Munawwa kuwa, a gajiye tib’is ta fad’a gidan, Mummy ma gaida ta kawai ta yi ta shige d’akinsu, tare da jefar da jaka ta fad’a toilet ta d’auki tsawon minti goma kafin ta fito. Ta fito towel d’aure a jikinta saboda wankan da ta yi. Sallah ta fara yi sannan ta fito falo, saboda yunwar da ke ta k’wak’walar cikinta.
Mummy ta baje mata abincin tana shirin kiran ta sai ga ta ta fito, jikinta yana rawa ta fara zuba abincin Mummy tana kallonta tana yi mata dariya. Sai bayan ta fara cin abincin ta ce,
“Kai yau na ji yunwa sosai WALLAHI, saboda tests d’in da na yi mana, saukinta ma ba a lokaci d’aya aka yi su ba. Amma duk da haka naci kwakwata sosai Mummy, saboda kwana biyun nan da ba mu je ba an yi abubuwa da yawa bama nan. ALLAH ya taimaka Nusy tana zuwa, shi yasa ma test d’in munara ta yi mini sauk’i, amman fa wallahi wani k’unataccen lecturer d’insu ya so ya gano ni ba Munara ba ce. Saboda kallo na ya yi ta yi yana jefo man tambayoyi, dole na yi ta acting irin nata, duk k’wak’war shi dole ya kyale ni.”
Mummy ta yi dariya ta ce,
“Ki ce yau ‘yata da kyar ta sha, ai na so na ga idonki a lokacin.”
Munawwa sai da ta guma loma a bakinta sannan ta ce,
“Ai kuwa baki gani ba, ido ya raina fata, kamar an kama sarki ya yi k’arya. Sai bayan an k’are na yi ta dariyar kaina.”
A tare suka yi dariya, tsidik Munara ta shigo Daddy biye da ita a baya, yanayin da suka ga Munawwa da Mummy ya sake tunzura su. Musamman Daddy da ya ga ciwon Munara ko a jikinsu, yana can yana fama da baby a asibiti, su kuma suna nan suna jin dad’i abinsu. Cike da takaicinsu ya haye sama ba tare da ya kalli gefen da suke ba.
Mummy jikinta yana rawa ta bi bayan shi zuciyarta cike da fargabar abin da zai biyo baya.
Munara kam har sai da ta k’are wa Munawwa kallo sama da k’asa sannan ta watsar tare da buga mata wani k’aton tsaki ta shige d’akinsu. Munawwa jiki a sanyaye ta ajiye plate d’in abincin ta bi ta da kallo, ALLAH ya taimake ta ta ci abincin k’ari ne ta yi. Cikin sanyin jiki ta kwashe kayan abincin ta kai kitchen ta ajiye, sannan ta nufi d’akinsu,
wanda ko da ta je ba ta tarar da ita ba, sai k’arar ruwan da ta ji a toilet, wanda alamu yaa nuna wanka take yi.
Ta zauna kan gadonsu tana tattara littafansu da suka zube, sai ga Munara ta fito fuskarta murtuk’e ba alamun sassauci ko kaɗan. Munawwa ta kalleta ta ce,
“Ya jikin?”
Munara ta watsa mata wani kallo mai cike da harara sannan ta ce,
“Ina ruwanki da ni balle lafiyata? Wallahi ki kiyaye ni don yanzu a shirye nake da duk wani munafuccinki. kuma tsaf zan gyara miki saiti a cikin gidan nan, tunda na gano ba k’aunata ake ba, wai ace Uwar da ta haife ka ma ba ta sonka to sai kuma wa ya yi saura wanda ya dace ya so ka a duniya?”
Munawwa ta bi ta da kallo cike mamakin kalamanta, a cikin dakiya ta ce,
“Kin tab’a ganin Uwar da ta haifi d’a ta ce ba ta son shi?”
Munara ta d’aga mata hannu tana cewa,
“Dakata malama! Ba wani kilbibi da za ki yi mini ya yi tasiri a yanzu, domin da idanuwana na gani ba fad’a mini aka yi ba. Ke d’in da take so ta je ta jik’a ki ta sha, ni kuma a saka ni a turmi a dake har sai na mutu sannan a fiddo ni.”
Ta k’are maganar tare da murgud’a mata baki, saboda jin take yi kamar da Mummyn ce take magana. Munawwa ta yi shiru ba tare da ta sake cewa da ita komai ba. Don ta fahimci a wuya take, kuma k’iris take jira a yi uwar watsiya da ita, shi yasa ta yi mata gum, sannan ta ci gaba da gyaran littafanta. Amma a zuciyarta sai fatan shiriya take yi mata, saboda ganin yau abin bai tsaya iya kanta ba har kan Mummy bai tsallake ba.
Sai dai a bayyane ta ce,
“Ai ba mune muka kar zomon ba, balle a sauke fushin a kanmu.”
Munara da ke kallon kanta a madubi tana ganin yadda ta rame cikin kwana biyu, maganganun Munawwa ya sa ta juyo babu shiri ta ce,
“Ai ke ce babbar wacce ta kare zomon, domin ke ce kika k’ara haddasa man duk wani bala’in da nike ciki a yanzu, saboda bak’ar muguntarki da mugun nufinki a kaina ni da HAIDAR. Ko kin ɗauka ban san ke ce babbar mai adawa da soyayyarmu ba? Shi yasa kika yi amfani da damarki kika rusa man farin cikina, to idan ma bak’in ciki kike yi saboda na samu d’aya tamkar da dubu a cikin mazaje; to ki sani har ki mutu ba za ki tab’a kamo k’afata ba, balle har ki samu irin honeyna.”
Munawwa ta fashe da dariyar tura haushi sannan ta ce,
“Honey’n mai rabo dai, amma ke kam ya riga da ya fita hannunki sai dai hak’uri.”
Munara kamar wata zakanya ta shak’o wuyan rigar munawwa ta baya jikinta yana rawa ta ce,
“WALLAHI ki kiyayi sake fad’in wannan irin maganar a bakinki, idan ba haka ba zan watsar maki da hak’ora. Domin a kan hakan zan rufe ido na karta maki rashin mutuncin da sai kin yi danasanin sani na WALLAHI. Don haka take care of your self! if not you will regret.”
Ta k’are maganar tana huci tamkar wata kububuwa, Munawwa ta fincike rik’on da ta yi wa wuyan rigarta tare da gyara zaman rigar jikinta ta ce,
“Ba laifinki ba ne wallahi, saboda ni na san ba ki cikin hayyacinki, ki nemi tsari da sharrin shi tun kafin ya kai ki a tarkon danasanin da ba za ki iya fitar da kanki a cikinsa ba.”
Munara bakinta yana rawa saboda masifa ta ce,
“Wa kike nufi?”
Munawwa ta ce,
“Shaid’an, saboda shi ne yake ingiza ki kike duk abubuwan da kike aikatawa, idan ba ki tashi kika yak’e shi da rundunar shi ba; za su yi nasara a kanki a banza. Don haka ko yanzu akwai dama, sai ki yi gaggawar koma wa ALLAH tun kafin lokaci ya kur’e maki, don yana gaf da sanya ki tashi a tutar babu, saboda a kullum ba ya gajiya wurin farautar mabiyan shi.”
Maganganun munawwa sun so su yi tasiri a zuciyarta, sai dai a take shaid’an ya canza mata tunani, ta sheke da wata arniyar dariya sannan ta yi d’if kamar ba ita ce ta yi ba, ri’ke k’ugunta ta yi sannan ta ce,
“Sannu alarammiya mai kashin aya da aman hadissai. Ni na fi k’arfin ki yi man dad’in baki, kunne dai na ja maki ki kiyayi danganta HAIDAR d’ina da wata mace idan ba ni ba. Domin har duniya ta tashi ba zan daina son shi ba, kuma nawa ne ni kadai, kuma don ni iyayen shi suka haifa mini shi. Kuma duk wacce ta yi saken shiga gonata sai na mayar da ita mujiyar da ko ‘yan uwanta sai sun yi gudunta, balle wani ya zo kusa da ita. Saboda haka ki sani ki k’ara sani HAIDAR nawa neeeeee niii ka daiiiii, Haidaaaarr nawaaaaaa neeeeeee niiiiii Munaraaaaa, babuuuuu wata macennnnn da ta isaaaaa ta rab’e jikin shiiiiiiii a matsayin matarrrrrrr shi alhali ina numfashiiiiiiii a doron k’asaaaaaaa.”
Ta k’are maganar a cikin karaji kamar wata mai aljannu, sannan ta fad’i kan gado tana k’yalk’yala dariya.
Munawwa saboda tsananin tsoron da ta ji kirjinta sai bugawa yake yi faattt! fat!! Tsananin tashin hankali. Babu shiri ta ji wani kuka ya zo mata, saboda ganin yadda yar uwarta ta zauce a kan namijin da bai ma san tana yi ba. A ranta sai nanata hasbunallahu wani’imal wakil kawai take yi, saboda ganin take yi kamar HAIDAR d’in ba mutum ba ne. Idan kuma mutum ne ya cika cikakken mayaudari, tun da har ya yi nasarar cusa mata son shi sannan daga baya ya guje ta.
Jiki a sanyaye ta fito falo ta baro mata d’akin, inda a nan d’in ma zamanta ke da wuya ta jiyo sautin Daddy yana ta zuba ruwan masifa. Wanda ko tantama babu a kan cewa da Mummy yake yi, saboda yadda take jiyo sautinta tana ba shi hak’uri cikin ‘yar murya. Haka kawai ta ji gidan ya gundure ta.
A lokacin marece sakaliya, magriba ta gabato, a haka ta fito compound d’in gidan kai tsaye ta nufi wurin malam Isah. Zuciyarta cike da begen ganin Basarake ta ce da shi,
“Baba barka da yamma.”
Ya d’ago daga gyaran tsohon radion.shi da yake yi, fuska babu walwala ya ce,
“Yawwa barka dai ‘yata.”
Ta fara jajjefa idonta inda za ta yi nasarar hango shi ta ce,
“Yana ina Baba? KO ya tafi gida?”
Malam Isa ya wayance tare da fad’in
“Shi wa fa?”
Munawwa ta ji nauyin fad’in sunan sosai ammaa haka ta dake ta ce,
“Aliyu nake nufi Baba, ko ya wuce?”
Ran Baba Isah a jagule ya ce da ita,
“Eh ya tafi tun lokacin da Maigida ya dawo, saboda ‘yar uwarki da ta nuna ba ta son ganin shi maigida ya ce ya je ya sallame shi daga aikin. Har ma ya biya shi kud’in aikin da ya yi, kin gan su nan ya bar mini saboda ransa ya b’aci sosai. Babu yadda ban yi da shi ba a kan ya tafi da kud’in shi amma ya k’i. Ga makullin motarku ma ya ba ni ns ajiye muku, saboda ya ce gobe tun da sassafe zai kama hanyar zuwa k’auyensu.”
Babu shiri Munawwa ta fad’i tare da k’walla k’ara tana birgima, saboda tsananin tashin hankalin da ta shiga. Daddy, mummy da Munarar suka fito da gudu saboda sunnji k’arar da Munawwa ta yi. Kafin su isa wurinta Baba isah ya riga su zuwa kanta yana ba ta hak’uri, Mummy da Munara suka fara tambayar me aka yi mata.
Baba Isah ya tashi tsaye jikin shi yana rawa ya ce,
“Don kawai ta tambayi ina Ali yake, na yi mata bayani maigida ya sallame shi daga aiki. Shi kenan na ga ta fad’i tana birgima.”
Daddy kam tun da ya gano ba Munara ba ce, tashin hankalinbshi ya rag cikin kashi d’ari saba’in ya tsere. Saboda ganin ta fito suna rigengen zuwa wurin domin su ga meke faruwa. Ya koma tafiya maimakon gudun da yake yi, tun daga nesa ya jiyo sautin muryar Baba Isah yana bayanin abin da ya faru. Ba tareda jin ba’asin komai ba ya wanka wa Baba Isah mari har sai da ya wuntsila hular kan shi ta fad’i kasa. Saboda haushin da ya ji a kan matsiyacin mutumin da babyn shi ba ta son ganin fuskarbshi ake wannan tarzoma.
Munara ma tana jin haka ta makawa Munawwa da ke ta kuka harara, sannan ta sake ta tare da buga tsaki d’auke da yi mata harara ta bar wurin. Mummy kam tana Jim ba’asin maganar ta gano akwai matsala, saboda ta daɗe da gano munawwa ta yi zurfi sosai da soyayyar shi. Daddy ma ya bi bayan Munara yana banbamin fad’an haka kawai ta tayar wa mutane hankali a kan wani bakin talaka.
Mummy dai babta bi ta kan zantukan shi ba ta ri’ko munawwa da ke ta uban kuka. Tayar da ita tsaye ta fara yi, sannan ta kalli Baba Isah, wanda tun marin Daddy ya yi masa ya dafe fuskarsa bai cire hannun shi ba. Saboda tsananin mamakin da ya kama shi, a ce shi ne yau aka mara da girman shi har da furfura, saboda kawai ya zo neman abin rufawa kai asiri. Domin ba zai iya tuno ranar k’arshe da aka mare shi ba tun yana d’an karami har zuwa yanzu da manyanta ta kama shi.
Cike da jin nauyin abin da Daddy ya yi masa Mummy ta fara babshi hak’uri kamar tabyi kuka. Sannan ta ja hannun munawwa suka shige cikin gida, m kai tsaye d’akinta ta nufa da ita, saboda zuciyarta da ta cunkushe da bak’in cikin halayen Daddy. Domin wannan abin da ya aikata, shi ake kira mari da tsinke jaka, ba ta gama wartsakewa da gumaguma bak’ak’en maganganun da ya jefe ta da su ba a kan Munara; sai ga kuwwar ‘yarta wadda ta fi soyuwa a cikin zuciyarta.
K’arin takaicin kuma marin da ya yi wa Baba Isah wanda ko a ido aka kalle shi za a gano ya girmi Daddy sosai. Don ko yayan shi Alhaji Musa da wuya idan Malam Isah bai girme shi ba, amman bai ji kunyar cira hannu ya zabga masa mari ba a kan dalilin da bai kai ya kawo ba.
A cikin kwantar da murya ta dinga bai wa Munawwa baki, amma iMunawwa ta ƙara rikice wa Mummy sosai tana fad’in,
“Don ALLAH mummy ki bar ni na je na ba shi hak’uri, saboda gobe tun da safe ya ce zai je garinsu, ga shi Daddy ya kore shi. Watak’ila ma idan ya je ba zai dawo ba, don ALLAH Mummy ki bai wa Daddy hak’uri ya dawo da shi gidan nan, kuma ya hana shi tafiya k’auyen ma duka kada ya je ko’ina don ALLAH mummy.”
Mummy kam tashin hankalinta ya k’aru, don yanzu ta k’ara tabbatar da son da take yi masa ba na wasa ba ne, ganin Mummy ta yi shiru ko motsi ta kasa yi ya sa ta fita da gudu ta nufi sama d’akin Daddy. Kamar an jefo ta ya ganta tsidik cikin falon shi, nan take ya had’e fuska fahimtar ita ce ba Munara ba. Tana zuwa ta durk’usa k’asa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi ta ce,
“Don ALLAH Daddy ka yi hak’uri ka dawo da shi don ALLAH, wallahi yana da kirki sosai Mummy ma ta sani Daddy.”
Tsawar da ya daka mata ce tasa ta kai bakin k’ofa babu shiriz hannunta biyu had’e wuri d’aya hawaye yana kwaranya akan fuskarta ta ce,
“Don ALLAH Daddy, don ALLAH Daddy.”
Ya taso kamar zai dake ta da sauri ta sauko k’asa ya rufo k’ofar falon shi garam! Tare da buga uban tsaki ya ce,
“Useless girl, haka kawai zan dawo da shi alhali fuskar shi tana tsorata baby?ya je cann ya k’arara da shegiyar bak’ar fuskar shi.”
Aiko tana saukowa ta fita aguje ta d’auki key d’in motarsu da ke ajiye saman teburin malam Isah ta bud’e gate da kanta ta je da sauri ta fad’a mota. Ta jawo ta da k’arfi ta fice gidan sai jin k’arar tashin motarta aka yi, Mummy ta k’ara sautin Kukanta, saboda ta kasa jure abin da yake damun zuciyarta, don tun fitar Munawwa zuwa wurin Daddy ta fara kuka saboda tsananin tausayin rayuwarsu dukansu, tun daga kan Daddyn har Munara da ita kanta Mummyn tare da Munawwarar, wanda ta fi alak’anta shi…