A zabure Munawwa da Daddy suka yi kanta, shi kanshi Basarake da ke waje sai da ya shigo. Saboda tsawar da ya ji Daddy ya yi, yana shigowa ya yi arba da Munara da ke ta kuka jikin Daddy, duk da kirjin shi da ke ta bugawa amman bai hana shi k’arasawa wurin ba. Saboda ko kad’an bai ji tausayin ta ba, domin har lokacin yana jin zafin zagin da tayiwa Ummin shi, kuma ya k’ara tabbatar da cewa sam ba ta san girman na gaba da ita ba.
Ya k’ara jin tsanarta da halayyarta gaba d’aya , saboda ba ya fatar ya auri matar da ba ta san girman manya ba haka kawai ya kai wa kanshi bala’i ya ajiye cikin gidan shi a cikin ran shi yace,
‘ALLAH ya so ni da yanz…’
Tunanin shi ya katse ne saboda maganar da ya ji Daddyn ya fara,
“Ki yi hak’uri kin ji Baby, da kaina zan je na nemo miki HAIDAR d’inki, amman sai kin kwantar da hankalinki kin samu sauk’i jikinki ya warware, don ba na son ganin kina d’aga hankalinki a kan hakan, ki d’auka cewa tamkar ma kin aure shi kin gama. Domin da raina ba zan tab’a barinki kiyi kuka a kan wani abu ba, matuk’ar ina da ikon nemo maki shi to tabbas zan nemo shi ko a’ina yake a fad’in duniyar nan, saboda haka ki kisha kuruminki kawai ki daina d’aga hankalinki kinji?.”
Munara ta d’aga kai amman har lokacin hawayen idanuwanta ba su daina zubar da hawaye ba, a hankali ta furta cewa,
“To yanzu ya zan yi na yi missing d’in contact’s d’insa gaba d’aya? Wallahi ina son na ji muryar shi Daddy ko hankalina zai kwanta, a kan kokwanton da zuciyata take yi mini, domin ina son na ji shin da gaske rabuwarmu yake nufi ko wasa yake yi mini?.”
Basarake da ke tsaye yana kallonta ya yi saurin cewa,
“Da gaske mana.”
Kallon da ya ga Munara, Daddy da Munawwa suna yi masa ne ya sa ya gano zancen zucin shi da ya fito fili, domin a tsammanin shi a cikin zuciya ya yi maganar. Amma yana gano sun ji maganar, ya yi saurin shiga taitayin shi da nutsuwar shi ya mazge kamar ba shi ne ya yi maganar ba. Daddy cikin kakkausar murya har tana rawa yayin fitowar lafuzzansa ya ce,
“Kana nufin da gaske HAIDAR din yake yi? To ya aka yi ka shiga zuciyar shi ka gano?”
Basarake ya yi saurin waskewa ta hanyar cewa,
“Ni ma mamakin da nake yi kenan Maigida, saboda ganin irin asarar da yake so ya yi wa kan shi na rashin macec kirki irinta, a gaskiya ba k’aramar wauta yake shirin aikatawa b…”
“Shout up!!!!!!!!!!!!!”
Munara ta katse shi da sauri cikin d’aga muryarta, wacce ta koma irin masu ciyo, cikin Kuka ta k’ara da cewa,
“Ya fita d’akin nan Daddy. Wallahi na tsane shi ba na son ganin bak’ar fuskar shi a cikin idona”
Ta k’are maganar tare da kwantawa jikin Daddy tana gunjin kuka, a zabure Daddy ya ce da shi ya fice tun da ta ce ba ta son ganin fuskar shi. Basarake ya rusuna kamar gaske ya ce,
“Ba damuwa Maigida yanzu zan tafi, Ranki ya dad’e Ki yi hak’uri, ALLAH ya ba ki lafiya.” Munara ta yi saurin rintse idanuwanta, saboda yadda take jin muryar shi ta ratsa ta har cikin zuciyarta. A dalilin kamanceceniyar da ta ji muryar shi ta yi da ta honey’nta, tun kafin ta ce wani abu ya yi fitt ya fice daga d’akin. Munawwa ta bi shi da kallon tausayin tozarcin da Munara ta yi masa har ya fice d’akin.
Sannan ta dawo da kallonta suka yi ido biyu da Daddy, babu shiri ta shiga nutsuwarta. Ya watsa mata wata k’atuwar harara sannan ya ce,
“Ke ma bi shi kuje yanzun nan, kada na sake ganin k’afarki a nan, abinci ma na yafe kada a kawo mana, ni zan kula da ‘yata har zuwa lokacin da za ta ji sauk’i a salleme ta, ki je can da bak’in halinki da kika gada ga Uwarki da kuke ganin kun fi kowa sanin abin da ya dace.”
Munawwa ta fara tafiya sum-sum za ta bar d’akin Munara ta d’aga kai ta kalli Daddy ta ce,
“Ai ita da an bar ta ta zauna Daddy.”
Daddy yana huci ya ce,
“Ba za ta zauna ba, ta k’ara saka ki a damuwa kike so? Ko ba ki san ita ce ta goge komai na HAIDAR a cikin wayarki ba?”
Da sauri Munara ta tashi zaune cikin kufula ta ce,
“ALLAH ya isah tsakannina da ke Munawwara, wallahi ban yafe miki ba, ni daman na san ba sona kike yi ba shi ya sa kika zab’i ki raba ni da rayuwata. To WALLAHI ki sani da na rabu da HAIDAR nafi son mutuwa ta zo ta raba ni da kowa ma na duniya.”
Ta k’are maganar tare da fashewa da wani sabon kuka, wanda ya k’ara d’aga wa Daddy hankali, duk da ya ji zafin jin maganganun da ta yi amman yadda yake son ganin farin cikinta shi ya sa bai bi kan maganar ba ya koma lallashinta, Munawwa dai salun alun ta fito d’akin amman zuciyarta cike take fam da jin takaicin sangarcin da Daddyn yake yi wa Munara, wanda take ganin kamar shi ne so wanda a bad’ini sam ba son ba ne.
Koda ta fito ta tarar da Basarake rungume da hannu duka biyu ya soke kan shi a k’asa yana tunanin abin da ya faru, tana zuwa wurin shi ta ja birki kanta a k’asa ta ce da shi,
“Don ALLAH ka yi hak’uri ka ji?”
Ya yi saurin d’ago kan shi tare da sauke kallon shi ga fuskarta, sannan ya fad’ad’a murmushin shi ya ce,
“Da me fa?”
Ta yi saurin kallon k’wayar idanuwan shi fuskarta d’auke da alamun mamakin tambayar da ya yi mata, ido cikin ido ta ce da shi,
“Kana nufin har ka manta abin da aka yi maka a yanzu?”
Ya yi murmushin yak’e sannan ya ce “Ok ai in dai wannan ne babu komai, a wurina komai ya wuce.”
Munawwa ta sauke idanuwanta ranta a jagule ta ce,
“Ni dai ka yi hak’uri plss don na san ba a kyauta maka ba.”
Tana k’are maganar ta fara tafiya sannan ta k’ara da cewa,
“Zo mu je mu tari napep mu koma gida.”
Basarake ya bi ta da kallo har ta yi masa nisa sannan ya biyo bayanta yana wani shu’umin murmushi. Saboda shi duk abin da Munara da Daddy suka yi masa ko a jikin shi, don shi burin shi d’aya ne ya shawo kan Munawwa. Wanda za a ganin shi da ya samu kanta shi kenan komai zai zo masa da sauk’i.
Tana bakin titi a tsaye ya tarar da ita, zuwan shi ya yi daidai da tsayar da wani mai napep da ta yi. Babu b’ata lokaci ta fad’a ta zauna tare da fadin sunan Unguwar da zai kai su. Shi ma Basaraken ya zagayo d’ayan gefen ya zauna, sannan ya kai kallon shi ga fuskarta yana murmushi. Ta yi kamar bata lura da shi ba, gefe ta kawar da fuskarta tana kallon k’aton gate d’in asibitin, ya sake yin murmushi cikin salon jan ta da hira ya ce,
“Wai fushin na mene ne? Bayan na ce da ke komai ya wuce?.”
Munawwa tak’i juyo fuskarta sanadiyyar hawayen da suke ta zubo mata, wad’anda ita kanta ba ta san dalilin zuwansu ba. Amma a zahiri yadda Daddy yake tafiyar da rayuwar gidansu abin bai mata dad’i, sannan maganganun da Munara ta yi sun daki zuciyarta sosai. ‘Wato dai wannan HAIDAR da gaske ya yi nasara sosai a kanta, wanda rashin shi gare ta zai iya haifar mata da gagarumar illah a rayuwarta. Shin daman shi so haka yake? Ko kuwa ita nata son ne ya sha bambam da na kowa?
Tambayoyin da ta yi wa kanta kenan, amma ta rasa sanin wa zai ba ta wannan amsar da take so ta gano gaskiyar.
Basarake sarai ya lura da kukan da take yi, sh iya sa jikin shi ya yi sanyi k’alau, cikin sanyin jiki ya d’auko wani farin hankicif da ke aljihun shi ya mik’a mata. Sai da ta kalle shi ido cikin ido sannan ta yi saurin janye nata idanuwan saboda abin da ta ji ya ratsa idanuwanta, kuma ya sa zuciyarta bugawa da sauri da sauri.
Ta kai kallonta ga farin hankicif d’in, jiki ba kuzari ta zura hannu ta karb’a ta nufi fuskarta da shi da nufin share hawayen, kamar yadda yake buk’ata, babu shiri ta lumshe idanuwanta saboda wani bala’in k’amshin turaren da ta ji ya daki hancinta. Wanda ya shagaltar da ita ta manta da share hawayen ta buge da shak’ar daddad’an k’amshin da ke cikin hankicif d’in.
Idonsa a kanta, shi ma yanayin da ta shiga tashi zuciyar sai bugawa take yi da sauri da sauri fat!! fat!!! Saboda yadda yake jin sonta yana ratsa jini da jijiya tare da b’argon jikin shi. Hak’ik’a son Munawwa kalar shi daban yake a cikin zuciyar shi, wanda ya sha bambam da wanda ya yi wa Munara a can baya. shauk’in son da ya kwashe shi bai san lokacin da ya zura hannun shi ta bayanta ba ya rungumota jikin shi, ita ko k’amshin da ta k’ara ji ya daki hancinta shi yasa ta k’ara narkewa a jikinshi, ALLAH ya taimaka wurin da suke ba yawan mutane akan titin saboda zagayen bypass d’in da Napep yayi dasu, saboda k’ok’arinshi na kaucewa go slow d’in da ake yi, wanda gurinshi kawai yayi saurin juye su ya ya kama gabanshi, saboda shi hankalinshi kwatakwata baya kansu, bin wak’arshi kawai yakeyi da sautinta ya karad’e Napep d’in gaba d’aya.
Basarake ya k’ara matse ta jikin shi tare da sauke k’atuwar ajiyar zuciya, numfashin shi da ta ji yana sauka a kan fuskarta, hakan ya sa ta dawo natsuwarta babu shiri ta bud’e idanuwanta, zumbur ta yi ta mik’e tare da kai kallonta a kan shi,l zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, cike da jin kunyar abin da ta gani ta ce,
“Ya aka yi hakan ta faru? Ni fa ba na son irin haka”
Ya bud’e idanun shi da suka canza launi a take ya ce,
“Daga taimako? Fad’uwa fa na ga za ki yi garin shinshinar hankacif na taro ki, sh ine kuma na yi laifi?”
Da sauri ta kawar da fuskarta tana ‘yar dariya ta ce,
“Ga kayanka ma na gode!”
Yayi saurin kallonta yana murmushi mai sauti sannan ya ce,
“Ki bar shi kawai a hannunki tun da kina so”
Ta kalle shi sannan ta kawar da kai gefe ta ce,
“Thanks.”
Kafin ya yi magana idanuwanta ya kai kan motar shi da yake ta ajiyewa a bakin titi gindin wata bishiyar dalbejiya, a daidai inda wani shago dake rab’e da k’ofar wani gida. Cikin sauri ta ce,
“Wow!”
Da sauri ya kalle ta tare da yi mata tambaya da hannu ya ce,
“Lafiya?”
Tana rawar baki ta ce, “Wata mota na gani ta yi mini kyau sosai, sai dai na ga kamar masu ita ba su san darajarta ba, saboda a kullum nazo wucewa ta nan sai na hango ta wurin ajiye.”
Basarake ya basar tare da fad’in, “Watak’ila kuma lalacewa ta yi.”
Munawwa ta ce, “Cab wannan had’ad’d’iyar mota ko a kallo za ta yi tsada, ni dai sosai ta yi mun kyau! “
Basarake ya yi shiru ba tare da ya ce da ita k’anzil ba, sai dai ya k’udurta wani abu a ransa.
Suna tafe shiru kowa da abin da yake sak’a wa a ranshi har suka je gida. Mai napep yana ajiye su ta bud’a jakarta za ta ciro kud’i da nufin ta biya, Basarake ya yi saurin ciro kudin a aljihu ya mik’a wa mai napep. Ya so ya bar masa har canjin, amman gudun fallasuwar sirrin shi yabsa ya mazge yana ba shi canjin ya karb’a ya soke aljihu. Munawwa ta bi shi da kallo cike da mamaki ta ce,
“Wai me ya sa kake son wahalar da kanka ne?, ni fa ba na son kana takura kanka, gaskiya ka daina idan ba so kake yi mu b’ata ba.”
Yana murmushi ya ce, “Tuba nake ranki ya dad’e.”
Ta harare shi sannan ta mayar da kud’inta a jaka ta fara tafiya za ta shige gate, hannuwan shi ya saka a aljihunsa duka sannan ya d’aga murya ya ce,
“Sak’ona fa! Kin manta ba ki ba ni ba fa!”
Munawwa ta juyo a hankali a cikin rashin gano inda ya dosa ta ce,
“Wane sak’on fa?”
Yana murmushi ya tako a hankali har inda take tsaye sannan ya ce,
“Kina nufin har kin manta?, to shikenan ni na ma hak’ura, amman dai da fatar ke za ki maye mini gurbin da nake so a cike mini.”
Cikin d’aure kai da maganganun shi suka saka ta, idonta a kan shi tace “Ka fito fili ka bayyana mini abinbda kake nufi, domin na gano inda zancenka ya dosa.”
Ya k’ure ta da kallo a hankali sannan ya ce,
“Munawwarah!!!”
Ya ja sunan nata da wani kalar salon magana wanda har sai da taji gabanta ya buga rass! rass!
Ta d’ago idanuwanta tana kallon shi ba tare da ta ce da shi k’anzil ba, bai damu da kallon da take yi masa ba ya fara magana kamar haka yana cewa,
“Tun da na ji ba ki ce komai ba dangane da maganar da muka yi jiya ba, ina da tabbacin ban yi nasara ba musamman da na gani da idanuwana, domin ko ba ki fad’a ba na san zuciyar Munara wani ya riga ni shigarta, saboda haka na hak’ura amman ina rok’on alfarmar taki zuciyar ta zamo mallakina.”
Da sauri ta ja da baya tare da dafe k’irjinta da ya tsananta bugawa da sauri da sauri bakinta yana rawa ta ce,
“Ni?”
Cikin dakewa ya lumshe idanuwan shi da wata muryar da ba ta tab’a jin shi da ita ba ya ce,
“Ke fa Munawy! Ina sonki son da ban tab’a yi wa wata ‘ya mace ba a duniya, ina jin sonki cikin kowane lungu da sak’o na zuciyata, fatar ba za ki watsa mini k’asa a ido ba.”
Munawwa ta bi shi da kallo kamar wata sakarya ta ce,
“Shi son na Munara ya fita kenan?”
Ya yi murmushi sannan ya ce,
“Kusan hakan tun da ita hankalinta ba ya kaina, ni kuma ba na son shiga hak’k’in wani, shi yavsa na zare kaina daga kanta. idan kin amince mini shi kenan ni na zama mai sa’a kuma d’an gatan da ya fi kowa gata a duniyar nan.”
Munawwa ta bud’a baki da nufin ta yi magana sai ga Malam Isah ya lek’o saboda maganganun da yake ji suna tashi k’asa k’asa, shine ya lek’o ya ga su waye, saboda ya ji saukar napep amman bai ga an shigo gidan ba.
Idanuwan shi suka hango masa Munawwa da Basarake da ke bakin….