Ba mafarki nake yi ba, kuma ba bacci mai nauyi ne ya dauke ni ba. Kawai dai na ji wani sauƙi mai ban mamaki a jikina, kamar an sauke min kaya masu nauyi da na ɗauka tsawon shekara da shekaru. Na buɗe idanuwana, amma ba idanu irin na jiki ba. Na ga komai, amma a wata siga dabam.
Na tsaya a kusurwar ɗakin kwanana, ina kallon jikina kwance a kan gado. Fuskata a nutse, kamar mai barci.
Aisha matata, ta shigo ɗakin, tana ɗauke da kofin shayi a hannunta. Ganin jikin nawa, sai ta saki kofin ya faɗi ƙasa, ƙarar. . .
