Gudu suke iyakar ƙarfin su, domin ceton rayuwarsu.
Basu ankara ba suka gansu gaban wani kogo, basu tsaya 6ata lokaci ba suka kutsa kai cikin kogon.
Cirko_cirko sukayi suna mai da numfashi saboda gudun da suka sha.
Sai lokacin suka lura da inda suke,
“Mun shiga ukku minike gani nan?, ina muka kawo kanmu.”
Salma ta faɗa tana nuna masu ƙwarangwal ɗin mutane birjik wurin.
Kogon ko ina ka kai dubanka ƙwarangwal ɗin mutane ne birjik ga yana duk ta mamaye wurin.
Ido suka fara rarrabawa suna ƙara bin wurin da kallo.
“Kada tsintar kammu a wurin nan ya tada mana hankali, mutsaya mu naimi mafita mu dage da addu’a,kada mu kuskura mu rabu da junan mu.”
Biba ta faɗa tana binsu Rabson da kallo.
“Eh haka ya kamata mu riƙa tafiya tare da junanmu, kada muyi kuskuren rabuwa da ƴan uwanmu.”
Salma ta faɗa muryar ta na kyarma tana ƙara shigewa jikin Biba.
“Muje mu naimi abinci nidai jina nike cikina kamar an hura wuta.”
Rabson ya miƙe tare da yin gaba.
Bayanshi suka bi tare da nausawa ciki kogon.
Tunda suka fara tafiya Basu gamu da komi ba sai ƙasusuwan mutane da yanar da ta tare hanyar sai sun ɗebe ta da hannunsu suke samun hanyar wucewa.
Tirjiya suka ja ganin
Mutum tsaye.
Salma cikin in ina ta furta da..da..daddyy…
*****
Sunyi gudu har sun galabaita.
Tsayawa sukayi ganin sun baro wurin duhuwar, sun bullo wani wuri mai yawan kwazazzabai ruwa na wucewa a hankali ta ƙasansu.
Yanayin wurin gwanin ban sha’awa.
Nan suka tsaya suka gabatar da sallolin da ake binsu.
Cikin ruwan da ke wucewa suka shiga suka ci gaba da tafiya, suna jan ƙafafu a hankali.
Jafar ne gaba sai su Basma a bayanshi.
Mandiya ji tayi kamar an tsunkule ta a ƙafa, a zabure ta yi tsalle ta ruƙunƙume Basma tana.
“Nashi ga ukku na lalace miye ya cijeni a ƙafa?, wayyo uwar daba da magajiya Allah ya tsinemaku albarka, duk ku kuka jefani ciki halinda nike ciki.”
“Ke ki sakini ya kike ƙoƙarin kayar dani, dake zaniji ko da yunwar dake ɗawainiya dani.”
Basma ta yakice Mandiya ajikinta.
“Ya isa! Ku fahimci halinda muke ciki, ku daina yawan hayaniya kuna ɗaga muryoyinku hakan zai iya janyo mana wata matsalar.”
Jafar ya fada
Cigaba da tafiya sukayi.
Tim! Sukaji ƙarar faɗuwar Mandiya cikin ruwan.
Janta ake ba ƙaƙƙautawa ana gwarata da dowatsun wurin.
Ganin wanda ke janta ya sanya su haɗiye wani yawun tashin hankali.
Nura shila suka gani kamanninshi sun sauya jikinshi yayi fari sol ya koma suffar horror yana jan ƙafar Mandiya.
Ihu take tana kiran sunayensu, su taimaka mata.
Nura nasarar ida janyo Mandiya yayi, ya dasa mata haƙoranshi a ƙafa.
Wata irin kururuwa tayi jin azababben cizon da Nura yayi mata a ƙafa.
Ganin halinda Mandiya ke ciki ya sanya Jafar da Basma fidda tsoron da ke cikin ransu, Basma ta kamo hannuwanta tana janyota tana kuka.
wani dutsi Jafar ya ɗauka ya bugama Nura a tsakiyar baya.
Wata ƙara ya ƙwala da tayi sanadiyyar sanya wurin amsa kuwwa, tsuntsayen dake wurin suka yi sama.
Hannun Mandiya Basma ta kama suka yi cikin dajin da azababben gudu.
Nura ganin su Basma sun Tsere mashi ya ya sanyashi bin bayansu shima………
____________________
“Daddy kai nike gani ko idanu nane ke yi mani gizo?.”
“Nine Salma, Mahaifiyarki ta sanar dani abinda ya faru shiyasa na biyo bayanki nazo in fitar dake daga jejin nan, Zo muje kinji Mamana.”
“Aa Salma kada ki yarda dashi, ba Mahaifinki bane, yaudara ce kawai.”
Biba ta faɗa tare da kamo hannun Salma tana ƙoƙarin hanata ida isa wurin Babanta.
“Dallah malama rabu dani, dan kinga ba mahaifinki bane yazo tafiya dake shiyasa kike ƙoƙarin hanani isa gareshi, ninasan dama zai zo da bataliyar sojoji ya fitar dani daga wannan jejin .”
Fizge hannunta tayi tare da rugawa ta rungume daddyn ta.
Wata Mahaukaciyar dariya taji an barke da ita, wadda ta haddasama Kogon girgiza.
Tuni su Rabson da Audu gwarama suka haɗe wuri ɗaya suna sallallami.
Biba baiwar Allah idanunta ta rufe taci gaba da kwararo duk addu’ar da tazo bakinta.
Salma jin Daddyn ta da ta rungume ne ke wannan dariyar ya sanya ta ɗagowa a matuƙar tsorace.
Ja tayi da baya ganin ya chanza suffa ya koma wannan tsohuwar da ta mara lokacin da zata shiga mota.
Cikin kakkausar murya tsohuwar ta fara magana.
“Ina kuma zakije ɗiyata?, ko har kin manta marin da kikayi mani?, bai kamata kiji tsoro tun yanzu ba.”
Zubewa Salma tayi bisa guiyoyinta ta fara ba tsohuwar haƙuri.
Ƙara tun tsurewa da dariya tayi.”Dole ki ɗauki hukuncin abinda kika aikata kigane wulaƙanci ba abu bane mai kyau.”
Hannu ɗaya tasa ta suri Salma ta buga da ƙasa kanta ya bugu da wani icce take goshinta ya haye yayi suntum, jini yaci gaba da zuwa.
Hayaƙi Aljanar ta koma ta shiga jikin Kwarangwal ɗin dake wurin take suka fara motsi suna miƙewa.
Salma miƙewa tayi da ƙyar ga zafin da goshinta ke mata ga lebenta daya haye yayi suntum ga hannunta da ta faɗa samanshi yana mata azababben raɗaɗi.
Ganin kwarangwal ɗin sunyo kansu, yasa suka fara ja da baya tsabar firgici kasa gudu sukayi.
Rabson cikin daga murya yace.
“Kuna gani ana naiman hallaka mu amma kunyi tsaye sororo, toni nayi gaba saikun taho.”
Zabgawa yayi da gudu ko waiwayowa bayayi.
Suna gani yayi gaba suka take mashi baya.
Kwarangwal ɗin suka bi bayansu a guje.
Gudu suke suna waiwayen kwarangwal ɗin.
Sunyi nasarar fita daga cikin kogon sukaci gaba da gudu.
Turjiya suka yi ganin wani wawakeken tsauni da suka tsinci kansu samanshi,ƙasan tsaunin ruwane ke gudu.
Basu da wata mafita face su dira cikin ruwan nan.
Juyawa sukayi gani sukayi kwarangwal suna ƙara kusanto inda suke baki buɗe suna wata irin kuwwa mai razanar da ruhin bil adam.
Rabson cikin kyarmar murya yace dasu Audu.
“Nidai da in tsaya waɗan nan halinttun su kasheni a banza ƙara in faɗa ruwan nan.”
Ƙafar wandonshi irin na gayun nan wanda ake kira Inna tayani cirewa ya duƙa ya nannaɗe ya nufi ramin yana nayi gaba sai kun iso.
Tsalle yayi ya dira ƙasan ramin, suma sauran take mashi baya sukayi suka tsunduma ƙasan ramin.
Lokacin da kwarangwal ɗin suka iso, har sun ɗira ƙasan.
Lokacin da suka dira cikin ruwan wani rin ruwane mai matuƙar yawa ga zurfi, iyo suka ci gaba dayi amma babu alamun zasu kawo ƙarshen ruwan, gilmawar wani baƙin abu suka gani ya wuce ta gabansu.
Tsananta yin iyon sukayi domin iskar da suka yi guzurinta ta kusa ƙaremasu.
Abun mamaki kowanensu cikin kwarewa yake iyo tamkar dama chan sun saba.
Rigar Audu akaja tareda yin ƙasan ruwan dashi, cikin kwarewa Rabson yayi saurin ruƙoshi yayo sama dashi.
Da kyar suka iso bakin gabar ruwan kowanensu yana jan dogon numfashi.
Basu bar wurin ba nan suka gabatar da sallolin da ake binsu, zama sukayi suna hutawa, domin a halin da suke ciki baza su iyacigaba da tafiya ba.
Jikin Audu ne ya ida zama green da baƙi, ga wasu iri jijiyoyi baƙaƙe da su ka bayyana a fuskarshi.
Kamar an ɗauje shi anyi jifa dashi haka aka wullar dashi gefe ko numfashi babu a tare dashi.
Cikin firgici su Biba sukayi kanshi suka tsaya chirki_chirko.
A hankali kamanninshi suka fara sauyawa yana komawa Horror.
Ganin haka ya sanya su Biba ja da baya cikin tsananin tsoro.
Tamkar an harba kibiya daga cikin kwari haka Audu yayi wata alkafura ya dira gabansu Rabson…….
Allah yakara daukaka