Skip to content
Part 13 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Kuka take tamkar ranta zai fita, ga wani gumi daya wanke mata fuska duk sanyin da ke gauraye ɗakin.

“Wallahi ko ki fiddoman ɗiyata ko kuma kiyi ta bakin aurenki, kinji na faɗa maki, ace yau tsawon wata hudu kenan kinturata biki ashe bama bikin danginku bane can biƙin ƙawar dana hanata zuwane, tsabar kin ɗaukeni banda mutumci a wurinki shine kikayi mani ƙarya,to kinji na rantse maki indai ɗiyara ta ƙara kwana goma bata dawoba kema saidai kitafi gidanku.”Alhaji Abdallah
Ya ƙarashe maganar yayi waje ranshi a matuƙar 6ace.

Cikin muryar daga jinta kasan tasha kuka harta gaji, ga idanunta da suka kumbura saboda kukan da ta sha ta fara magana;
“Yau ni Zaliha nashiga ukku, watan tonen asirina ya kama, nibama sakin da Alhaji zai mani ke damuna ba face muggan mafarkan danike da Salma, ya Allah nagane kuskurena Allah ka maido mani ɗiyata gida lafiya.”
Kukan dayaci ƙarfinta ne yayi sanadin haɗiye sauran maganar.

*****
“Habib wai bazaka cire damuwar yarinyar nan aranka bako?, yau wata huɗu da tafiyar ba ba bamo ba labari ga Ɗanka kanata fama dashi,sai wani ciwo ya sameka ita batama san kanayiba tana can wurin biki, to munyanke shawara da kawunka ga Hanan nan da aurenta ya mutu ƴar ƙanwata, yarinya mai hankali da natsuwa, gata yarinyace ko haihuwar fari batayiba,tunda ta gama idda ranar Juma’ar nan za’a ɗaura maku aure ranar zata tare tunda komi nata yana nan, Allah yasa wannan za6in danayi maka yazame maka Alkhairi arayuwarka.”

Tunda ta fara maganar kanshike sunkuye aƙasa cikin girmamawa da yin na’am da za6in da Hajiyarsu tayi mashi yace;

“Amin Hajiya, insha Allah nimai biyayyane a gareki, bazakiyi kuka daniba.”

“Nagode Habib, Allah yayi maka albarka, Allah ya shirya maka zuri’a.”

“Amin Hajiya.”

Yaune jama’a da dama suka shaida ɗaurin auren HABIB BELLO da amaryarshi HANAN HANIF, ɗaurin aurene daya samu halattar manyan ƴan kasuwa da ma’aikatan gamnati harma da ƴan siyasa ta 6angaren abokan Alhaji Bello mahaifin habib da kuma shi kanshi Habib ɗin.

Ƙarfe huɗu dai_dai aka ɗauki amarya zuwa gidan mijinta.

Zama suke irin wanda inka gani saiya birgeka, Hanan wayayyar yarinyace mai ilimin addini dana boko, shiyasa bata sha wahalaba ta sace zuciyar Habib tasamu babban gurbi azuciyarshi ta zauna daram, ga Walid da take kula dashi ta maidashi tamkar ɗan da tahaifa acikinta, shiyasa Habib ke ƙara ƙaunarta.

Allah sarki Habib duk auren dayayi bai manta da Basma ba, kullum cikin yimata addu’a yake, saboda muggan mafarkar da ye da ita, yana mata fatan tadawo dumin har yanzu akwai ƴar sauran soyayyarta kaɗan azuciyarshi.

*****
Uban tagumin da ta yi hannu bibbiyu ta lula duniyar tunanin Rabi’un ta jikanta ɗaya ƙwali daya rage mata, da yau har tsawon wata Huɗu bai dawoba shiru kamar Malam yaci shirwa, abinda yafi ɗaga mata hankali shine munanan mafarkan datake tana ganinshi cikin mawuyacin hali.

Kukan da Busurulle ya fasa da ƙarfine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.

“Kai nikam nagaji dakai wannan bunsuru, ga abincinka yau ya ida ƙarewa, yanzu nike tashi in kai ka wurin tsalha sarkin fawa in saida in raba ƙuɗin biyu in sawo kyan abinci sauran kuma in ajema ɗan kaka inyadawo.”
Ta miƙe ta zari mayafi ta kwance bunsuru tajashi tayi waje.

Tsalha sayen wulaƙanci yayima bunsurun, wai yunwa ta kamashi ya saya dubu ukku.

“Kai tsalha kaji tsoron Allah, wannan Bunsurun alalace ai zaiyi dubu goma.”
Ta ƙarashe maganar tana kamo iggiyar ƙafar Bunsurun.

“Iyakar yadda na saya kenan hajiya, nifa bama zani sayi Bunsurun nan ba, saboda jikanki ko kin saidashi inya dawo nasan nizaima wulaƙanci in biyashi.”

“Kai arr! Shiyasa kai mashi tayin wulaƙanci?, to nima nafasa saidawa.”
Taja Busurulle ta mai da gida ta ɗaure tana mai addu’ar Allah ya mai do mata Rabi’unta gida lafiya.

*****
“Umma wai yaushe Aunty Biba zata dawo.”?
Ƙanwar Biba ta jefoma Ummansu tambayar.

Tagumin da ta zuba da hannu biyu ta cire tana mai kallon Siyama.

“Siyama ku taya Habiba da addu’a, insha Allah jikina yana bani tabbas Habiba nacikin mawuyacin hali, duba ga muggan Mafarkan da nike da ita, insha Allah darajar addu’ar danike mata zata dawo gidannan.”

“Umma ki kwantar da hankalinki insha Allah aunty zata dawo ta samemu cikin ƙoshin lafiya.”

“Amin siyama, Allah ya maidota lafiya.”

Alwallah sukayi tareda kabbara sallah suna masu kai ma Allah kukansu, domin Allah gafurun rahimunne.

*****
Giɗan yayi tsit, Umma da Hanifa kowa da abinda yake saƙawa cikin zuciyarshi.

“Ni ko Umma ƙwanan nan sai inta ganin Yaya Jafar cikin mawuyacin hali cikin wani baƙin jeji.”

Jin wannan maganar ya sanya jikinta ya ƙarayin sanyi, cikin ƙarfin hali da nuna mafarki ba duka ne gaskiyaba ta fara kwantarma Hanifa da hankali.

“Marfarki ba duka ne gaskiya ba kinji Hanifa, Yayanki yana nan dawowa kiriƙa yimashi addu’a inkinyi sallah , yana nan dawowa insha Allah.”

“To Umma Allah ya maidoshi lafiya, amma Umma mike danmunki kwanan nan sai inta ganinki cikin damuwa.”?

Duk yadda take ƙoƙarin 6oye damuwarta amma tasan fuskarta ke fallasa sirrin zuciyarta har agano halinda take ciki game da mafarkan da take da Jafar.
“Lafiyata lau Hanifa, wani lokaci ina fama da zazza6i shiyasa kike gani na haka, amma nasha magani, yanzu tashi kiyi shirin islamiyya lokaci yayi kadaki makara.”

“To Ummu.”
Ta miƙe tahau shirin tafiya makaranta.

Wasu guntayen hawaye Ummu ta sharce tare da addu’ar Allah ya maido mata ɗanta gida lafiya.

Zaune suke Saman kujerun Alfarmar da suka zagaye tsakiyar falon.

Kallo ɗaya zakayi masu kasan hutu ya zauna ajikinsu.

Hajiya kubra momyn jamcy dogon tsoki taja tare da kaɗa kanta ta fara magana cikin takaici;

“Wato idan Jamcy ta dawo gidannan ta iskeni saina karya mata ƙafar gaba data baya, shegun ƙafafu kamar na Zal6e, yau wata Huɗe kenan sun faki idanunmu sun tafi ganin ƙwam.”

Hajiya Hafsa mahaifiyar Kulu ita ta amshe zance;

“Ke kike faɗi anaji, wato ni idan Kulu ta dawo innayi mata Wata zauna sai ƙasusuwanta sunkarairaye, kaga yarinya ta sani cikin masifa mahaifinta gani yake kamar nice na sanyata ta tafi Baƙin dajin nan ganin ƙwam.”

“Ai ni narasa yadda zaniyi da Daddyn Nas, kullum cikin tada mani hankali yake yana tunanin dasa hannunna nasani Nas yabar gida, ai yadda Nas ya tada mani hankali in Allah ya maidoshi saina gwara kanshi da bango ko naji sauƙin abinda nikeji azuciyata.”
Hajiya asabe Mahafiyar Nas ta ƙarashe maganar tana huci.

“Ai ni dangin Mahaifin Tk gani suke kamar dan Mahaifinshi ya rasu shiyasa nabarshi sakaka harya tafi dajin nan, wallahi sun sakoni gaba niduk nafiku shiga matsala.”

Ranar haka suka wuni suna jimamin halinda ƴa’ƴansu suka jefasu ciki, yamma nayi kowacce ta nufi gidanta cike da jimamin halinda suke ciki.

*****
Ihu Rabson keyi iyakar ƙarfinshi ga hannunshi nata zubar da jini.

Ganin halinda yake ciki yasa Jafar rugowa yana duba yatsan, ashe duk ihun da yake yatsan yankarshi kawai akayi ba gundulewa yayi ba.

Tsoki Jafar yayi ganin asheba datse yatsan akayiba tsabar rikicewa sai cewa yake yatsanshi ya gundule.

“Kanatsu Rabson, yatsanka ba gundulewa yayi ba yankarshi akayi.”

Ihun da yake ya tsaida;
“Da gaske kake Jafar yatsana nan.”?
Ya jefoma Jafar tambayar yana mai kallonshi.

“Eh yana nan.”
Ya faɗa a taƙaice.

“Alhamdulillah, Allah nagode maka ashe banida rabon zama Rabson gundul, Allah na godemaka.”

Biba kallabinta ta kwace ta yaga aka ɗaurema Rabson Hannu.

Zaune sukayi sunyi jigum_jigum ga yunwa ga ƙishirwa da suka addabesu.

6angare ɗaya kuma ga jikin Basma nata ƙara rikiɗewa.

“ALHAMDULILLAH.”
Jafar ya furta fuskarshi ɗauke da murmushi.

Kallinshi sukayi cikeda son jin abinda ke faruwa suka furta, “Jafar miya faru.”?

<< Bakar Tafiya 12Bakar Tafiya 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×