Basarake ya tsura mata idanuwansa sosai ransa a b’ace, tana had’a ido da shi ta ji gabanta ya k’ire ya fad’i ba shiri, saboda tun da take ba ta tab’a had’a idanuwanta da shi ba sai ranar, ta waske tare da buga masa wani k’aton tsaki ta shige mota ta zauna, domin ba ta son ya gano ta ji tsoron shi ya ce zai raina ta.
Basarake ya k’araso idonsa a kanta ya ce,
“D’ayar hajiyar fa, ko ba da ita za mu je ba?”
Munara tana latsar waya ba tare da ta d’ago ba ta ce da shi,
“Ka shiga ka fito da ita to tun da rashin ganinta ya dame ka.”
Ya yi murmushi kamar bai ji zafin maganarta ba, ya shiga ya tayar da motar, za su fita gate Isa ya duk’o yana cewa,
“A dawo lafiya hajiya.”
Munara ko kallo bai ishe ta ba balle ta amsa masa, dole Basaraken ne ya mayar masa da amsarsa zuwa murmushi sannnan suka fice, ya hau kan titi suka fara tafiya sannan ya ce da ita,
“Ranki ya dad’e ya maganarmu ta kwana ne?, ni fa har yanzu ina kan bakana fa, ko aikin nan ina yi ne kawai a dalilinki, don ALLAH ki daure ko ya ya ne ki ba ni lokacinki.”
Munara ta ji shi sarai amma ta yi banza da shi sai latsar wayarta take yi, a cikin sanyin murya ya ce da ita,
“Hak’ik’a So masifa ne wanda idan ya sako mutum a gaba ba ya ji kuma ba ya gani, ni mai sonki ne na gaske ki daure ki so ni ko da kad’an ne, idan kin yi mini haka zan ta dawwama a matsayin bawanki, tare da dukkan ahalin gidanku gaba d’aya.”
Munara ta d’ago tare da watsa masa wani kallon wulak’anci ta ce,
“Wai kai da wa kake wad’anan surutan?, to bari ka ji na gaya maka kuskuren da kake so ka yi na k’arshe a wurina shi ne, ka sake bud’a k’azamin bakinka ka ce kana sona, wai kai me ya sa ba za ka banbance tazarar dake tsakaninmu ba?, Ni dai wallahi ka gama cutata a kalle ka a kalle ni ace wai kana sona it’s ashame wallahi.”
Ta k’are maganar da wata murya kamar ta yi kuka saboda ita a ganinta ya mata k’arshen raini da wulak’anci. Basarake bai ce da ita k’anzil ba har suka kai makarantar, ta b’alle murfin motar ta fita, har ta fara tafiya ya kira sunanta babu shiri ta waigo, a take zucitarta ta buga dam! dam! Motar ya fito ya tako har kusa da inda take tsaye ya ce da ita,
“Tunda ke ba kya sona, shin kin amince da na nemi soyayyata a wurin ‘yar uwarki Munawwara?”
Munara tayi ‘yar k’aramar dariya mai sauti sannan ta ce,
“Meye nawa a ciki? Ka je kawai idan kun sasanta kanku shikenan zan taya ka murna.”
Basarake yana murmushinsa mai kama da yak’e ya ce,
“Babu fushi?”
Munara tana Dariya ta ce,
“Fushin me? Malam ka je kawai daman da ita ka fi dacewa.”
Ya saka hannu a aljihu yana dariyar mugunta ya ce,
“Yanzu kina nufin ke ban dace da ke ba kenan?”
Ta fara taku za ta bar wurin tace da shi, “Ido mudu ne ai kai ma ka sani, ka je wurinta kawai za ku yi matuk’ar dacewa da juna.”
Ta k’are maganar tana dariya yana kallonta a cike da mamakin halinta ya ce,
“Kin ba ni ita kenan?”
Ta ce, “Kyauta ma kuwa.”
Zuwan wasu abokanta a wurin shi ya katse masu hirar, inda wata d’ayar abokiyarta ta ce,
“Shegiya muny, wannan ko da shi za a yi ne?”
Munara ta kai kallonta a kan bak’ar fuskar shi ta yi mere tana cewa,
“Direban gidanmu ne ko baku da idanuwa ne, ku kalle shi da kyau fa ku kalle ni, ai ku kun san cewa ruwa ba sa’ar kwando ba ne, ku dube shi fa da kyau dangin kutaren kuke so ku manna mini na dinga…”
Ta kwatanta yadda kutare suke yi da hannunsu tare da yin maganarsu ta hanci ta ce,
“A ba ni na Annabi”
Gaba d’aya abokan suka sa dariya, wata daga cikinsu tana dariya ta ce,
“Munny ba ki da kyau fa.”
Munara tana dariya ta ce,
“Sai a kan fuskata”
Suka bar wurin suna tafe tana kwatanta yadda kutaren suke yi tana kwaikwayon maganarsu, sai dariya suke kwasa har suka k’ule wa ganin shi yana tsaye a wurin yana kallon hanyar da suka bi.
A cikin sanyi jiki ya ja k’afafunsa ya shiga motar tare da fisgar ta da k’arfi ya bar makarantar, koda yaje gidan ya tarar da Malam Isah yana sauraren radio’n shi yana gyangyad’i, sai da ya yi horn da k’arfi sannan ya yi zumbur ya tashi ya bud’e masa gate ya shigo. Bayan ya yi parking ya zo ya zauna saman bencin Malam Isah, tare da janyo wayarsa yana danna kiran wayar Munawwaa. Saboda rashin ganinta ya dame shi sosai, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta d’aga cikin wata siririyar murya ta ce,
“Hello”
Babu shiri tsikar shi ta yi yarr! A cikin tattausan lafazi ya ce,
“Ranki ya dad’e barka da safiya, dafatar dai lafiya ce ta b’oye ki.”
Munawwa ta lumshe idanuwanta saboda jin dad’in maganar shi tace,
“Kaina ne yake ciyo, jiya ko baccin kirki ban samu na yi ba, shi yasa yau ban je makarantar ba.”
Basarake har cikin ransa ya ji zafin jin ba ta da lafiya,cikin muryar damuwa ya ce,
“Subhanalllah Uwar d’akina! ALLAH ya ba ki lafiya, ban san ya zan yi na gan ki ba da nazo na duba ki.”
Munara ta k’ara lumshe idanuwanta ta ce,
“Ayya sorry ba damuwa ai ko hakan ma na gode sosai.”
Yana murmushi ya ce,
“Naso a ce na ganki ko don na ga ya yanayin jikin naki yake, amman ba komai ALLAH ya ba ki lafiya.”
Ita ma ta yi murmushi ta ce,
“Kar ka damu ai nama ji sauk’i yanzu zan yi wanka, insha ALLAH da na ji k’arfin jikina zan fito mu gaisa.”
Yana murmushin jin dad’i ya ce, “ALLAH ya k’aro afuwa Uwar d’akina.”
Idonta a lumshe ta ce,
“Nagode sosai da adduarka.”
Ya ce, “Ba komai yi wa kai ne.”
Sannan suka yi sallama ta ajiye wayar tare da yin shiru tana nazarin kirki irin na sabon d’an aikinsu. Har ga ALLAH ta ji dad’in damuwar da ta ga ya yi da ita, sannan uwa uba muryarsa da take ji har tsakiyar zuciyarta. A cikin wani sabon kuzarin da ya ziyarce ta miƙe, saboda wayar da suka yi ta ji kwata-kwata ciyon ya tafiyar shi. Don daman can damuwar da ta saka a ranta ce ya sa ta rashin bacci da wuri, wanda ya yi sanadin ciyon kanta saboda bashin baccin da ta ci ne yake tambayarta. Domin raba dare ta yi tana tunanin abin da yake shirin faruwa da ita, waton soyayyar honey’n Munara da ta dabaibaye mata zuciya. Wanda ko rufe idanuwa ta yi shi ne take kallo yana yi mata Murmushi, a gefe d’aya kuma wannan d’an aikin nasu da Muryar shi da k’wayar idanuwansa suke sakata shiga cikin wani yanayi. Wanda ita kanta ba za ta iya fassara shi ba, sannan wannan saƙon da aka yi mata jiya ya tsaya mata a rai.
Abin mamaki yau ma tun da sassafe an k’ara turo mata wani ana yi mata ina kwana, wanda ta mayar da reply da cewa,
“Plss wanene?”
Amma har zuwa time d’in babu reply, ta ja k’afafuwanta ta shige toilet, minti biyar a tsakani ta fito tana tsane ruwa da towel d’in dake d’aure a jikinta. Ta zauna a kan gadonsu tare da dafe kanta da ta ji ciyon ya dawo mata sabo, ta sanadiyyar tuno Fuskar HAIDAR d’in Munara da a kullum ta ga fuskarsa cikin kwayar idanuwanta sai taji kirjinta ya buga dam! dam!
Ta lallab’a ta shafa mai tareda shafa hoda kad’an sai lips, ta bud’e ma’ajiyar kayansu ta saka wata doguwar rigar material wacce ake yi wa suna bubu, ta d’auko k’aramin gyale ta d’ora a kanta bayan ta shafa d’an turare sama-sama sannan ta janyo plat shoes ta saka. Ta fito babban falonsu ta tarar da Mummy tana kallon Arewa 24, tana zuwa Mummy ta washe fuskarta ta ce da ita,
“Jikin ya saki kenan?”
Munawwa tana murmushi ta ce,
“Eh na d’an ji k’arfin jikina yanzu, shi ya sa ma nace, bari na fito na d’an yawata ko da jikin nawa zai saki, bari na je na d’an zagayo harabar gida na dawo Mummy.”
Mummy ta ji dad’in ganin ‘yarta ta washe, saboda tun d’azu da ta ji shiru ba ta je gaidata ba, sannan taga Munara ita kad’ai ta tafi Makarantar, shi yasa ta je ta dubo ta. Jin jikinta da d’an zafi ta matsa mata sai da tasha tea sannan tasha magani, ko zaman da take yi a nan falon idonta kawai ne ga Tv’n, amman zuciyarta tana can tunanin ‘yarta. Shi yasa ta ji dad’in ganinta, har ta fice idonta yana kanta, saboda farin cikin ganin ta warware, domin tsananin son da take yi mata saboda biyayyar da take yi mata sau da k’afa.
Hakan ya sa nata son daban yake a cikin zuciyarta, sab’anin Munara da kullum sai ta yi abin da ba daidai ba, wanda dole sai ta b’ata mata rai tayi ta fad’a wani lokaci har da duka. Saboda ba ta wasa, amman duk da haka sai da Munara taso ta gagareta, saboda d’aurin gindin da take samu a wurin Daddynsu.
*****
Basarake yana k’are wayar da ita ya kalli Malam isah da tun d’azu yake ta kallonsa, saboda jin hirar da suke yi ya gano da Munawwa yake yi. Cike da mamaki ya kalle shi ya ce,
“Anya Ali ba ka yi tsaga da fad’i ba? Na ga fa kana son ka cusa kanka wurin yarinyar nan, ba ka gudun abin da zai je ya dawo ne? Ni dai shawarar da zan ba ka don ALLAH ka rufa wa kanka asiri ka tsaya matsayinka, ba na son ka yi abin da zai sa a kore ka daga aikinka .”
Basarake ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,
“Baba fa kasan bawa ba ya ci sai da rabonsa, ka sani ko rabon ne ya sa na zo gidan nan?”
Malam isah ya zaro idanuwa yana cewa,
“Rabo fa ka ce?”
Basarake ya gyad’a masa kai yana ‘yar dariya ya ce,
“Shi fa Baba.”
Ya ce “Cabd’ijam! To ga mu gani idan tusa za ta hura wuta.”
Basarake bai san lokacin da dariya ta zo masa ba, yana cikin dariyar Munawwa ta fito, a hankali take taku har ta k’araso wurinsu ta fara gayar da Malam Isah, sannan ta kai kallonta ga Basarake ta ce,
“Sannun ka.”
Basarake da tun da ya tsinkayo ta ya ji kirjinsa ya buga da k’arfi, saboda kyawun da ya ga tayi masa sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba. A ran shi ya furta cewa,
‘Har ga ALLAH Munawwa kina burge ni, takunki da komai naki ya yi mini.’
Wannan nazarin da ya lula shi ya hana shi jin abin da ta ce da shi, sai da ta k’ara kai kallonta a kan shi ta ce,
“Ni zan koma sai anjima.”
Sannan ya yi firgigit ya wayance, tashi tsaye ya yi yana kakkab’e rigarsa tare da fad’in,
“Ya jikin naki?”
Tana wasa da yatsunta ta ce,
“Da sauk’i”
Saboda ba ta son su had’a idanuwa, gudun ya gano yanayin da take shiga idan ta had’a idanuwanta da shi, har ta fara tafiya zata bar wurin ya d’an d’aga murya ya ce,
“Akwai maganar da nake son mu yi dake fa idan ba damuwa”
Munawwa tayi saurin kallon shi saboda fad’uwar gaban da ta same ta a lokaci d’aya. Ba tare da ta ce da shi komai ba ta fara tafiya zuwa rumfar motarsu, wurin wasu bulo-bulo da aka zagaye sabuwar shukar flower da su. A nan ta samu d’aya daga cikin bulon ta zauna tare da duk’ar da kanta tana wasa da yatsunta tana tunani a ranta, a kan ALLAH ya sa dai ba gano ta ya yi ba, don ita kam wannan abin kunya ne gare ta a ce ya gano halin da take ciki game da shi.
Shi ma ya samu d’aya daga cikin buloluwan ya zauna, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce,
“Munawwara kin san tun farkon zuwana gidan nan saboda Munara na zo, amman hankalinki da nutsuwarki da na hango ya sa na ji kamar saboda ke na zo gidan, shi yasa na ji zan iya fad’a miki damuwata ko ALLAH zai sa ki taimake ni. Har ga ALLAH ina son Munara, amman ita na ga sam ba ta d’auki hakan da muhimmanci ba, ga shi ni kuma ina son ta sosai na rasa ta hanyar da zan bi ta fuskance ni. Don ALLAH idan ba damuwa ina son ki shawo mini kanta duk da na san hakan ba mai sauk’i ba ne a wurinki, amma dai ina son ki yi iya k’ok’arinki ko da ALLAH zai sa ta fuskance ni, wallahi ni da gaske ni ke ba wasa ta kawo ni ba.”
K’irjin Munawwa ya buga dam-dam! A take ta mik’e tsaye, tare da sauke ajiyar zuciya ta ce,
“Me zai hana ka tare ta da kanka ka sanar da ita? Ina ga hakan zai fi sauk’i a kan ka aika wani d’an sak’o wurinta.”
Ta k’are maganar cikin b’acin rai, wanda ya kasa b’oyuwa a kan fuskarta. Basarake ya kallet a da kyau na tsawon minti biyu sannan ya ce,
“Ki yi hak’uri, na ga kamar ranki ya b’ace. Kin ga abin da nake ji wa tsoro tun a yanzu na fara fuskantar matsala daga gare ki, ballantana ita da na san har marina ta taɓa yi a kan kalmar son da na taɓa furta mata a ranar da muka fara had’uwa da ita. Munawwara ki taimake ni ki shawo mini kanta, saboda Allah ne ya jarabe ni da son ta ba yin kaina ba ne ni ma.”
Sai dai da ya san yadda maganganun shi suke mata zafi a zuciya da bai k’ara fad’ar irin wad’annan maganganun ba. Babu shiri hawayen da take mak’alewa yw sauko a kan fuskarta, wad’anda ita kanta idan za a titsiye ta ba ta san ko na mine ne ba.
Hankalinsa ya k’ara tashi, saboda ganin saukar ruwan hawaye a kan fuskarta, da sauri ya zo gabanta ya tsaya tare da rungume hannunwansa a ƙirji yana k’are mata kallo. A cikin sanyin muryarsa ya ce da ita,
“Na san ni ban kai matsayin da zan ce ina sonta ba, shi ya sa tausayina ya sa kike kukan nan ko? To na ji idan har ba za ta so ni ba; ske za ki iya taimako na ki share mini hawayena?”
Munawwa ta yi saurin kallon shi ido cikin ido zuciyarta sai aikin gudu take yi da sauri da sauri. Abin da ta hango cikin k’wayar idon shi ya sa ta yi…