A duk lokacin da zan ji an ambaci wani abu wai shi shakuwa ko kuma aminta ko ince aminiya, sai naji gabana ya yi wawan bugun da yai sanadiyar tarwatsa rayuwarta. Duba da yadda amana tai kanranci baza mu ce babu amin ƙwarai ba amma mafiya yawan su, maciya amana ne, domin da na jikinka ake cin amanar ka.
Aminiya wata kalmace wacce ake wa laƙabi da abin da ya shiga jikin ka ya zauna daram, tamkar fatar jikinka ce wacce launinta ke dauke da ko wani kalar na zanen hallitar ka. A wasu lokutan idan naga mutum yana rayuwa shi kaɗai nakan tuhumi kaina meye dalilin hakan, ganin babu mai bani amsa hakan yasa na ke jan bakina nai gum. A lokacin da rayuwa tai mun juyin yuyayi wai kwado ya fada a ruwan zafi. A sannan ne nagane cewa rayuwa mutum shi daya itace mafi alkairin domin babu amini na kwarai.
BABI NA ƊAYA
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Kasan cewar yau juma’a ya sa jama’a ke tafaman kai kawo jefi-jefi. Hannun Shahid ta riko, suna tafiya sai labarin masallacin juma’a yake ba ta, dariya tai ta dubeshi tana fadin, “Toh mai yasa baka ragomun alewa ba ka shanye kayan ka ai babu ruwana da kai wallahi”.
Chak ta tsaida maganarta sanadiyar abin da tai tozali da shi, Hamdan ne ke tunkaro inda take tsaye kicin-kicin tai da fuska, ƙara rike hannun Shahid tai tana kokarin tsallaka titi da mutanen ke kai komo sakamakon ba’a dade da sakkowa daga sallar juma’a ba, kuma wasun su sun tsaya daurin Aure.
Saurin da Hamdan yakeyi ne ya fara bata tsoro duk da ta dake amma kirjinta sai dukan lugude yake yana dukan tara-tara, kokarin tsallaka titin take, taji ya riƙe hannun Shahid da karfi ya jashi ya kusa rinjayar ta, tana juyowa ta dauke shi da wani irin mari wanda yai ƙara tass, har sai da ya jawo hankalin mutanen dake wurin.
Saurin dafe wurin da marin ya sauka ya yi yana dubanta, hankali tashe ya buɗe baki zai mata magana, amma ina bai samu dama ba don ta rigashi fara nata managar cikin daga murya take fadin.
“Sakin mun hannun ɗana ko nai maka ihun barawo, wannan wani irin naci ne don girman Allah, billahilazi muddin baka dena bibiyar rayuwata ba sai na yi maka abin da yafi wannan muni”.
“Wallahi Hamdan na tsaneka duniya da lahira, na gaya maka kafita daga rayuwata idan kuma ka ƙi kiji wallahi Allah sai na maka abun da baka taba tsanmmani ba a duniyar ka, banza wawa dakiki wanda bai san darajar dan adam ba, kuma gani ga Shahid idan ka kara kokarin taba shi billahilazi sai kayi dana sani banza butulu”.
Wani Dattijo ne da kalaman Mardiyya na suka sauka akan kunne shi yai saurin wai-wayowa yana fadin “Asha! ke kuwa yarinya don Allah kiyi hakuri haba wannan ai bai kamace ki ba, tun dazu ina kallan duk abin da ke faruwa amma meya ya haduku don Allah?”
Kallan tsohon Mardiya tayi tana sake kallan titi domin taga mutane sun fara taruwa, “Kayi hakuri Baba wannan ba hurumin ka bane amma dukkan maci amana karshen shi in Sha Allah sai yafi na wannan ƁARAGURBIN MUNI”.
Bata jira cewar tsohon ba ta tsallaka da sauri tana jan Shahid yaron da bai wuce shekara shida ba, tsohon ne ya juya yana duban Hamdan da ya daskare a tsaye tamkar mutum mutumi.
Dafashi tsohon ya yi yana fadin, “kayi hakuri yaro kilah sonta ka ke take maka wannan wulaƙanci ko?”.
Sabule hannun tsohon ya yi ya soma tafiya batare da yace mai uffan ba.
Tsallakawar ta yai dai-dai da tahowar ɗan sahu hannu ta samai ya tsaya kwatanta mai Anguwar da zasu tayi ya gaya mata kudin ta dauki Shahid suka shige ciki.
Tunda Hamdan ya fara tafiya tamkar wanda aka zare ma lakar jikinshi haka yake taka kasa, mamakine ya cika mai zuciya abin da bai taba tsanmmani Mardiya za ta mai ba yau shine take mawannan cin kashi a bainar duniya, shin ina son da ta take mai ina kaunar da take ikirarin tana mai, shin ko dai karya take mai dama ba don shi take ba, innalillahi wani’inna alaihi raji’un.
Tafiya ya ke yana zance zuci wanda ya fara fitowa waje, domin yadda yaga mutane suna kallanshi, ajiyar zuciya ya sauke zuciyarsa na cigaba da tafasa da abin da ya faru da shi a cikin mintinan da basu wuce uku ba.
Kofar get din gidanshi ya tura mai gadi dake zaune bakin kofar dakinshi hannunshi rike da Qur’ani yana karatu ya bishi da kallo, ganin bai kalli inda ya ke ba yasa shima ya mai da hankali shi kan karatun da yake.
Yana shiga cikin gidan ya wuce ɓangarensa wanda ke cikin gidan, Zainab da ke aiki a kichin ta hango shigar shi falo. A jiye soson hannunta tai ta fito ta nufi inda ya shiga.
Bakinta dauke da sallama ta murda kofar falon wayam taga babu kowa a ciki, haka yasa ta miƙe ta shiga bedroom din shi, nan ma murda kofar tai ta shiga da sallama, yana kwance yai rigigine gabanta ne ya fadi ganin shi a irin wannan yanayin da bata taba gani ba.
Dear takira sunanshi tana hawa gadon, jin shiru yasa ta karasa ta shafo fuskarsa jin ruwa kamar na hawaye yasa ta zaro ido waje, Abu Amrah ta kira sunansa da karfin gaske wanda ya bayyana firgicin ta a fili ƙarara.
Miƙewa ya yi ya zauna, yana dubanta fuska cike da hawaye ya furta. “Plz fitarmun a dakina don Allah”.
Kallan shi tai adan tsoroce kafin tamike tana fadin “Don nazo ina tambayarka shine haddamu wani tsawa mtswwwww! taja tsaki don ma nadamu da kai shine zaka mun haka, toh ka mutu a haka kai ka sani”.
A harzuke ya mike tsaye saukar mari taji a gefen kuncinta, da sauri ta dafe wurin ta kallanshi girgiza kai tai tana fadin, “Ni ka mara dan nazo ina maka magana”.
Gabanta ya matso yana jan tsaki cike da jin ɗacinta ya furta, “Kirama don Allah nace Ubanwa yai sanadiyar fadawata cikin wannan iftila’in idan bake ba zaki fita ko sai na miki wanda yafi na farko”.
Saurin fita tai dan dago hannu yai da niyyar sake sauke mata wani marin.
Tunda Mardiya ta shiga cikin dan sahu ta jawo Shahid a jikinta sosai ranta ke mata zafi sai ambaton kamal hasbunallahu wani’iimal wakil take domin samun sassauci daga abin da takeji yana motsa mata.
Wasu sirraran hawaye ne masu dumi su kai nasarar sauko mata akan kuncinta, ido ta kurawa Shahid tana kallan tsantsar kamar Hamdan a fuskar sa murmushin da yafi kuka ciwo tai, da za tai kukan da yafi mata dadin hakan akan da taji sauki akan abun da takeji yana kokarin bullowa ta zuciyarta.
Tsayuwar keken ne ya sanar da’ita isowar su bakin layin, sauka tai ta ciro kudinshi ta mikamai. Hannun Shahid taja suka shiga cikin gida, a bakin kofah suka tarar da Adda zaune wacce ta bisu da sannu da zuwa, ganin fuskar Mardiya chunkushe da bacin raine yasa ta wurgo mata tambayar Lafiya.
“Idan har Hamdan bai fita a rayuwata ba na rantse da tsarkin mulkin Allah zan rabashi da dukkan wani farin ciki na rayuwarsa, koma in rabashi da rayuwar baki ɗaya”.
Aysha D. Fulani