Skip to content
Part 8 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Baƙar Ƙaddara

A birnin Kano, an yi wani mutum da ke jan tifa ana kiran sa da Audu mai Tifa. Audu ya fara bin tifa ne tun yana ɗan shekera goma. Saboda haka da wannan sana’a ya taso tun yarintarsa har zuwa yanzu da yake da mata biyu da yara shida. Tun yana bin tifar mai gidansa har ya kai ga siyar tasa ta kansa.

Wannan sana’a kuwa ita ce dai yake yi rani da damina. Daga ɗiban yashi, ƙasa, duwatsu har kayan aiki na ma’aikatu ma. A taƙaice dai kowa da wannan sana’ar ya san shi. Babbar matsalar Audu mai tifa ita ce zuciya. Abu ƙanƙane sai ya sosa mishi rai ai ta kai ruwa rana. In kuwa ba hankali aka yi ba yanzun nan sai abin ya koma rikici. Sai dai duk da wannan zuciya tasa, yana da cika alƙawari kuma baya tauye wa na ƙasa da shi haƙƙinsa.

Wata rana, ana I gobe za a fara azumin watan Ramadan sai tsautsayi ya sa Audu mai Tifa ya buge wani matashi ya faɗi ya mutu. Wannan abu fa ya sa Audu mai Tifa yin sanyi sosai game da lamarin Duniya. Bayan an biya diyya an yi komai. Da aka sha ruwa, bayan sallah da kwana biyu sai Audu mai Tifa ya fara azumtar kwanaki sittin da zai yi na kaffara. Ranar da ya fara wannan azumi kuma dai sai wani tsautsayin ya ƙara gittawa ya buge wani magidanci shima ya mutu, bai ko shura ba. Abin fa ya taru yai mishi yawa. Can kuma dai, bayan ya yi kamar guda arba’in sai ya sake buge wata budurwa ana gobe bikinta. Nan fa akai ta sururutu a garin nan kowa na ta faɗin albarkacin bakinsa. Ƙarshe dai sai da aka siyar da tifar Audu sannan aka samu aka biya diyyar ran wannan budurwa. Audu ya koma kamar mabaraci. Ga haƙƙoƙin rayuka bisa kanshi, ga azumi da ya zamo mishi wajibi sai ya yi. Ga kuma ci da iyali wanda ya rasa yadda zai yi don babu tifar aiki. Rannan sai ya tafi wurin wani abokinsa mai suna Alti domin ya taimake shi ya bashi tasa tifar ya dinga yin aiki da ita kafin Allah ya sa al’amura su warware masa.

Alti ya tausaya masa bisa wannan hali da yake ciki, ya bashi tifa ɗaya daga cikin guda uku da yake da su sannan ya ba shi ɗan wani abu da zai yi amfani da shi zuwa wani lokaci. Ranar da ya fara fita da tifar ya buge shanun wasu fulanin tashi akai ta shari’a. Daga ƙarshe dai jama’ar garin suka haɗa mishi kuɗi da kaya suka ce don Allah ya kwashe iyalinsa ya bar garin ya koma wani.

<< Bakar Kaddara 7Bakar Kaddara 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×