Ya yi zuru yana kallonta ita kuwa sai kwasar loman dumamenta take yi. Jefi-jefi ta kan kai kallonta kansa, sai kuma ta kauda kai. Cikin mintunan da ba su gaza biyar ba ta tashi da kwanon, bayan ta kashe ta sude hannun, sai ta turawa yaron kwanon. "Dan Abba je ka ka cewa Indo ta zuba maka wani tuwon tunda na cinye maka nakan, yaron ya tashi ya fice, ita kuma ta shafe guntun kukan da ke hannunta bisa gashinta, ta mutsuttsuke hannun, sa'annan ta warto modar ruwan da ke gabanta ta kwankwade, ta saki gatsa qyatt tana. . .
