Bangare Basarake kuwa, yana tafe iska yana kwasar shi, saboda yadda jikin shi ya yi sanyi k’alau. Amma kan matsananciyar soyayyar Munawwa da ta saka shi kasala. Musamman idan ya tuno da kalamanta inda take cewa,
‘Aliyu i love u morethan anything in dis world, i don’t have any word to describe how i feel when i see u, I love you so much my only.’
Yana tafe muryarta tana yi masa amsa amo a cikin kunnwa, har ya je inda ya ajiye motarsa. Da sauri ya tayar da ita ya bar wurin bayan ya yi wa d’an Liti mai shago ihsani. D’an Liti ya bi shi da kallo zuciyarsa cike da tunanin yau meke damun mutumin nasa, saboda a d’an fahimtar da ya yi masa ya gano mutum ne shi mai matuk’ar kirki, duk da bai cika yawan surutu ba. Amma tun da marece lokacin da ya zo d’aukar motarsa ya fahimci akwai abin da yake damun shi, a cikin ransa ya ce,
‘ALLAH ya kawo maka mafita a cikin lamurranka, kuma ya yaye maka abin da yake damun ka, burinka na alkhairi kuma Ubangiji ya cika maka shi koma mene ne, tun da ka ce da ni alkhairi ne.’
Saboda bai b’oye masa komai ba, tun ranar da ya fara ba shi ajiyar motarsa ya yi masa bayanin akwai aikin da yake zuwa yi, wanda yake fatar ALLAH ya sa ya yi nasara a kan lamarin. D’an liti ya nuna masa in har ya san abin ba na rashin gaskiya tun wuri ya fitar da shi a ciki, Basarake ya tabbatar masa da ba komai sai alkhairi. shi ya sa ya saki jiki da shi har suka fara sabo da juna, don wani zubin ma idan ya fito gidan sai ya tsaya shagonsa sun d’an tab’a hira. Wani lokaci ya yi wa matasan da ke zama wurin alkhairi. Idan ya fito gidan sai ya yi SALLAH wurinsu, kafin ya wuce masaukinsa, hakan ya sa D’anliti zuciyarsa ta natsu da shi sosai.
*****
Munawwa ko, kai tsaye Mummy ta wuce da ita d’akinta. Saboda ba ta son su had’e ɗakinsu su k’ulla fad’a cikin dare babu wanda ya sani. Sai da ta tabbatar ta daina kukan sannan ta fito ta nufi d’akinsu, inda Munara take a kwance ta yi shiru tana nazarin abin da za ta yiwa Munawwa ta huce da marin da Mummy ta yi mata a kanta. Shigowar Mummy ya sa ta yi saurin tashi zaune don ta zaci Munawwa ce, saboda ta ci alwashin sai ta rama marin da Mummy ta yi mata a kanta. Tana ganin Mummy ce ta k’ara had’e fuska tana gunguni, Mummy ba ta damu da yanayinta ba ta zauna a kan bed side d’in gadonsu, idonta a kanta, saboda ganin ta fara zunbure zunburen baki tana muimui, a hankali ta kira sunanta ta ce,
“Munara me ya sa a kullum ba kya son ganin farin cikina ne? Me na yi maki Munara? Ki fad’a mini me ‘yar uwarki ta tare miki da a kullum masifarki a kanta take k’arewa? Idan har wani abu take yi maki ki sanar da ni ba zan ji nauyin rok’arki ki yafe mata ba. Saboda ni dai na gaji da wannan tashin hankali, ‘yan biyu ne ku, wad’anda kuka fito ciki d’aya, kuka sha nono d’aya, kuka tashi gida d’aya. To me ya sa ba za ku had’a kanku ku k’aunaci junanku ba? Amman a ce kullum kuna cikin rikici da juna, wanda tun yana tsakaninku har yanzu ya dawo tsakanina da mahaifinku. Don ALLAH munara ki natsu ki gyara halayyarki ku zauna lafiya ke da ‘yar uwarki kin ji?”
Munara ta tashi tsaye tana ta kunbura hanci ta nufi hanyar toilet, sannan ta tsaya ta ce da ita,
“Bayan duk ke ce kike haddasa komai, sannan yanzu ki dawo kina d’ora man laifi, tun da kin manta bambancin da kike nunawa a tsakaninmu? Kin sha nuna kin fi sonta da ni, to ai ku je babu komai tun da ni ma Daddyna yana sona.”
Ta shige toilet tare da rufo k’ofar, Mummy ta yunk’ura jiki babu kuzari ta je k’ofar toilet d’in ta tsaya. Cikin muryar Kuka ta ce,
“Da ke da ita duk ‘ya’yana ne, wad’anda nike so fiye da komai nawa a duniya, yadda kike ganin ina sonta haka ke ma nike sonki Munara. Bambancinku d’aya a wurina ita tana jin maganata, duk abin da na hane ta ba ta sake yin shi, kuma duk abin da na ce ta yi shi take yi ke ma shaida ce. Sab’anin ke da a kullum ba kya shayin sab’a mani a kan koma mene ne na hana ki, shin ta ya ya ni da na haife ki ba ki yi man biyayya ba; sannan a ce ni zan faranta maki? To ki yi wa kanki karatun ta nutsu Munara, ki sani akwai rayuwa akwai Mutuwa, kuma idan za ta zo ba k’wank’wasa kofa take yi ba, balle ki yi sauri ki kimtsa kafin ta shigo ta d’auke ki. Ki gyara halayyarki ki zauna da ‘yar uwarki lafiya ku kaunaci junanku, saboda ba tabbas d’in za mu yi ta kasancewa tare da ku har k’arshen rayuwa, balle mu yi ta zaman yi muku shari’a koyaushe. Abin da ba ki sani ba; a kullum fatan mu ku k’ara had’a kanku musamman ku da kuke mata, don shi yayanku namiji ne ba ruwansa da wannan. Tun da ko yanzu kina gani tun da ya yi aure ya tafi da matarsa har yanzu ko ganin gida bai zo mana ba. Shin idan ku kun ware wurin wa za mu je mu ji sanyi?.”
Mummy tana k’are maganar cikin tuk’owar wani sabon Kukan da yazo mata, da sauri ta fice d’akin ta yi kitchen saboda ba ta son Munawwa ta gani ta k’ara d’aga hankalinta.
Munara kam daga toilet d’in duk abin da Mummy ta fad’a tana jin ta, amman sai mere take yi tana wani abu da baki alamar abin da ma Mummyn ke fad’i; ba ta cikin kunnuwanta maganganun suke shiga ba.
Har sai da ta ji shiru sannan ta d’an bud’e k’ofar ta lek’o tana ganin ba ta wurin ta fito sadaf-sadaf ta saka wa k’ofar d’akin key. Sannan ta fad’a kan gadon tana tunanin ta wace hanya za ta rama muguntar da Munawwara ta yi mata, tun da ita ma yanzu ta kamu da son wancan bagidajen, ta san zafin so, shi ya sa ta yanke shawarar idan har ta ga za a aura mata shi; to sai ta zuga Daddy ya raba su. Don ta san muddin aka raba su tabbas za a k’unsa musu bak’in ciki ba kad’an ba. Da haka za ta rama duk munafuccin da Munawwa ta dad’e tana k’ulla mata wurin Mummynsu. Wanda ya yi sanadin da ba ta son ta, kuma wanda ya sa ta fi sonta fiye da ita.
A daren ranar babu wanda yayi bacci mai dad’i kowa da abin da yake sak’a wa a ransa, daga Basaraken har Munawynsa, Daddy, Mummy da Munara har Baba Isah. Don shi ma kansa kwana ya yi yana juyi zuciyarsa cike da tunanin rikicin da ya b’allo a cikin gidan. Tare da tausayin Aliyu saboda rashin aikin sa da yabyi, amman da ya k’ara nazari sai ya ga gara ma hakan da cin zarafin da Munara take yi masa, sannan uwa uba rashin hankalin da Maigidan yake yi duk don ya farantawa shalelensa.
Ko da safiya ta waye Basarake bai bar garin Kaduna ba har sai da sak’on da yake jira ya iso, sannan ya ba da umurnin a kai wa Munawynsa kai tsaye. Tare da uwar siyayyar da ya narko mata, wacce duk yanyi ne da sunan Muhammadu zaharadden waton abokinsa. Sannan ya hau motarsa direba ya ja shi suka bar kuduna cikin kewar masoyiyarsa ya nufi birnin tarayya Abuja.
Da misalin k’arfe d’aya da rabi na rana, Munawwa tana zaune a kan sallaya ta k’are SALLAH tana jera addu’o’i, idanuwanta har lokacin ba su daina zubar da hawaye ba. Saboda hargitsin da zuciyarta take ciki, da damuwa goma da ashirin d’in da suka cika mata rai, duk da dai damuwarta ta ɗan rage saboda ta hango kamar Mummy da Daddy sun shirya. Saboda tun da ta tashi da safe yanayin da ta ga suna tarairayar juna ya tabbatar mata da an samu ci gaba. Amma kuma har lokacin fuskar Mummy cike take taf da damuwa.
Bayan ta k’are addu’o’in ne ta mik’e tare da cire hijabinta tana cikin linkewa ta ji shigowar text a wayarta. Da sauri ta d’auki wayar tana dubawa saboda tsammanin ko Aliyunta ne, don ta yi ta kiran number’shi ba ta samu ba. Shi ya sa ta zaci ko rashin netwk d’in k’auyensu ne ya sa wayar tak’i shiga, don ta matsu sosai ta ji idan ya sauka lafiya.
Sai ga sab’anin tunaninta, domin kuwa saƙo ne na mutuminta Nuradden, yana sanar da ita gift d’in da ya ce zai ba ta d’an aiken zai kawo mata. Cike da jin haushin shi ta buga wani uban tsaki ta ajiye wayar cikin ranta tana cewa,
‘Rashin aikin yi.’
Ta d’an gincira kan gadon Mummy tana k’ara gwada kiran lambar Aliyu, ta kira har ta katse ba tare da ya d’aga ba. Saboda hankalinsa ya d’auku sosai wurin tunani, sai da direbansa ya ankarad da shi, wanda da ke ta sharara gudu a cikin dokar daji. Domin hankalinsa ya kai in da wayar ke ta fidda haske ya ce da shi,
“‘Yar lab’ai, ana ta nemanka a waya fa!”
Sannan hankalinsa ya dawo jjikinsa daga zuzzurfan tunanin da ya lula, jiki a sanyaye ya fiddo wayar da ke aljihunsa sai ga number’r Munawynsa ta fito b’aro b’aro a kan screen d’in wayar. Wacce ya saka wa suna da heartbeats, a take wani farin ciki ya lullbe shi, fuskarsa cike da yalwataccen murmushi ya d’auki wayar, babu zato ya ji muryar Mummy tana cewa,
“Ki je Baba Isah ya ce ana nemanki a waje.”
Munawwa ba ta samu damar cewa da shi komai ba ta datse kiran, saboda bin umurnin Mahaifiyarta dake tsaye a kanta. Ta yunk’ura ta tashi jiki babu kuzari ta saka hijabin da ta yi SALLAH da shi ta fice ɗakin. Mummy ta bi ta da kallo zuciyarta cike da tausayin ‘yarta, saboda yadda ta zama sukuku a lokaci d’aya.
Tun daga nesa ta hango fuskar Baba Isah cike da annushuwa, sai da ta k’araso jikin gate ta ce,
“Barka da rana Baba, na ji an ce ana nemana, wake nema na halan?”
Baba Isah yana murmushi ya ce,
“Je ki gani, wani ne aka aiko da sak’o wirinki.”
A cikin kokwanto a ranta ta ce,
‘Anya ba wannan d’an rainin hankalin ba ne kuwa?’
Ta tsaya bakin k’ofar gate d’in ta lek’a kanta, aikuwa idanuwanta suka hango mata wata dank’areriyar mota light pink mai shegen kyau, sai k’yallin sabunta take yi. Da wani mutum tsaye a k’ofar gidan wanda yana hango ta ya yi saurin k’arasowa inda take ya ce,
“Ranki ya dad’e sak’o ne aka ce na kawo maki, idan har babu damuwa a bud’e gate d’in sai na shigo maki da ita ciki.”
Munawwa cike da mamaki tare da rud’ewa ta gwalalo ido a waje ta ce,
“Wane sak’o ne wannan da har sai an bud’e gate?.”
Mutumin ya yi d’an murmushi saboda yadda ya ga ta rud’e ya ce,
“Wannan motar da kika gani taki ce, ke aka ce na kawo ma wa, in ji Muhammadu Nuradden. Ki sa a bud’e gate na shigar maki da ita sauri nike yi jira na ake yi.”
Kafin tace wani abu Baba Isah ya wangale gate d’in, ya bai wa mutumin umurnin ya shigo da motar ciki. Kamar wata sakarya haka ta rab’e tare da bin mutumin da kallo har ya shigo da motar ya yi parking. Sannan ya ciro k’attin ledodin da ke cikin motar ya ajiye gabanta, ya rusuna har kasa ya mik’a mata key d’in motar cikin ladabi. Ta zura hannu ta karb’a ba tare da ta san ta karb’a ba, saboda hargitsin da kwakwalwarta ta shiga ta kasa gano me ya dace ta yi har mutumin ya wuce baba isah ya rufe gate. Jikinsa yana rawa ya isa wurinta yana murmushi ya ce da ita,
“Kwantar da hankalinki ‘yata, kin isa ne shi ya sa aka ba ki, kuma kin fi k’arfin kowace kyauta a duniya saboda kyawawan halayenki. ALLAH ya sanya alkhairi, kuma ya kare ki da sharrin k’arfe, bari na kai maki kayan daga ciki kafin ki ƙarasa.”
Baba Isah ya jidi ledodin ya shigar mata da su ya ajiye cikin corridon da zai kai mutum k’aton falonsu. Sannan ya dawo, inda ya bar ta anan ya tarad da ita, cike da mamakin ganin yanayinta ya ce,
“Yata ga su can na ajiye maki sai ki k’arasa shigar dasu daga ciki. Munawwa kam sai a lokacin ta dawo daga suman tsaye wuccin gadin da ta yi, idanuwanta suka sake sauka akan tsadaddar motar wadda take ta so ta tuno inda ta tab’a ganin irinta. A take yanke zuciyarta ta tuno mata da motar da tasha gani ajiye bakin gindin wani icen dalbejiya, musamman idan za su je makaranta, ko idan sun dawo. Wacce har ta tab’a yi wa ALIYU korafi a kan ajiyetan da ake yi wurin, babu shiri kirjinta ya buga dam! dam! A ranta ta ce,
‘Na shige su! Shin ko mai motar shi ne Nuradden d’in?’
A rikice ta bar wutin ta nufi k’ofar shiga cikin gidan, idanuwanta suka yi tozali da ledodin da ke ajiye, da sauri ta ci birki hankalinta ya k’ara tashi cikin tsananin rud’ewa ta rab’a gefen ledodin ta fad’a babban falonsu. Jikinta yana rawa ta fara k’walla wa Mummy kira a haukace,
“Mummy! Mummy! Munara ku fito ku ga wani abin al’mara.”
Saboda ta manta shaf da zancen fad’a suke da Munarar. Mummy a d’ari ta fito da ludayin miyar da ta saukar kenan tana zubawa a kula. Munara ma da ke bacci a zabure ta fito d’akinsu domin ta ji kiran har tsakiyar kanta, suna fitowa jikinta yana rawa ta ce da su,
“Ku zo muje waje ku ga abin Mamaki.”
Gabaɗaya suka yi dii suka bi bayanta da sauri. Fitowarsu ke da wuya idanuwansu suka yi tozali da wad’annan manyan ledodin, don Munara har sai da ta yi tuntub’e da su a lokacin da ta fito, saboda gaf suke da shiga falon. Cikin takaici tare da mamaki ta ce
“Wa ya ajiye mana kaya anan? Don kawai a sa mutane su je su karya k’afafuwansu a banza.”
Ta k’are maganar tare da buga wani uban tsaki, Mummy ma ido bud’e ta bi kayan da kallo, kafin ta ja ta tsaya tana k’ok’arin yin magana Munawwa ta jawo hannunta tana cewa,
“Zo mu je ku gani don Allah!”
Mummy baki a buɗe ta bi bayan Munawwa, Munara ta k’ara buga wani uban tsaki ta juya za ta koma cikin gidan, mai ta tuna kuma ta dawo ta bi bayansu tana ɓata fuska. Babu zato idanuwansu suka hango
musu….
🙏🏻🙏🏻