Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Bakin Fenti by Matar yaya

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Chabdi! Yanzu Hajiya A’isha da hankalinki da wayon ki da komai za ki bari a yiwa ɗanki wannan kwamacalar?

Inaahh!!..Wallahi da nice ba zata taba saɓuwa ba..haka kawai..dan suna ƴan uwa duk ina sauran yaran gidan?..naki kawai aka gani..koda yake..kece kikaso dan wallahi ina tabbatar miki za’a gogawa zuri’ar ki BAƘIN FENTI..wanda bazai taɓa goguwa ba..gwara tun wuri ki canza shawara..tamm!!

“Yanzu me kike son nayi Hajiya Ruƙayya kina ganin yanda Abbansu yaƙi ba ma kowa damar magana akan wannan lamari, kuma kada ki manta Sajeederh ɗiyar ƙanwarsa ce… kusan duka rayuwar ta acikin gidan nan tayishi tare da ƴaƴanmu..Ni kaina ina danganta wannan lamari a matsayin ƙaddara dan bai wuce yafaru akan kowa ba.. sannan Sajeederh yarinya ce ƙarama ba komai ya kawo wannan ba sai rashin sanin ciwon kai da kuma sakacin mahaifiya”

Hmm! Numfashi H.Ruƙayya ta sauke sannan tace”yanzu dai kina nufin kinji kin gani kuma kin yarda da wannan haɗin kenan..ta ƙara da tambayar tana mai zuba mata ido.

“Ehh! Kusan hakan abinda kawai nake fata Allah ya basu zaman lafiya..da Ameen Hjy Ruƙayya ta amsa mata tana mai canza firar tasu zuwa wata…

“Haba Amina kinsan fa ƙarfe huɗu daidai ne lokacin fara walimar amma gashi har biyar saura bamuje ba…kinsan cewa kubra bazata ji daɗi ba Allah”…to bagashi nan ina shiryawar ba..ɗayar da aka kira da Amina ta fada tana mai ƙoƙarin ɗaura ɗan kwali akanta..a daidai lokacin ne kuma wata kyakkyawar budurwa wadda zasuyi sa’anni da waɗan nan ƴan matan tashigo ɗakin..sanye take da wani ɗayen leshi royar blue mai watsin pink acikin shi wanda ya ƙara haska farar fatar ta..kallo ɗaya zaka yi mata ka hango tsantsan yarinta acikin ta..sai dai kuma irin yarannan ne da ake kira da kajin turawa saboda girman jikinsu daya girme shekaru..ba wata ƙatuwa bace sai dai tanada albarkatun jiki waɗanda ɗan tsawon da take da ya taimaka wajen ɓoye su Yarinya ce wadda shekarunta basu wuce 19-20 ba…

“Kingani ko Amina har Sajeederh ta shirya amma kinanan kina shiririta..Ni wallahi na kusa duk tafiya ta tashi tsakaninmu dake kowa yayi tashi”

Haba Hajiya miemie, ai da zaki iya da tuni kinyi basai yanzu da tsufa ya kama ki ba…
Dundu miemie ta sakar mata a baya tare da faɗar”wallahi sai dai idan kece tsufa ya kama amma nikam da jini na ajika…ta ƙarashe faɗa cikin jin haushi..dariya suka saka gaba ɗayansu su ukun..

Kallon Sajeederh tayi dake ƙoƙarin zama agefen gado haɗi da faɗar to matar yaya daina ƙoƙarin kai zaune..lokacin tafiya yake yi ba ragewa ba…ɓata fuska Sajeederh tayi tare da faɗar miemie ki daina banaso please..

Tarar numfashin ta Amina tayi tare da faɗar”ke Malama,ji yadda kinka wani haɗiye rai kamar wadda aka hada da wani mugun abu..ai yaya Umar ne ya dace ya faɗi hakan bake ba..zaki wani zo kina wani ɓata fuska..hala kina tunanin wani zai zo a halin da ake ciki yace yana sonki bayan wannan abin kunyar da kika tafka koshi dole aka mishi da babu abinda zaiyi dake ta ƙarashe tana mai jan dogon tsaki…

“Innalillahi! Amina ke da kanki kike gayawa Sajeederh wannan baƙar maganar…kada ki manta cewa Sajeederh ƴar uwarmuce fa..nazata ko wani kikaji yana ƙoƙarin cin zarafin ta sai inda ƙarfinki ya ƙare…amma keda kanki to wallahi kamar kinyi gaban Amma”

“Ehh!nafaɗa ɗin ƙarya nayi mtssw!”

Yayi miki kyau wallahi saina faɗa..kin daɗe baki bafaɗa ba…

Ƙarasawa Miemie tayi kusa da Sajeederh wadda ko kadan fuskar ta bata nuna alamun taji zafin ko ɗaya daga cikin kalaman Aminar ba..saboda ta cancanci fiye da hakan..ƙoƙarin zama agefen ta miemie takeyi tayi saurin tarar ta tare da faɗar”karki damu miemie, ba komai bane fah..lokaci na tafiya muna makara tafaɗa haɗi da duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun ta tare da fara tafiya..

Bayan ta miemie tabi da kallon tausayi tare da nazarin ramar da sajeedar tayi a ɗan tsakankanin nan..wanda duk yasan ta kallo ɗaya zaiyi mata yaga ramar da tayi sai afkin idanun da sukayi saura.

Ga wanda bai santa ba kuma bai san halin da take ciki ba zaiyi tunanin cewa tana cikin kwanciyar hankali saboda babu ta inda fuskarta tanuna..sannan duk wasu al’adun ta na rayuwa babu wanda tafasa sai ɗaiɗai ku waɗanda aka hanata daga cikin gidan.. sannan Sajeederh yarinya ce mai sanyin hali kuma bata da hayaniya amma tanada rawar kai da sakewa agurin waɗanda ta saba dasu..ga waɗanda basu santa ba kuma suna dubin hakan a matsayin girman kai….

“Ke dalla muje kin tsaya kina tunanin da bazai fidda keba… girgiza kai miemie tayi tare da bin bayan Amina..

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×