Skip to content
Part 22 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

“Ga shi Baba kai ma ka sayi goro.”

Baba isah ya karb’i kud’in zuciyarsa cike da mamaki ya lissafa kud’in, sannan ya ce,

“Dubu biyar fa Ali? Ai ba za a yi haka ba, kai ma kana ta fama da kanka.”

Baba ya cire dubu biyu ya mayar masa da uku yace, “Ka rik’e sauran na gode ALLAH ya biya ka ya saka maka da gidan Aljannah Ubangiji ya cika maka burinka na ALKHAIRI.”

Basarake ya ji dad’in addu’ar Baba Isah baki a washe yace, “Ka bar su kawai Baba ka dai ci gaba da yi man addu’ar ALLAH ya shige muna a gaba.”

Sannan suka yi sallama Baba Isah sai zuba masa ruwan albarka yake yi, tare da yi masa addu’ar fatan nasara a rayuwarsa tare da gamawa da duniya lafiya. 

Munawwara kam da gudu ta shiga cikin gidan tana kuka,kai tsaye d’akin Mummy ta nufa, Mummy tayi saurin bin bayanta, sai da ta k’ule Munara ta tashi tana rawar murna zuciyarta cike da jin dad’i tace, “Ai sai na yi ta saka Daddy yana kuntata maku tunda har kin kasa gano abin da ya dace dake, in ban da dakikanci ta ya zaki had’a wannan had’ad’d’en guy da wancan bak’in matsiyaci dangin matsiyata.”

Daddy ya shigo ransa a b’ace ya fara hawa sama sannan ya juyo ya ce da Munara, “Duk lokacin da kika ga ya k’ara zuwa gidan nan ko ba na gida ki kira ni a waya ki sanar dani.”

A cikin jin dad’i tace, “To Daddy.”

Munawwa kam ta dunk’ule kan gadon Mummy sai kuka take yi, Mummy ta shigo jiki a sanyaye ta zauna bakin gadon tare da kiran sunanta, Munawwa ta yi k’ok’arin tsayar da kukanta tare da yunk’urawa ta tashi zaune, sai sharar hawayen da suke sauka a kan fuskarta take yi, Mummy ta rik’o hannunta a cikin sigar lallashi ta ce, “Duk da ban san abin da ya saka ki kuka ba amman na san abin ba mai dad’i ba ne, tun da daga yanayin da na ga Daddynku ya fita, Munawwara in da sabo ya kamata a ce kin saba da halin Mahaifinku, ki zama jaruma a kan duk wata matsala da za ta fuskance ki, ki daina bari zuciyarki tana rauni har ki zauna kina tsiyayar da hawayenki, shawara d’aya zan baki a duk lokacin da kika tsinci kanki cikin b’acin rai, kiyi k’ok’ari ki dinga nanacin fad’ar INNALILLAHI WA INNA ilaihirrajiuna, da sannu za ki tsinci kan ki cikin nutsuwa tare da rage k’uncin damuwar da take damunki, sannan ki kiyaye a duk lokacin da kika ji damuwa ta dame ki to ki d’auko al Qur’ani ki karanta, in sha ALLAHU za ki ji zuciyarki ta yi sanyi damuwar da kike ciki ta gushe, ki yi hak’uri kin ji kar ki gaji wurin yi wa Mahaifinku addu…”

Wayarta tayi k’ara Mummy dake kusa da wayar ta jawo ta mik’a mata, tana duba mai kiran ta b’ata fuska tare da buga tsaki ta ajiye wayar, cikin mamaki Mummy tace, “Ki d’auki wayar mana.”

Munawa ta zunb’uro baki sababon hawaye ya gangaro a kan fuskarta ta saka hannu ta share sannan tace, “Nifa WALLAHI Mummy ba na son shi.”

Mummy ta yi saurin fad’in, “Wane ne?”

Munawwa ta share hawayenta da ke ta fareti a kan fuskarta tare da gyara zamanta ta ce, “Wannan da yazo d’azu amman na ga Daddy da Munara sai rawar jiki suke yi da shi, don yanzu haka ma Munara ce ta je ta yi man gami wurin Daddy ya zo ya mare ni ya koro ni, kuma ina da tabbacin ba zai yi k’asa a gwiwa ba wajen ci wa Aliyu zarafi, narasa me Aliyu ya tare wa Munara da take ta son wulak’anta shi.”

Mummy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, “Yaushe Aliyun ya zo? ko Daddynku ya mayar da shi kan aikinsa ne?.”

Munawwa ta b’ata fuska sannan ta ce 

“A’a Mummy ya dai zo mu gaisa ne.”

Mummy ta yi tagumi idonta a kan fuskar Munawwara ta ce, “Yanzu kina nufin ba kya son d’an gidan Mustapha mai Gwal d’in?”

Munawwa ta yi saurin d’aga kai sannan ta k’ara da cewa, “Ni fa wallahi ba kud’i ne gabana ba, don sam ni kud’insu ba sa rud’a ni idan dai Munara tana son shi shi kenan, ni dai a bar ni da zab’ina don ALLAH Mummy.”

Mummy ta sauke k’atuwar ajiyar zuciya sannan ta cire tagumin ta ce, “Ki rufa wa kanki asiri ki bar wannan magana a tsakaninmu, saboda muddin kika ce ba kya son shi daga ni har ke mun shiga uku ga Daddynku, don zai ce ni ce nike zuga ki kuma bayan ni kaina wannan Aliyun fa bai kwanta man a rai ba, ki natsu ki fahimci abin da ya dace ba wai ina raina matsayinsa ba ne a’a, kawai dai hankalina ne bai kwanta da shi ba” Munawwa ta fashe da kuka gwanin ban tausayi sannan ta ce, “Don ALLAH Mummy ni dai ki taimake ni ki fad’a wa Daddy ba na son Nuradden d’in a aura wa Munara shi don Allah.” 

Mummy ranta a jagule ta ce, “Wai ke kuka ba ya yi maki wuya ne? Ni fa ba na son ganin kukan nan, ki tanadi hawayenki zuwa lokacin da za su yi maki amfani, don ina da tabbacin Daddynku ba zai taba lamunta a kan ki auri Aliyun ba, amman idan kina da jarumtar tunkarar shi da zance, kije da kanki ki sanar da shi don ni kam wallahi babu ruwana.”

Tana k’are maganar ta tashi tsam ranta a b’ace ta fita, Munawwara ta k’ara sautin kukanta saboda ita dai so take kawai a yarda da zab’inta, duk da ita kanta ta san abu ne mai matuk’ar wahala, zuciyarta ta nutsa da tunanin mafita, sai kawai Alhaji Musa ya fad’o mata a rai wato yayan Daddynsu uwa d’aya uba d’aya, ta jawo wayarta ta fara dealing number’r Yusuf, kira d’aya biyu ya d’auka cikin barkwancin da suka saba ya ce, “Student ya aka yi ne?.l” Cikin damuwa ta shanye kukanta tare da k’ok’arin saita muryarta ta ce, “Yusuf ALHAJI Baba yana gari? Gobe da safe ina son na zo wurin shi idan zan je makaranta.”

A cikin damuwa da yanayin muryarta da ya ji ya ce, “Lafiya? Me aka yi maki kike kuka Munawwara?” 

Munawwara ta shanye kukakanta sannan ta ce, “Ba na son tambaya ni dai ka gaya man yana gida gobe zan zo wurin shi, don ALLAH ka fad’a masa don ya san da zuwana.”

Kit ta kashe wayar, yusuf ya yi sororo rik’e da waya a hannu zuciyarsa cike da mamakin abin da ya b’ata wa Munawwara rai har haka, saboda sanin da ya yi mata mace ce mai sanyin hali da hak’uri duk da ya san ta gwana ce wurin kuka abu kad’an zai saka ta kuka, sab’anin Munara da abu ne mawuyaci a ga kukanta, duk da jibgar da Mummy ke yi mata lokacin k’urciyarsu, saboda d’an banzan rashin jinta don ta k’ware da muguntarsu ta k’ofi, don Mummy Ta sha wuyar Munara sosai lokacin da tana ‘yar k’arama, saboda duk lokacin da ta ci zalin Munawwara Mummy ta dake ta ita ko ranar ba za a dafa abinci a gidan ba sai dai asiyo na waje a ci, don ruwa ko zafi ba za su yi ba balle har ta kai a dafa abinci da su a ci, yadda ta zuba su haka za ta zo ta tarar da abunta, idan kuma ta zo dukan ta Daddy ya hana ya saka ta mota su je su siyo abin da za a ci, tare da yi mata gargad’i a kan kada ta kuskura ta doke ta, idan ba ta son hakan tana faruwa ta daina dukan ta, dole ba don taso ba take hak’ura sai dai idan ta cika ta watarana ta saka ta d’aki ta rufe mata baki da k’yalle ta yi ta jibgar ta, shi yasa ta kangare tun tana ‘yar k’arama don ma Mummyn a kullum tana tofe ta da addu’ar shiriya, da ALLAH kad’ai ya san inda bala’inta zai kai don wani zubin mummy sai ta je bud’a sanwarta ta ga macizai suna yawo sun cika tukunya fam, ta fito kitchen d’in da gudu a firgice Munara ta lab’e ta yi ta dariya abunta, hankalinta a kwance tun da burinta ya cika ta rama dukan da Mummy ta yi mata, don ko Munawwara sai da ta shekara biyu ba ta iya tafiya ba, sai daga baya aka gano ita ce ta yi mata k’ofi, saboda ita tun tana wata takwas ta iya tafiya, Munawwara fa bala’in da ta yi ba kad’an ba, don ma an samu abun ya rage ba kamar lokacin da suna k’ananu ba. 

Munawwa tana k’are wayar da yusuf ta ga text a kan wayarta tana dubawa taga alert d’in kud’i ne da Nuradden ya turo mata 100k, ba shiri ta zaro ido a cikin tsoro ta ce, “Shi wai wannan me yake nufi ne? Ni zai saya da kud’i koko ya abun yake ne?ni fa wallahi ba na son hak….. .”

Maganarta ta katse ne saboda shigowar Mummy idonta a kanta ta ce, “Ke da waye kike fad’a kuma?”

Munawwara ta yi saurin fad’in “Nuradden wai ya turo man dubu d’ari abu sai ka ce hauka, bacin wad’anda ya bai wa Daddy kuma fa ko ALIYU sai da ya watsa masa kud’i wai ya je ya rik’i kansa da su kada ya koma ganin shi a k’ofar gidanmu, ni fa WALLAHI Mummy wannan b’arin kud’i da yake yi tsoro yake ba ni, ko fa Munara na gan ta da kud’i a hannunta kuma na tabbata shi ne ya ba ta, sannan ga wannan motar da ya bayar da uwar siyayya, shin Mummy ina hankalinmu ya shige ne? Da ba za mu zauna mu fahimci abin da ya dace mu yi ba , yanzu fa idan za a lissafa kud’in da ya kashe a kanmu wallahi Mummy za su kai kusan miliyan uku daga had’uwarmu ko wata ba a haura ba, shin siya ta zai yI ne ko kuwa?.”

Mummy ta kai zaune babu shiri jikinta a sanyaye ta ce, “In don wannan da wannan gaskiya, amman kuma ai kin ji Daddynku ya ce masu kud’in gaske ne fa, duk da ni ba kud’in ne abun ji ba nafi so ki je inda hankalinki zai kwanta, da za ki bi shawarata ki daina zancen Aliyunnan mu duk’ufa rok’on Unbangiji a kan ALLAH ya kawo maki wani nagari da yafi, tun da dai wannan bai kwanta maki a rai ba.”

Munawwa ta sauko k’asa tare da kai gwiwoyinta k’asa ta ri’ko hannun Mummy, hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce

“Wallahi Mummy ina son ALIYU, ke ma ki so shi don ALLAH, jikina yana ba ni ALIYU shi ne kad’ai wanda zan zauna da shi na ji dad’in aure, Plsss Mummy don ALLAH ke ma ki so abin da nike so, ko da zan rage mizanin tashin hankalin da nike ciki, ni na san ALIYU ba kowa ba ne, kuma ba d’an kowa ba, amman ni dai zuciyata ta natsu da shi, saboda samu da rashi duk na ALLAH ne, idan ya so zai azurta shi ta hanyar da bai yi tsammani ba, saboda haka ni dai na ji na amince zan zauna da shi a hakan, fatana kawai kiyi ta yi man addu’a ALLAH ya sanya alkhairi a cikin lamarin.”

Kalaman Munawwara sun dabaibaye zuciyar Mummy, wanda har ta kasa samun abun fad’a saboda duk abin da Munawwa ta fad’a gaskiya ne, sai dai ita tana hango rikicin da za a yi da Mahaifinsu, don ta san ko da ya sha giyar wake ba zai tab’a amincewa da Munawwara ta auri Aliyu ba, ko babu Nuradden balle yadda ta ga ya rud’e da wuya idan zai yarda da zab’inta. 

Mummy ta fara share wa Munawwara hawayen da ke ta sauka a kan fuskarta, a cikin wata kasala da ta sauko mata ta yi jarumtar fad’in, “Ki kwantar da hankalinki k ici gaba da addu’a in sha ALLAHU komai zai zo da sauk’i.”

A cikin sanyin jiki Munawwa ta d’ora kanta a kan cinyar Mummy ta ce, “Ke ma ki na son shi ko Mummy?”

Mummy ta dafa kanta wasu hawayen tausayinta suka sirnano mata, da sauri ta saka hannu ta share don ba ta son ta gani, a cikin wata murya mai cike da tausayi ta ce, “Ni ma ina tare da ke, kuma ina goyon bayan duk abin da kike so, matukar babu sab’on ALLAH a ciki.”

Munawwara ta tashi zumbur ta rungume ta cikin tsantsar farin ciki ta ce, “Na gode Mummy, ALLAH ya saka miki da gidan aljannah.”

Mummy ta ce, “Amin, kuma ALLAH ya yi maku albarka ya ba ku mazaje nagari ya k’ara shirya man ku duka har d’an uwanku, shi ma ALLAH ya karkato da hankalinsq ya waiwayo gida haka nan.”

Munawwa ta ce, “Amiñ Mummy, ai insha ALLAHU zai dawo ki dai ci gaba da yi masa addu’a, don ba abin da ya fi k’arfin ALLAH, saboda duk tsanani yana tare da sauki.”

Da dare misalin k’arfe tara Munawwa ta nufi d’akin Daddy, har ya fara murna ya zaci Munara ce, ganin sanyinta da yadda take ta d’ari d’ari da shi ya sa ya gano Munawwa ce, nan take ya had’e fuska ko gaisuwarta a ciki ya amsa mata, ta samu jikin kujera ta rab’e gabanta yana fad’uwa ta fara magana, “Don ALLAH Daddy ka yi hak’uri ni dai wallahi ba na son mutumin nan, idan Munara tana son shi don Allah a aura mata shi a matsayin ni don Allah Daddy.”

Babu shiri ya kai kallonsa gare ta cikin tsananin fushi ya ce, “Wai ke dak’ik’iyar ina ce da kwata-kwata k’wak’walwarki ta dusa ce? Don ma kin samu ya ce yana son ki maimakon ki ji dad’i ki gode wa ALLAH sai ki koma yi wa ALLAH butulci? A zatonki kinfi shi kenan? To bari ki ji ko a k’asar waje ya so ya je ya auro mace WALLAHI da gudu za a ba shi balle ke don kin samu za ki zo wa da mutane iya shege da iskanci, WALLAHI ki kiyaye ni tun kafin in canza maki kamannu a gidannan, aure ke da shi ba fashi matuk’ar ba shi ne ya ce ya fasa ba, amman kuma kada ki ji na ce haka ki dinga wulak’anta shi har ya yi zuciya ya ce ya fasa d’in, WALLAHI ki sani koda wasa na ji kin yi abin da zai b’ata masa rai sai na illata ki a cikin gidan nan, bak’ar munafuka mai k’ashin tsiya wadda arzik’i yana kiran ta tana gudu, muguwa wadda ba ta son ganin cigaban kanta balle na wani, Wallahi idan kika yi wasa sai na tsine maki a kan auren nan!”

Munawwa ta fara kuka tana rok’ar shi a kan ita dai ba ta son shi ya dawo ga Munara, cikin zafin nama ya yi cikinta da duka, da k’yar ta samu ta fito d’akin ido rufe ta….

<< Bakon Yanayi 21Bakon Yanayi 23 >>

3 thoughts on “Bakon Yanayi 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×