Sanyin da sukaji yana ratsa fatar jikinsu ya sanyasu fara bude idanunsu.
Jamcy da Tk dake tsaye kansu da wani icce ahannuwan su, suna jiran farkar warsu, a tunaninsu suma Horror ne lambo sukayi masu.
A firgice suka miƙe, Mandiya ganin mutane biyu saman kanta ya sanyata kwala ihu cikin tsananin kaɗuwa, kafin ta rufe baki Jamcy dake tsaye kanta atunaninta horror ce bata 6ata lokaci ta kwadama Mandiya sandar nan, a take Mandiya ta baje ƙasa a sume.
Sallallami su Jafar suka hauyi tare da yo kan Mandiya.
“Mutane ko Aljanu?, mikuke naima awajenmu da har kuka sumar da abokiyar tafiyarmu.”
Tk da idanunsu suka raina fata cikin ƙarfin hali ya fara jawabi.
Nan ya kwashe komi ya fada masu har batan abokan tafiyarsu wato Kulu da Nas.
Sun yi matuƙar mamakin ƙarfin hali irin nasu Jamcy, kawai saboda ganin ƙwam irin nasu zasu baro gida.
Mandiya da ta samu ta farfaɗo buya tayi bayan Basma tana mai da numfashi.
Bata yarda dasu Jamcy ba sai da Jafar yayi da gaske sannan ta yadda su ɗin mutane ne.
(Niko nace Mandiya anji sambaɗebaɗe)
Wurin da suke wurine mai wuyar misaltawa, domin tunda suka fara tafiya basu taba tsintar kawunan su a irin wannan wurin ba.
Tsabar duhuwar dake wurin tamkar dare ya fara haka yanayin wurin yake.
Kallon_kallo suka shiga yi, tamkar yau suka fara ganin juna.
Da dai sukaga basu da wata mafita face su ci gaba da tafiya, miƙewa sukayi tare da kakka6e jikinsu suna makyarkyata saboda tsananin sanyin da ake zabgawa wurin.
Mandiya kai ko ɗan kwali babu ga kitson attach ansha ga kayan jikinta sun matseta, Basma riga da siket ne jikinta wanda suka sha ɗinki yayi rigar nan daga sama ta matse ƙasa kuma ta buɗe, ga siket ɗin irin wanda ƴan mata ke yayi wanda ake kira mai guiwa.
Uwa uba Jamcy da ta takesu wurin wayewa zamuce ko gantalewa, jikinta T.shirt ce ta ɗan kawo guiwa sai wandon ta jins wato crazy wanda matasanmu ke yayi.
(Wasu mutanen ganewace basuyiba wani fa inya kalleka bada halayenka zai duba ya gano kai waye ba, shigar jikinka ita zai fara kallo yayi maka hisabi, dan haka musan irin shigar da zamu riƙayi, in bakajin tsoron Allah to akwai lalatattun mutane in babu su akwai Shaiɗanun Aljanu.)
Tafiya suke suna bankar juna saboda sanyin da suke ji bakunan su har farin hayaƙi ke fita.
Tun suna tafiya iyakar ƙarfinsu har ƙarfin ya ƙare suka koma jan ƙafa.
Tsayawa suka yi da tafiyar tare da bajewa ƙasa suna huttai.
Ga yunwa ga ƙishirwa da basu iya tantance yaushe rabon da su kai wani abu bakinsu.
Fashewa da kuka Basma tayi tana faɗar;
“Wayyo mijina! Wayyo gidan aurena, shikenan a haka zani ƙare nayi bankwana da asuwaki da cinyoyin kaji gani nan abinda zanisa cikina yana gagarata,da gida nike da ina chan ina asuwaki da naman kaji abinci sai wanda naga damarci, amma yanzu ganinan na ƙare a daji,Ta gaban goshi Allah ya isa tsakanina dake da kika turani na bijiirema maganar Habib nafito damin halartar bikinki, Wayyo Ɗana wayyo mijina.”
Haka taita sambatu tana kuka kamar ta 6a66a.
Kece wa da dariya Jamcy tayi tareda kallon Basma.
“To la’anan na mai kama da ƴa’ƴan yahudawa wakikema dariya?.”
Ci gaba da dariyar Jamcy tayi ta nuna Basma da yatsa.
“Wa fa nike ma dariya in ba ke ba, tsabar gantali da aurenki amma kika baro mijinki kika taho bikin wata ƙawa.”
Ashariya Basma ta tattaro ta ɗurama Jamcy tare da miƙewa tayo kanta gadan_gadan.
Da ƙyar Jafar yayi nasarar raba wannan faɗan daya yaso barkewa.
Ƙutawa kawai Basma keyi tana hararar Jamcy, ita kau Jamcy da sun haɗa ido saitayima Basma kwalo tana mata dariya.
Iya ƙuluwa ta ƙulu da Jamcy, jira kawai take Jafar ya ɗan kauce tasamu sa’ar tumurmusa Jamcy.
Jafar daya lura Tk ɗan zafin kai ne tunda suka haɗu sai wani shan ƙamshi yake yana hura hanci.
“Tk ka taso muɗan zagaya cikin jejin nan musamu abinda zamu sama cikunnan mu.”
Kallon up and down Tk yayima Jafar.
“Ok muje.”
Yafaɗa yana yamutsa fuska kamar yaga kashi.
“Ku su Basma ku tsaya nan kujiramu mu dawo.”
Tsalle Mandiya tayi ta dire ita bazata tsaya nan ba wani abu yazo ya hallakata.
Suma sauran mara mata baya akan bazasu zauna ba.
Sunyi tafiya mai ɗan tsayi suka iso wani wuri mai yalwar ganyayen bishiyoyi.
“Laaah! Kuduba ku gani chocolate da sweet a chan.”
Dubansu suka kai wurin suna masu mamaki ganin kayan daɗin da ko a cikin gari sai kanada manyan kuɗi zaka mallakesu.
Hannun Jamcy Tk ya kamo saboda yasan mayyar kayan zaƙice.
“Sweety ka sakeni in ɗauko, kasan fa yadda nike bala’in son chocolate.”
“Aa ƙaunata kada ki ɗauka zai iyafa cutar mani dake, kinsan da wani abu ya sameki ƙara ni ya sameni.”
Shamatarshi tayi ta fizge ta ruga tana dariya ta nufi wurin chocolate ɗin.
Kafin hannunta ya ida isaga chocolate ɗin tuni sun rikiɗe sun koma wani jibgegen baƙin kumurci ya fasa kai yayo kanta.
“Nashiga ukku nalalace, Sweety ka kawo mani ɗauki wayyo na bani ni Jamilatu.”
Cikin firgici da hargagi yake faɗar” kada ki motsa ƙaunata gani nan zuwa gareki.”
Cikin zafin nama ya jawo Jamcy suka ɗiba ana kare,su Jafar take masu baya sukayi, ganin haka macijin ya bi bayansu.
Abinda suka lura macijin yabar binsu sai yanayin wurin daya chanza duhun wurin ya ƙaru.
Ƙarar tsuntsaye sukaji saman kawunansu.
Ɗaga kan da zasuyi suka ga Wasu irin jibga_jibgan tsuntsaye masu suffar jemage sai dai su sunfi jemage girma da suffa mai ban tsoro.
Ganin haka suka ƙara ƙaimi wurin gudun, tsuntsayen na biye dasu.
Ƙarar da sukaji an kwala ce ta sanyasu tsagaitawa da gudun suka juyo, Basma suka gani tsuntsayen sun sureta sunyi sama da ita………..
____________________
……..Gudu suke gadar na ƙara karairayewa, sunyi nasarar ida ƙara sawa ƙarshen gadar, suna ida tsallaketa tana Rubzawa ƙasa.
Duƙawa sukayi wurin wasu kuma suka baje suna maida numfashi.
Mtsw Salma taja dogon tsoki.
“Aikin banza mutum gashi nan mugun rago da anshiga bala’i sai ya hau ihu yana cika ma mutane kunnuwa yen_yen_yen, mtsw sauna kawai.”
Fashewa Rabson ya ƙarayi da dariya.
“Bakomi masoyiyata mai bakin shantu, kin ga yadda bakinki ke ƙara tsayi da kina kwaikwayar maganata kuwa.”
A fusace ta nufo inda yake tana zazzaga masifa.
Ganin da gaske take ya sanya Rabso fara magana.
“Masoyiya kina ƙarasowa wurin nan zani chakumeki muyi ƙasan ramin nan muyi mutuwar shahada irinta masoya.”
Ya ƙarashe maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya.
Tsayawa tayi daga nesa tana aiko mashi da baƙaƙen maganganu.
“Heeey! Yau ni naga marasa hankali, yanzu ku a halinda muke ciki har kunada bakunan yimana faɗa, to duk ɗan….Ta ɗura wata ashariya Daya ƙara mana fada saina hankaɗashi ya faɗa cikin ramin nan.”
Kulu ta fada tana nuna Salma da yatsa.
“To ɗiyar matsiyata waya sako dake?, gantalalliya uwar ƴan yawon ganin ƙwaf.”
Salma ta ƙarashe maganar kamar zata kai ma Kulu bugu.
“Wa’iyazubillah! Ku kam ko gasar ƙunduma ashariya muka fito sai haka, abinda ya kamata mu dage da addu’a amma kun dage sai zagi da ashar kuke ɗurawa, kuyima kanku faɗa kufa ƴa’Ƴan musulmai ne.”
Shiru suka yi kowa na hararar ɗan uwanshi.
“Haba babynah, ki rabu da ita Ke ba sa’ar yinta bace.”
Nas ya karashe maganar da sigar rarrashi.
Nausawa suka kuma yi ciki dajin suna rarraba idanu.
A hankali wata iska ta fara kaɗawa tamkar irin in hadari ya fara tasowa.
Jin wannan baƙon lamari ya sanya suka ƙara matsewa wuri ɗaya.
Duhu wurin ya farayi tamkar ruwan sama zai balle.
Gudu suka farayi suna sassarfa,kafin su ankara an kece da wani irin mamakon ruwan sama mai haɗe da iska mai ƙarfin gaske.
Gudu suke idanunsu rufe basu ganin gabansu saboda Iskar da ake, wani wawakeken kogon dutse suka gani basu yi wata shawara ba suka afka cikinshi, suna ida shigewa ƙofar kogon Wani dutse ya tugo ya rufeta garam!……