Skip to content
Part 3 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Bayanina

01.

Da sunan sarki Allahna, 

Da Yai jiki har ruhina, 

Sannan shi yai Abbana, 

Sannan shi yai Ummina, 

Yai yayye da ƙannena, 

Allahu ɗaya Ubangijina.

02.

Ƙara salati ga Manzona, 

Manzon Allah Annabina, 

Bawan Allah mai Madina, 

Shi ne sirrin ilimina, 

Domin Shi ne malamina, 

Baban Zahara Rasulullah. 

03.

Ya jama’a ga bayanina,

Bayani aakan ra’ayina,

Bayan kun ji jawabina,

Ku yo shari’a a batuna,

Bisa kan dukkan bayanina, 

Cikin hikima da tunanina. 

04.

Bayani ne a cikin raina, 

Kuma kullum yana ta damuna, 

Na rasa ma ina zan sa kaina, 

Mutane sun ɓata min raina, 

Suna zagin jagorana, 

Akan laifin duka dangina. 

05.

Ace shugaba a yankina,

Yana ta kure akan kaina,

Kuma an sani ba a gyara ba,

Kuma an yi sake ba a nuna ba,

Ana ta zagi ba a daina ba,

Shin to haka ɗin ba laifi ne ba?

06.

Shugaba dai jagora ne,

Jagora ba mala’ika ba,

Kuma shi sam laɗifi ba,

Ba Annabi ba Sahabi ba,

Kuskure kuwa bai kauce ba,

Kamar kowa ku dudduba.

07.

To in hakane a tunanina,

Me zai hana zagin mu daddaina,

Mu ɗau haƙuri da yin gyara,

Na halinmu mu d dduba,

Mu gyara kar mu ɗau hauka,

Mu sani Allah baya son haka.

08

Kai ma watarana kana laifi,

Ke ma watarana kina laifi,

Ni ma watarana ina laifi,

Ku ma watarana kuna laifi,

Mu ma watarana muna laifi,

Allah Shi ke yafe dukkan laifi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 2Tambaya 4 >>

1 thought on “Tambaya 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.