Skip to content
Part 16 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Kamar yadda kibiya ke fita daga cikin ƙwari haka Mandiya tayi tsalle ta fito daga cikin ruwan, abin al ajabi tana fitowa kafin tayi ƙoƙarin guduwa kamar an fizgota haka ta faɗa cikin ruwan, tun tana ihu iyakar ƙarfinta har tayi tsit.

Su Jafar da suka samu suka baro cikin ruwan jin shirun Mandiya tayi yawa yasa suka fara tunanin ya zasuyi su samu su fiddota.

Jafar kallonsu Biba yayi fuskarshi da alamun damuwa ya fara magana.
“Yanzu ba lokacin yin dogon tunani bane, kamata yayi musan yadda zamuyi mu ceci rayuwar Mandiya kada ruwan nan yayi mata wata illar, garin naiman magani kuma asamu wata matsalar, niba muharramata bace da sai in fiddota, amma cikinku yakamata ku yi ƙoƙarin fiddata a ruwan nan.”

Tsuru_tsuru sukayi tamkar basuji abinda ya faɗaba, Biba ita tayi ƙarfin halin fara magana.
“Jamcy da Kulu ku yakamata mu haɗa karfi mu fiddota tunda mune mata.”

“Wa! Allah ya tsare gatari da sarar suka, haka kawai kinta6a ganin wanda yakai kanshi ga halaka yanaji yana gani?, to nidai har yanzu ina son rayuwata inku bakuda buƙatar taku.”
Jamcy ta ƙarashe maganar tana jan kitson attach ɗinta dayaji wuya yayi burcin_burcin.

“Mtssw! Allah wadaran naka ya lalace, yanzu ke ki taimaka aceci rayuwar baiwar Allah amma kitsaya kina 6ata mana lokaci, Biba zo muje ni koda wannan aikin da zaniyi zai zamto ƙarshen rayuwata ba shakka zani aikata, ina roƙon Allah sanadinshi yasa mahaifana su yafe mani laifinda nayi masu na barin gida batare da izininsu ba.”
Tana ƙarashe maganar taja hannun Biba suka nufi ruwan.

Suna shiga sukayi nasarar samun Mandiya amma babu alamun tana motsi.

Da ƙyar suka samu sukayi nasarar fitowa da ita, kowa yayi tsit ganin kamar Mandiya ta mutu.

Fuskarta da suka kalla ganin ta koma suffarta ta ainahi yasan yasuka ji wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyoyinsu.

Motsi da suka ga hannunta nayi wadunsu suka dare daga wurin, Rabson bayan Jafar ya koma yana leƙe yaga yadda zata kaya.

A hankali take ƙoƙarin buɗe idanuwanta da sukayi mata matuƙar nauyi,ɗaya bayan ɗaya tariƙa ƙarema su Jafar kallo.

Yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana murmushi ɗauke a fuskarta.

Rabson gani yayi kamar shi ɗaya take kallo tana dariya tana lashe baki, ihu ya ƙwalka tare da cikuikuye Jafar yana ƙoƙarin kayar dashi.
“Innahumin sulaimanu…, La’ilaha illallahu, shikenan kallona take tana lashe baki zata cinyeni, wayyo nashiga ukku lokacina yayi, Busurulle da Salma zaku zama marayu, shikenan Kakata yau zani mutu in barki.”

Ganin Rabson na ƙoƙarin kayarda Jafar ya sanya Jafar mangarema Rabson geya.
“Kai ko anya zaka yi hankali?, mufa take yima murmushi ba kaiba, yanzu ta dawo ainahin Mandiyarta ba horror bace, kadawo cikin hankalinka.”

Jin wannan maganar tasa Rabson ƙara kallon Mandiya da kyau, gani yayi ita ɗince ta dawo ainahin mutum ɗinta.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadar;
“Wai Allah nagode maka, ashe inada sauran shan ruwa nan gaba, inada rabon auren Salma masoyiya.”

Kaɗan ta hana su dara ganin wannan wauta ta Rabson.

Wurin Mandiya suka matsa suna mata sannu.

Amsawa taruƙayi hawaye na wanke mata fuska tana ƙara nadamar rayuwar da tayi abaya, tayi alƙawali har cikin ranta insha Allah bazata ƙara karuwanci ba har ƙarshen rayuwarta.

Jafar ya ji daɗi sosai, domin ya tuno da wani hadisi dayace, _KASHIRYAR DA MUTUM ƊAYA YAFIYE MAKA JAJAYEN RAƘUMA_
Allah sukayi ma godiya suna masu ƙara tawakkali da addu’a, domin sai yanzu suke ƙara tabbatarwa a baya sunyi sakaci da addu’a.

Yunwar dake cikinsu ce ta fara addabarsu, tunanin inda zasu samu abinda zasuci suka farayi, sallolinda ake binsu suka farayi, inda Biba ita tafarayi sannan ta anshi ɗankwalin kulu ta yafa ta basu hijabinta da ta Sha gwagwarmaya amma har yanzu tana nan saidai cukuikuyewa da tayi.

Bayan gama sallar wasunsu kwanciya sukayi suna hutawa, su duka sun lula duniyar tunani.

Ƙarar da sukaji ce ta sanya su miƙewa tsaye tare da dunƙulewa wuri ɗaya duna masu dafe kunnuwansu dake bara zanar tarwatsewa.

Tsagaitawa sukayi tare da rufe wangama_wangaman bakunansu.

Ɗago kawunansu sukayi jin ƙarar da sukeji ta tsaya, abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ya sanyasu ƙara matsewa wuri ɗaya tare da fara sallallami wasu kuma suka fara hawaye tareda sabbatu.

Wasu irin maridan Aljanune mace da namiji tsaye fuskokinsu a matuƙar murtuke ba alamun imani a tattare dasu.

Namijin ya wangame baki ya fara 6a66aka dariyar da ta haddasa dajin girgiza, tsaida dariyar yayi tareda tur6une fuska ya nunasu da yatsa ya fara magana.
“Yau kwananku yazo ƙarshe, a baya kunyi nasara a kanmu mun iskeku kuna bacci kun ƙona mana hannuwa nida matata, na tsananta bincike aka wane irin sihiri kuke amfani dashi inda na gano kai wannan matsitsiyar halitta kai ka yi sanadin faɗawarmu wannan hali.”
Ya nuna Jafar dake taye.

“Alokacin nayi ƙoƙarin ɗaukar fansa a kanku amma wannan sihiri da kuke amfani dashi nakasa koda taba akaifarku, nafara ɗaukar fansa akan abokan tafiyarku dana haɗu dasu su Ukku maza a hanya ta ta zuwa inda kuke tuni na hallakar dasu, yanzu kuma zani kashe ku in ba matata Matsayi kyautar masoya saboda tsananin ƙaunar da nike mata.”

Jin an kashe Garba, Nura da Audu Jafar yaji zuciyarshi ta fara tafasa, wani irin ƙarfi yaji yazo mashi yayo kan waɗan nan halittu ba tsoro ko fargaba a tare dashi, ya nunasu da yatsa tare da fara magana.

“Ƙarya kuke yaku waɗan nan la’anannu kuma ta6a66u, ubangijinmu bai koya mana sihiri ba Sai dai addu’a wadda insha Allah ko a yanzu da ita zamuga bayanku, kun kashe mana ƴan uwa amma nasan lokacinsune yayi, domin bawa baya mutuwa sai Kwananshi sun ƙare, ku baku isa kuyi mamu komiba sai in Allah ya rubuta hakan zai faru damu.”

“Hhhh! Yauni hatsabibi marz mijin marhaz naga halitta mai ƙarfin hali da taurin rai, tunda nike a dajin nan na kaikazo bantaba arba da halittu barasa tsoroba kamarku, yanzu zaniyi fata_fata da naman jikinku in shayar da matata jinanenku.”
Ya ida maganar tare dayo kan Jafar da mummunan nufi a zuciyarshi.

” _LA’ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNIKUNTUMINAZZALIMIN._ “
Jafar ya furta a bayyane.

6acewa Jafar yayi a idanun aljani Marz, dube_dube yahauyi amma bai ganshi ba.

Gefe dasu Jafar ya hango wani irin icce mai tsinin gaske, ɗaukarshi yayi ya daka ma Aljanin a zuciya tare da kwala kabbara bakinshi ɗauke da sunan Allah.

Kuwwa aljanin ya ƙwala dayayi sanadin jawo hankali matarshi itama tayo kanshi da azababben gudu, kafin ta iso har yafaɗi ƙasa jini na malala ta hancinshi da baki.

Kafin ta iso wurin mijinta sul6i ya kwasheta ta faɗa cikin wannan ruwa da Mandiya ta faɗa.

Ihu take tana naiman taimakon mijinta, amma ina tana samu tafito daga cikin ruwan ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus shima mijin ƙonewa yayi iska ta kwashe tokarsu tayi sama.

Ganin wannan al amari daya faru su Nas da Tk mamaki suka riƙayi na yadda Jafar yake da ƙarfin hali.

Jimamin rashin abokan tafiyarsu suka yi tare dayimasu fatan rahamar Ubangiji.

Sunyi kwana biyu a wurin saida jikin Mandiya da Su Salma suka gama warkewa.

Sun yanke shawarar zasuyi tafiya batareda tsayawaba ko da cin abinci Sallah ce kaɗai zata tsaidasu.

Sunyi kwana yakai biyu suna tafiya ba ƙaƙƙautawa batare da sun samu abinda zasuciba koda ƴa’ƴan itatuwane.

Kallo ɗaya zakayi masu kagane sun fita hayyacinsu, ga bakunansu sun bushe jikinsu duk yayi yaushi.

A kwana na ukku ne suna tsaka da tafiya ƙarfinsu ya kusa ƙarewa kamar daga sama bazato ba tsammani suka gansu bakin hanya, wasu mutane suka hango sunyo kansu amma ina kafin su ida ƙarasowa wurinsu tuni su duka sun yanke jiki sun sume.

Ogan sojojin ne ya ƙarema Salma kallo dan gano ko i ta ce wadda suke naima, ganin tafita hayyacinta tamkar ba itaba.

“Yess.”
Ogan ya furta ganin i ta ce wadda suke naima , umarni yayi akira motar asibiti domin abasu taimakon gaggawa….

<< Bakar Tafiya 15Bakar Tafiya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×