a hannun matar uban. Daga ƙarshe dai ta sa uban ya kore shi daga gidan. Shi kuwa yaron sai ya koma gidan wani kawunsa da zama.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yaron yana ta karatu. Kuma duk sati sai ya zo ya gaishe da uban amma ba ya ko amsawa, ita ma ko ya gaishe ta ba ta amsawa. A haka dai har ya girma ya samu aikin yi a kamfanin Hammadi Global Enterprises da ke nan kusa da su. Bayan wani ɗan lokaci kaɗan sai uban ya rasu, sai dai kafin ya rasu ya bar wa ɗan wasiyyar duk abinda zai yi ya tabbatar ya kula da matar nan tasa Rakiya. Ita kuwa duk tsawon wannan lokaci da aka ɗauka ba ta samu haihuwa ba.
Bayan an raba gadon mamacin, sai ta shiga fantamawa abinta, kafin wani lokaci ‘yan kuɗin suka ƙare. Daga nan fa sai ta kafa wa wannan yaro ƙahon zuƙa. Ya zamana bini-bini ita ce ba ta da kaza, kazan ta ya ƙare. Shi kuwa saboda biyayya bisa ga wasiyyar mahaifinsa, sai ya zamana ba ya ko ɓata ransa game da wannan. Wani lokaci ma tai ta yamaɗiɗi da shi a gari wai baya mata komai amma duk da haka bai damu ba. Ana nan har ya yi aure, ranar da aka kawo amaryar da ta ga irin tabban da ke jikinshi sakamakon dukan da rakiya tai ta yi masa tun yana ƙarami ta ce ba ta zama da shi. Domin bata yarda shi mutum ba ne. A cewar ta, babu mutumin da za a yi masa irin waɗannan tabbai da duka kuma ya rayu. Haka nan aka raba auren tunda ta ƙi zama. Daga baya dai ya samu wadda ta aure shi a hakan.
A kwana a tashi, ran nan sai Rakiya ta kwanta cutar ajali. Ya zamana wannan ɗa dai shi ke kula da ita da komai nata. Musamman ya ɗauki hutu a kamfanin da yake aiki domin ya kula da ita sosai. ‘Yan uwa kuwa kowa ya guje ta. Da dai ta lura cewa wannan cuta ba ta tashi ba ce. Sai ta dinga kuka tana roƙon wannan yaro da ya yafe mata irin abubuwan da ta yi masa. Shi kuwa in ta faɗi irin wannan maganar ba ya cewa komai. Sai dai duk da haka bai daina kula da ita ba. A ranar da za ta rasu, a bainar duk jama’ar da ke ɗakin asibitin ta ke roƙonsa ya yafe mata. Har ma wasu daga cikin mutanen wajen suka saka baki game da haka. Shi kuwa sai ya ce da ita, ‘Ko da ace zuciyata na so in yafe miki ba zan iya ba. Domin kuwa kin yi min abinda ba zai iya yafuwa ba a gare ni. Hatta wannan kulawar da nake baki ina yi ne domin cika wasiyyar mahaifina ba wai don daɗin raina nake yi ba.’ daga nan sai ya fita domin ya siyo wasu abubuwa da ake buƙata, sai dai kafin ya dawo har ta cika. Haka ta yi mutuwar kare tana shure-shure.