Basarake ya dinga rarrashinta da daddad’an magana har ya samu ta yi shiru, sannan ya samu damar gaisawa da Ummi. A cikin farin cikin ganin juna suka baje a nan falon yana cin abinci suna fira har ya k’are, sannan Kakale ta fara magana tana cewa,
“Wai kai ba ka ga na fara tsufa ba? A ce shekara biyar kana zaune babu mata, ka fa yi wa kanka fad’a ALIYU, don ALLAH ma ai sai ya yi maka hisabi da gangar jikinka. Saboda ALLAH kai fa ba saurayi ba ne amma a ce har yanzu ka kasa auruwa? Haba Gadanga in dai ba so kake k’asa ta shafe idona ba tare da na ga abin da zaka haifa, ba don Allah ka yi aure.”
Ta fashe da kuka wiwi, hankalin Ummi ya tashi ta fara rarrashinta, Aliyu kam shiru kawai ya yi yana kallonta yana ‘yar dariya, don inda sabo ya saba da rigingimun Kakalen, a cikin kukan ta sake cewa,
“Yanzu ina wannan yarinyar da ka had’a mu da ita muka gaisa?”
Basarake yana dariya ya ce,
“Tana nan me za ta yi miki?”
Kakale ta b’ata fuska irin ba wasa d’in nan ta ce, ” To ni zan je da kaina har gidansu na nema maka aure ta tunda kai ka mayar da abin shiririta.”
Basarake yana dariya ya ce,
“To fa! Ashe na yi kwanciyata sai dai na ga an kawo mini mata kawai.”
Kakale ta ce, “Tun da ka kasa ai ni sai na fito da k’arfina don idan ban yi da gaske ba tsofewa za ka yi a haka, d’an nuna mini hotonta ma ni dai na gani, shin muryarta da na ji ta yi daidai da ita ko kuwa dangin su dunb’aru ne?”
Basarake yana dariya ya shiga nemo pic’s d’in Munawwa, sai ya ci karo da wani pic d’in Munara don bai ma san yana cikin wayarsa saboda ya goge su gaba d’aya, a take ransa ya b’ace, ya d’an sunkuyo saitin Kakale ya ce,
“Kin ga duba man wannan ki gani ai za ta yi ko?”
Kakale ta jawo medical glass d’inta ta saka sannan ta karb’i wayar tana d’ora idonta a kan pic d’in Munara ta ce,
“Ya salam! Wannan fitsararriya fa? Ka ga wannan daga ganin idanuwanta a tsaye ka san za ta yi tsiwa, Mu’aza duba mini ita ki gani ko idona ne?”
Ta mik’a wa Ummi wayar tana mere tare da maka masa harara ta ce,
“wannan k’yalk’yali banza ce fa!”
Basarake ya k’ume dariyarsa Ummi kam ba ta aibata ta ba, sai dai har a ranta yarinyar ba ta yi mata ba. Saboda rashin kamun kan da ta nuna a pic d’in, jiki a sanyaye ta mik’a masa wayar, Basarake ya yi murmushi sannan ya jawo pic d’in Munawwa inda tayi rolling d’in gyale a kanta, kamilallar fuskarta ta fito rad’am a ciki ya mik’awa Kakale wayar yana cewa,
“Wannan fa?”
Kakale ta k’ura wa pic d’in Munawwa idanuwa sosai sannan ta d’ago ta kalle shi ta ce,
“Sai na ga kamar fuska d’aya ce da mai wancan hoton ko dai idanuwa na ne?”
Basarake ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,
“Eh fuskarsu d’aya, amma wannan ita ce wacce zan aura in sha ALLAH, sunanta Munawwara, kuma ita ce wacce na had’a ku a waya kuka gaisa. Ta ma ba ni sak’o ta ce na kawo maku kuma ta ce a gaishe ku”
Jiki a sanyaye kakele ta k’ara kallon pic d’in idonta a kan hoton Munawwara ta ce,
“To dai ita wannan kam na hango natsuwa a tattare da ita, sai dai ina jin tsoron kada a ce ita ce wannan fitsararriyar mai ido a tsakar ka.”
Basarake a take ransa ya b’ace, saboda tuno zagin da ta d’ura wa Ummi, a cikin rashin walwala ya ce,
“Kama ce kawai, amma ba ita ba ce”
Kakale tana mik’a masa wayar ta ce,
“Saboda me za ka ce ba ita ba ce kama ce? To ta ya ya har suka yi kamar?”
Basarake ya furzar da iska a bakinsa sannan ya ce,
“Tagwaye ne Kakale, a baya na so na bar komai har sai na kammala basajar da nike yi, amman wajibi ne ku na fayyace muku komai ko don na cire muku kokwanto a ranku. Munara da Munawwara ‘yan biyu ne masu kama da juna, wannan fitsararriyar da kuka gani ita ce na fara had’uwa da ita, sai ga shi na gano halinta ya sha bamban da nawa, sannu a hankali ina bibiyarsu sai na gano wannan ta photon ita ce daidai da rayuwata.”
Kakale da Ummi suka zaro idanuwa Kakale tana hararar shi ta ce,
“Ta ya za ka had’a son tagwaye wuri d’aya? Kar fa ka je ka had’a yaran mutane rigima, ka fita iskansu duka ka samo wata ka aura ya fi maka kwanciyar hankali.”
Basarake ya k’ura wa pic d’in Munawwa kallo cikin wata kasala da ta ziyarce shi nan take ya ce,
“Ina sonta sosai kakale saboda kyakkyawan halayenta, domin ke ma idan kika ji za ki so ta sosai.”
Jiki a sanyaye a kakale ta ce,
“Ina da tabbacin ba za ka yi abin da zai janyo shigar mu a matsala ba, amman duk da haka ina ji maka tsoron had’a son mata biyu a wuri ɗaya, matan ma kuma wad’anda suka fito ciki d’aya.”
Basarake ya ce,
“Ki kwantar da hankalinki Kakale in sha ALLAH babu abin da zai faru, ku dai kawai ku taya ni da addu’ar ALLAH ya zab’a mini mace tagari.”
Sai a lokacin Ummi ta yi magana, bayan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,
“ALLAH ya yi maka zab’i na alkhairi.”
Dukansu suka ce, “Amiñ. “
Sannan ya tashi ya nufi gidansa, inda shi ma yake d’aya daga cikin part biyar d’in da ke gidan. Zuciyarsa cike da fatar komai ya zo masa da sauk’i, don ya ƙudurta babu gudu babu ja da baya sai ya farauto munawynsa matuk’ar ta cinye jarabawar da yake kan yi mata.
Bayan ya yi wanka ya yi sallolin da ke kansa, sannan ya kira abokinsa Nuradden, yana tambayar shi yana ina ya zo ya same shi gida, shi ne yake sanar da shi ai ma yana kan hanyar zuwa gidan nasu, yana kashe wayar ya kira munawynsa domin ya sanar da ita ya sauka lafiya. Daga gaisuwa suka luntsume cikin danshin so sai firar masoya suke yi, saboda wuni d’aya da suka yi jin su suke yi kamar sun shekara ba su had’u ba.
Minti goma a tsakani sai ga sallamar Nuradden, sanin da ya yi gidan na gwauro ne ya sa bai tsaya jiran komai ba ya shiga k’aton falon dake tsakiyar gidan ya zauna, ya danna masa kira akan ya fito ga shi yazo. Yana waya da Munawwa ya ga kiran shi, da sauri ya mik’e tare da yin sallama da ita a kan zai kira ta idan ya k’are wani uzuri.
Sannan ya fito cike da farin cikin jin muryarta da ya yi, da murmushinsa a fuska ya isa wurin Nuradden ya ba shi hannu suka gaisa, Nuradden yana yi masa dariyar shakiyanci ya ce,
“Honey’n Munara angon Munawwara! WALLAHI ka kiyayi ranar da masifaffiyar budurwarka za ta gano ka, don ranar mai tab’arka a hannunta ma sai ya ji jiki.”
Ya k’are maganar tare da yin wata dariya, shi ma Basarake yana dariyar ya ce,
Ai tare za mu raba duk abin da ta tanadar mini ni da kai, don kai ma ka shiga rigimar, yanzu haka ma dalilin da ya sa na kira ka kenan. Domin kai naka aikin zai fara ne daga yanzu, amman fa sai ka iya takunka Alaji”
Nuradden ya zaro ido a waje yana dariya ya ce,
“Rufa ni ka saya ni, kar kasa masifaffiyar budurwarka ta tsokale mini idanuwa saboda shegen kishinta, don wannan jarababbiyar yarinyar wallahi komai za ta iya aikatawa a kanka, idan ba so kake yi ka yi wa Aysha asara ba.”
Basarake yana ‘yar dariya ya ce,
“Matsoraci fa baya zama gwani, saboda haka ka saurare ni da kyau ka ji bayanin da zan yi maka, don ya zama dole fa kai ne za ka yi mini wannan aikin, saboda amfanin da na yi da sunanka.”
Nuradden ya gimtse dariyar da yake yi saboda yadda ya ji k’irjinsa ya buga, Basarake ya so ya yi dariya saboda ganin yanayin da ya koma, amma ya basar, kai tsaye ya fiddo wayarsa aljihu ya shiga nema chat d’in da ya yi da Munawwa, ya mik’a masa wayar jiki a sanyaye Nuradden ya zura hannu ya karb’i wayar, sannan Basarake ya ce da shi,
“Karanta chat d’in za ka fi gano abin da nake nufi.”
Nuradden ya mayar da kallonsa a kan wayar sannan ya fara karanta chat d’in, yana kawowa daidai inda Basarake yake sanar da ita sunansa Muhammadu Nuradden, babu shiri ya d’ago kansa da sauri ya kalle shi, Basarake ya yi wani munafukin murnushi tare da gyara zamansa ya aza k’afa d’aya kan d’aya ya fara girgizar k’afa, alamun ba sauk’i a cikin duk wata magana da za ta fito daga bakinsa, Nuradden bakinsa yana rawa ya ce,
“Mene ne manufar saka sunana a cikin wannan issue?.”
Basarake ya had’iye murmushinsa nan take, domin ya zama so serious, kuma ya fara magana kamar haka,
“Na saka sunanka ne saboda ina son na yi amfani da kai na cimma manufata, wacce da ita ne nake son na k’ara gano gaskiyar soyayyar da Munawy take yi mini. Yanzu haka na aika mata da sako amma da sunanka, saboda haka yanzu zan kira ta ku yi waya, sai na ji abin da kuka tattauna sannan na had’a target d’ina na gaba. Saboda haka don ALLAH abokina ka ba ni had’in kai kada ka bari ko da wasa a gane ba ni bane kai plss and plss, na zab’e ka ne saboda na san kai ne ka fi cancanta da hakan, da fatar ba zaka watsa mini k’asa a ido ba.”
Nuradden ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce,
“Na san wane ne kai Aliyu! Kuma ka san duk abin da ka nema a guna ba zan tab’a k’in yi maka ba, matuk’ar abin ba na sab’a wa Mahaliccinmu ba ne. Wanda na san ko kusa kai ma ba za ka aikata hakan da gangan ba, saboda haka na ji na amince zan ba ka gudunmuwata daidai yadda kake buk’ata, yanzu fayyace mini komai ta yadda zan gane, na yi alk’awali zan yi maka koma mene ne.”
Basarake ya yi murmushin jin dad’i domin ya san daman can ba zai k’i amince masa ba, a tak’aice ya fayyace masa duk abin da yake nufi, abin da ya sa a gaba, da matakin da zai d’auka idan gaskiya ta bayyana. Nuradden ya jinjina masa sosai tare da yi masa kirarin,
“Aliyu Haidar! Basaraken K’asar Agadas! Ali mai aikin gidan Daddy! Honey’n Munara angon Munawwara! Kai a gaishe ka Muhammadu Nuradden!”
Gaba d’aya suka kwashe da dariya, suna tsaka da dariyar kiran Munawwa ya shigo wayarsa, amma ita a nufinta Nuradden ta kira, saboda Mummy ta matsa mata lamba a kan ta k’ara kiran shi tun da shi har lokacin bai neme ta ba.
Suna ganin kiran gaba d’aya suka tsayar da dariyarsu,saboda daman wayar tana hannun Nuradden shi ya sa yana ganin an saka heartbeat ya gano Munawyn Basarake ce, kuma da layin ne wanda yake amfani da shi a matsayin Nuradden. Alamu ya masa da hannu a kan ya d’auki wayae, babu b’ata lokaci ya d’auka zazzakar muryarta da ya jiyo ya sa shi natsuwa babu shiri, a can b’angarenta kuma wani dad’i ya ziyarce ta sosai, don gaba d’aya ba ta cikin nutsuwarta daga ita har Mummy, saboda banbamin bala’in da Daddy ya rufe ido yana yi musu har lokacin, shi ya sa Mummy ta matsa sai an kira shi tun da shi ya ƙi kiran. A hankali ta ce da shi,
D’azu sak’onka ya zo kamar yadda ka fad’a, sai dai Daddy ya yi fad’a sosai da ganin sak’on, shi ya sa ya ce ka zo yana son magana da kai. Saboda ka san tun farko sai da na sanar da kai akwai matsala, amma ka yi biris da zancena, don haka yanzu ka zo yana neman ka ka yi masa bayanin komai da bakinka.”
Nuradden yana murmushin da iya kacinsa a baki ya ce,
“OK ba damuwa, ki dube ni nan da kwana biyu kacal, in sha ALLAH zan zo. Sai dai komai kika ga na yi miki na yi ne kawai don son da nake miki, saboda kin ji Hausawa sun ce; tukuicin so kyauta ne, na gode sosai da kulanin da kike yi.”
Kit ya ji ta kashe wayar, saboda ita gaba d’aya kanta ya k’ulle, saboda rigimar da take ganin ya k’ara jefa su cikinta tsakaninsu ita da Mummy, sannan Daddy da Munara. Don tun lokacin Munara sai jifanta da jafa’i kala kala take yi har sai da Mummy ta so dukanta, ita ce ta hana don gudun wani tashin wata sabuwar tarzoma a tsakaninsu da Daddy, idan ta dake ta.
Nuradden da Basarake suka kalli juna suka yi murmushi, Basarake ya ce,
Shi kenan komai ya yi daidai, ni ma a ranar ce nake so na koma, fatan mu kawai ALLAH ya shige mana gaba. Daga nan suka ci gaba da tattaunawa a kan matsalar, sannan sukayi sallama. Nuradden ya tafi zuciyarsa tana ta kai-komo a kan wannan badak’alar.
Basarake kam bajewa ya yi ya kira Munawy suka ci gaba da fira duk da ya fahimci damuwar da take ciki a cikin sautin muryarta.
Ko da safiya ta waye da sak’on munawwa ya tafi yi wa su Ummi ina kwana, sai da ya fara zuwa wurin Ummi bayan ya yi mata barka da safiya sannan ya mik’a mata ledar, tare da yi mata bayanin sak’o ne daga surukarta. Duk da kayan ba wasu kaya ba ne, amman ta ji dad’i sosai kuma ta yaba.
Ganin yadda ta ji dadi ne ya sa ya kira Number’r Munawyn ya had’a ta da Ummi, cikin farin ciki ta fara gayar da Ummi da muryarta mai cike da ladabi, Ummi ta ji dad’i har a ranta ganin a waya ma yadda take girmamata ina ga fili, ta yi mata godiyar sak’on sannan suka yi sallama cikin tsantsar farin ciki. Ummi ta dinga yi musu addu’a tare da fatan a ƙulla alkhairi, Basarake zuciyarsa cike da jin dad’i ya nufi wurin Kakale.
Kakale ma da taga sak’on ta ji dad’i sosai, amman fa zuciyarta tak’i kwantawa da budurwar da yake son, saboda ita dai da zai bi ta tata; da ya rabu da tagwayen duka ya je ya nemi wata ya aura. Saboda samun nutsuwar auren shi, don ita ma ta hango akwai matsala cikin wannan tafiya, duk da bai fayyace mata komai ba, amma a ɗan abin da ya sanar da su ta hango matsala, don Hausawa sunce abin da babba ya hango yaro ko ya hau sama ba zai iya hango shi ba. Ita ma ya had’a ta da Munawwa ta yi…
Masha Allah
Very good
Very good
Very interesting book
I will like to read the book