Munawwa ta bud’a baki da nufin ta yi magana Malam Isah ya lek’o, saboda maganganun da yake ji suna tashi k’asa-k’asa, shi ne ya lek’o domin ya ga su waye. Saboda ya ji saukar adaidaitasahu amman bai ga an shigo ba. Karaf idanuwan shi suka hango masa Munawwa da Basarake da ke bakin gate tsaye, cike da mamaki ya ce,
“Ali har kun dawo?”
Ya ce, “Eh Baba”
“Ya jikin nata” cewar Malam Isan, Basarake ya ce,
“Da sauk’i sosai Baba.”
“To ALLAH ya bi da lafiya”
Ya ce, “Amin Baba”
Ita dai Munawwa ko motsin kirki kasa yi ta yi, saboda zuciyarta ta yi shocking da yawa. Malam Isah ya kai kallon shi gare ta ya ce,
“‘Yata zo ki shiga gida kada tsayuwar ta dame ki”
Zumbur ta mik’e ta shige ko waiwaye babu jikinta yana rawa. Yayin da ta bar Basarake a nan zuciyar shi cunkushe da takaicin rashin jin amsar da za ta ba shi.
Malam isah kuwa da gangan ya yi hakan don ba ya son alak’arsu, gudun wani abu ya je ya faru a ce da hannun shi a ciki, duk da ya yaba da hankalin Alin, amman dai ai an ce ba a yabon d’an kuturu har sai ya girma da yatsunsa.
Basarake ya shigo harabar gidan ya zauna bisa dogon bencin da Malam Isah yake zama, tare da dafe kan shi da hannu biyu saboda tsananin haushin da ya ji na rashin jin amsar da Munawwa za ta ba shi.
Malam Isah ya k’ura masa kallo tsawon minti biyu yana karantar shi, zuciyar shi dai ta tabbatar da zargin shi ya zamo gaskiya. ‘Waton Ali soyayya yake yi da Munawwara.’ A hankali ya kira sunan shi saboda tsananin tausayin da ya ba shi na d’ebo wa kansa rigimar da tafi k’arfin shi. Ya k’ara maimaita kiran sunan shi har sau biyu sannan Basarake ya d’ago fuskar shi tare da yin tagumi da hannun shi duka biyu yana kallon shi ba tare da ya ce da shi k’anzil ba.
Malam Isa ya zauna gefen shi cike da tausayawa ya ce, “Ali shawara zan ba ka, wacce nake muradin ka d’auke ta, kuma ka yi amfani da ita ko don tsira da mutuncinka. A matsayinka na d’ana da nake ji tamkar ni ne na haife ka, saboda tun zuwanka a gidan nan na ji hankalina ya kwanta da kai. Amma duk da haka dole ne na fad’a maka gaskiya don ba na son abin da zai cutar da kai ni ma ya jawo mini fitina ina zaman zamana. Na san kana son yarinyar can, amman da za ka daure ka cire sonta a zuciyarka da ka huta da rigimar da za ka d’ebowa kanka. Saboda ina jin tsoron ka janwo wa kanka gagatumar matsala. Domin Maigidan nan komai zai iya aikatawa a kan yaran shi, ba na son ka jefa kanka cikin matsala, ka tsaya matsayinka inda ALLAH ya ajiye ka. Ka shafa wa kanka lafiya ka rabu da yarinyar nan tun kafin mahaifinta ya gano abin da ke tsakaninku ya kore ka daga aikin da kake rufa wa iyayenka asiri da shi.”
Basarake ya sauke k’atuwar ajiyar zuciya sannan yace, “Na ji shawararka Baba, kuma nagode. Amma abin da kawai nake so a wurinka shi ne; ka ci gaba da taya ni addu’a, idan har ita ce matar ALLAH ya saka alkhairi a cikin auren mu ni da ita, saboda WALLAHI da gaske nake so nta Baba.”
Malam isah ya bi shi da wani kallo tamkar wani tab’ab’b’e sannan ya ce,
“Ana ga yak’i kai kana ga k’ura, ni fa ina yi maka magana ne a kan ka shafa wa kanka lafiya ka rabu da ita ya fi maka alheri. Amman kai ka rud’e sai wani zancen auren ku kake yi, shin kai ba ka ganin wuce gona da irin da kake so ka yi ne?.”
Basarake ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,
“Na sani Baba, amma ina fatar ALLAH ya sa ta zamo matata, ai abin rabo ne aure da marar kwabo. Idan ita rabona ce sai ka ga anyi, duk da ban kai matsayin da zan aure ta ba.”
Yana k’are maganar ya tashi tsaye yana cewa,
“Ni zan wuce gida Baba, saboda yau ban a jin dad’in jikina.”
Malam isah ya bi shi da kallo har ya kai bakin gate sannan ya ce,
“Ba z aka tsaya kaci abincin ba.”
Basarake ya sosa kan shi ya ce,
“Bakina babu dad’i Baba, abincin nan ba zai shiga. Barni na wuce sai gobe idan na dawo.”
Yana k’are maganar ya sa kan shi ya fice gidan Malam Isah ya bi k’ofar da kallo sannan ya ce,
“ALLAH ya kawo afuwa.”
****
Munawwa kuwa tana shiga d’akin ko Mummy ba ta nema ba ta shige d’akinsu babu shiri ta fad’a gado, tare da sauke wata k’atuwar ajiyar zuciya sannan ta dafe kanta da yake ta sarawa. Saboda tsananin tashin hankalin da ta shiga, kalmar ina sonki da Basarake ya fad’a mata ita ce take ta amsa amo a cikin kunnuwanta. Da sauri ta toshe kunnuwan tare da rintse idanuwanta ta ce,
“No.. No.. “
Sai ga hawaye mai zafi shaaa yana kwaranya a kan fuskarta, sai bin gefe da gefen fuskarta yake yi yana sauka shimfiɗar gadon. A zabure ta tashi zaune saboda tuno maganar da ya yi inda yake cewa,
“Ina rok’on alfarmar taki zuciyar ta zamo mallakina.”
Babu shiri ta mik’e tsaye tare da cire kayan jikinta ta fad’a toilet, ruwa ta dinga sakar wa kanta shaa. Yadda ruwan shower’r ke zuba a saman kanta haka take jin soyayyar shi tana kwaranya a cikin jikinta. Maimakon ta ji sauk’in lamarin sai abin ya k’ara k’aimi, babu shiri ta kashe shawar tare da dafe saitin zuciyarta saboda yadda take ta bugawa da sauri da sauti.
Cikin sanyin jiki ta jawo towel ta d’aura sannan ta fito ta zauna kan gadon tare da dafe kanta da hannuta duka biyu, saboda barazanar rabewa da yake ƙoƙarin yi a dalilin tuɗun da ta tsinci kanta.
K’arar shigowar saƙo a wayarta ya sa ta kai dubanta gefen da ta jefar da jakata ar lokacin da ta shigo d’akin. Amma ta kasa tashi ta d’auko sai tagumi ta zuba tare da lulawa cikin nazarin kalamansa ɗaya bayan ɗaya.
Shigowar kira a wayar ne ya sa ta dawo daga zuzzurfan tunanin da take yi, jiki babu kuzari ta jawo k’afafunta ta d’auko jakar tareda fiddo wayar. Ganin mai kiran nata ya sa kirjinta ya k’ara bugawa dam! Dam! har wayar ta tsinke ba tareda ta yi k’ok’arin d’agawa ba, wani kiran ya sake shigowa tana kallo har ya k’ara katsewa shima ba ta ɗauka ba. Sai a na uku ta d’auka ba tare da tace komai ba, muryar da ya yi amfani da ita wurin fad’in sunanta ya sa tayi saurin rintse idanuwanta babu shiri.
Saboda dad’in muryarsa da taji har cikin mak’wallaton zuciyarta, wutar son shi sai ci take yi balbal a cikin zuciyarta, ruwan k’aunarshi kuwa suka ci gaba da kwaranya a duk wata k’ofar gashi da ke jikinta.
Shirun da yaji tayi ne ya sa ya k’ara kiran sunanta, wanda ta ji ya rad’a mata sabon sunan da ba ta san da shi ba, waton Munawy sannan ya ce,
“Kiyi hak’uri da ni kin ji, ni ma ba yin kaina ba ne laifin zuciyata ce, da sonki ya yi mata yawa ta kasa hak’uri har sai da ta sa na fallasa sirrin da ke cikinta. Ina sonki ina sonki Munawy, soyayyarki a cikin jinin jikina take, don ALLAH ke ma ki ce kina sona kin ji, ko da hankalina zai kwanta.”
A cikin daburcewa ta ce,
“Sai nayi shawara.”
Da sauri ya ce,
“Ki ice kina sona kawai don ni na san kina sona, babu wata shawara da za ki yi a kan abin da kika san akwai shi a ranki.”
Cikin sanyin murya ta ce,
“Baka canka dai dai ba, don ni ka gan ni nan ko so ban sani ba har yanzu, saboda ina kokwanto a kansa har gobe.”
Basarake ya lumshe ido kamar yana ganinta ya ce,
“Sai zuwa wane lokaci kike ganin za ki san minene Son? Pls ina son in tambaye ki amman sai kin yi mini alk’awali za ki fad’a mini gaskiya.”
Ta sulale kan gadon ta kwanta tare da bajewa sosai saboda taji dad’in hirar, don gaba ki d’aya jikinta ya mutu murus saboda yadda Voice d’inshi ke ratsa duk wata gaba dake jikinta. A lokaci d’aya wata kasala ta sauko mata ta yi jarumtar furta cewa,
“Idan na sani me zai hana na fad’a maka? kawai ka fad’a matukar ka san ina da masaniya a kan abin da za ka yi tambayar.”
Ya shafa d’an k’aramin gemunsa ya ce,
“Akwai wanda Idan kika gan shi kike jin fad’uwar gaba? Sannan muryarsa idan kika ji shin wane yanayi kike tsintar kanki a ciki? Haka ma idanuwanku idan sun had’u ya kike ji?”
Ba shiri ta sauke ajiyar zuciya mai sauti sannan ta ce,
“Sirri ne tsakanina da zuciyata plss don ALLAH ka yi hak’uri, saboda amsar wad’annan tambayoyi za su yi mini nauyin fad’a a baki, kawai ni dai na san akwai wanda idan na gan shi, ko na ji muryarsa, ko muka had’a idanuwa akwai abin da nike ji, amman ban san ta ya zan kwatanta hakan da bakina ba.”
Ta k’are maganar a cikin wata sanyayyiyar murya tare da karya ta alamun jin tausayin kanta. Wanda hakan da ta yi ya jefa Basarake cikin yanayin da sai da tsikarshi ta tashi yarrrr!
Babu shiri ya rintse idanuwa saboda shi kad’ai ya san abin da yake ji, kasancewar shi lafiyayyen matashin namiji, kuma mai jini a jika. A cikin muryar shi mai d’an karen dad’i wacce ya canza ta zuwa kalar luv ya ce,
“Wane ne shi?”
Munawwa ta dafe kanta saboda yadda masifaar sara mata, bayan fad’uwar gabanta da ya tsananta. Maimakon ta ba shi amsa sai ya ji ta ce,
“Wash!!!!.”
A rude ya ce, “lafiya? Meke faruwa?”
Ta daure tare da saita kanta saboda jin yanayin muryarsa cikin tashin hankali. Da sanyin murya ta ce,
“Babu komai.”
Yayi saurin fad’in,
“Ba komai kuma kika zab’i ki tayar da hankalina? Fad’a mini gaskiya meke damun ki?.”
Ta dafe kanta tare da rintse ido kamar tana ganin shi ta ce,
“Kaina ne yake d’an ciyo.”
A cikin rawar murya ya ce,
“Sannu kin ji? Je ki d’auko magani ki sha yanzu ina jiran ki”
Babu shiri ta bud’e idanuwanta sannan ta ce,
“Katinka fa nake ji.”
ya ce, “Wannan ba damuwa ba ne, je ki sha na ji ina sauraron ki, kuma na ji motsin ballar maganin tare da motsin ruwa a mak’oshinki. Hakan zai tabbatar mini da tabbacin kin sha.”
Munawwa ta tashi zaune sannan ta ce,
“Plss ka kashe wayar, idan na k’are zan kira ka saboda kada a k’arar maka da kud’i a iska.”
Yayi murmushi mai sauti sannan ya b’ata fuska ya ce,
“Je ki sha ina jira.”
Munawwa ta tashi tsaye ta d’auko maganin ta b’alla sannan ta bud’e d’an karamin firij dinsu da ke d’akin, ta janyo ruwa ta jefa maganin a baki sannan ta kurb’a ruwan maganin ya wuce sannan ta sha ruwan sosai ta ajiye saura. Wayar ta ciro daga mak’aletan da ta yi tsakanin wuyanta da kafad’a tana murmushi ta ce,
“Lalle baka jin garin.”
Yana ‘yar dariya ya ce,
“Taya zan ji garin bayan ina tare da ke.”
Ta k’ara kwanciya da wayar mak’ale a kunnenta ta ce,
“Ni a suwa? Rufa mini asiri.”
Shi ma ya yi dariyar sannan ya ce,
“Asirinki a rufe yake ruf matar HAIDAR.”
Babu shiri Munawaa ta mik’e zaune tare da dafe k’irjinta, saboda sunan da ta ji ya kira ya tuno mata da fuskar HAIDAR d’in munara. Da rawar murya a rud’e ta ce,
“Wane HAIDAR kuma? Ka manta saurayin Munara ne ba ni ba? Kuma sannan ni babu wata alak’a tsakanina da shi. Kai a tak’aice ma ni ko ganin shi ban tab’a yi ba sai a photo, to ta ya ya za ka ce mini Matarsa?”
Basarake ya yi wani k’ayataccen murmushi mai sauti, saboda jin yadda ta rud’e a lokaci d’aya, a take zuciyar shi ta tabbatar masa da akwai aiki ja a gaban shi. Domin kuwa ya tabbatar ba k’aramin rikici za su yi da Munawwa ba duk ranar da ta gano shine HAIDAR d’in Munara. Don shi ba ya jin ta Munara, saboda bolar da ke k’ofar gidansu ma ta fi ta daraja a wurinsa. Sanadin zagin da ya ji ta yi wa mahaifiyar shi, haka ya sa muguwar tsanarta a ranshi. Cikin dakewa ta kasaitattun maza ya ce,
“Mene ne abin tayar da hankalinki har haka? Koo ba ya cikin jerin mazajen da kike ganin za ki iya aura?”
Munawwa ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
“Ban tab’a kallon pic d’in wani a lokaci d’aya ya kwanta mini a rai ba sai shi, yana da Kira sosai wadda duk wata d’iya mace za ta yi alfakhari idan aka ce shi ne mijinta. kyakkyawa ne ajin farko a cikin mazaje, rud’ewar da ka ji na yi kuwa, saboda ina jin tsoron a ce ka gano sirrin da ke zuciyata ne, amman bayan haka babu wani abu.”
Basarake ya lumshe idanuwa saboda tsananin dad’in da ya ji yana ratsa shi a hankali ya ce,
“Yanzu misali a ce ya dawo kanki, ya ce ke yake so, kuma ke ce zai aura, shin ya za ki ji.”
Munawwa ta yi saurin dafe zuciyarta da ta buga dam! dam! Sannan ta ce,
“Daina wannan zance ai abin ma ba zai tab’a yiyuwa ba ko a misalin.”
Ya yi saurin cewa,
“Saboda me to kike ganin ba zai yiyu ba? Ko ke ba mace ba ce? Wai kin ko san yadda ALLAH ya k’awata halittarki? Ai babu wani d’a namijin da zai gan ki ya ce bai k’yasa ba, komai isar sa kuwa. Saboda ALLAH ya azurtaki da kyawawan halaye wad’anda suka k’ara haskaka hasken zallar kyaun da ALLAH ya yi miki ki gode wa ALLAH saboda ba kowa yake yi wa wannann baiwar ba kyau da kyakkyawan hali ba a lokaci ɗaya. Wanda shi ‘yar uwarki ta tawaya da shi, am sorry for u duk namijin da ya san abin da yake yi; to gaskiya ba zai aure ta ba.”
Munawwa kam, duk da tsananin dad’in da ta ji saboda yabonta da ya yi; amma nan take ranta ya b’aci. Saboda jin zafin sukar da ya yi wa ‘yar uwarta, a take b’acin rai ya ziyarci fuskarta da muryarta cikin jin haushin maganarsa ta ce,
“Ai gari da yawa maye ba ya cin kansa, don wani ya k’i ta, ai wani da gudu zai so ta. Mazan ma har wuya ne da su? Ga su nan kamar jamfa a Jos!”
Ta k’are maganar tare da murgud’a baki kamar a gabansa. Babu shiri ya fashe da dariya, irin wacce sai ya yi watanni ba tare da ya yi irinta ba. Saboda ya fi yin murmushi mai…
Nice