Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Bincike by Umar bin Ally

File din da inspector sani ya karbo file ne na case din wani minster da aka sace masa dansa aka nemi ya bada kudi har naira million dubu goma.

Gomnati ta nemi ayi wannan bincike a sirrince kar labari ya fita domin masu garkuwar sunce idan akasa hukuma a ciki zasu kashe yaron. Kuma sannan mutane zasu zargesu da kasa kare kansu ballantana susa ran samun kariya daga garesu.

Shidai minister maisuna alhaji Habib yanada mata maisuna Hajiya Maimuna dansu da aka sace shine kadai dansu maisuna Haneef shekararsa 7 da haihuwa tunda suka haifeshi kuma basu sake haiwuwa ba shine yasa suka dauki duk soyayyar duniya suka daura masa.

Tunda akayi masa minister ya koma Abuja da zama, a daren ranar da yazo jaharsa washe garin ranar aka sace dan nasa bayan ankaishi makaranta anje daukoshi aka tarar bayanan saikima kira da suka samu cewa anyi garkuwa dashi.

kasancewar an nemi ayi wannan bincike cikin sirri Inspector Sani baitafi da tawagar jami,ai ba yatafi ne dagashi sai Kofur Abba saikuma dansa wato Muneef domin yafara sha,awar yaga dan nasa yazama jami,in dan sanda saboda bajintar da yanuna a case din da ya gabata yanaji ajikinsa watarana dan nasa zaiyi abinda shikansa baiyi ba.

Suna sauka agarin basu tsaya ko ina ba sai gidan Hajiya Maimuna wato matar minister Habib suna zuwa Inspector Sani yafara tambayarta taya abin ya faru Hajiya Maimuna ta fara da cewa ankaishi makaranta kamar ydda aka saba akowacce safiya lokacin daukarsa kawai an aika da driver ya daukoshi aka tarar bayanan sai Kira muka samu wai masu garkuwa da mutane sun sace shi

Tana zuwa daidai nan azancenta sai kuka ya kwace mata tana mai cewa dan Allah yallabai kuceto min dana shikanai nakeda shi inspector sani yace da ita kiyi hakuri insha Allah zamuyi iya bakin kokarinmu dan muga mundawo dashi lafiya kalau

Nan take suka tafi makarantar domin su gudanar da bincike suna zuwa basu zame ko ina ba sai offishin shugaban makaranta sukai masa bayanin abinda ya kawosu sannan suka fara gudanarda binciken su.

Sunfara tun daga kan malamai har yan ajinsu da abokansa kuma aka tabbatar musu yazo makaranta kuma kamar kullum anzo an daukeshi ankaishi gida saidai ance wannan lokacin ba motarda ta saba zuwa bace wata mota ce ta daban.

Abokin Haneef wato Ibrahim shine ya bada kwatancen motar cewa bakar mota ce kirar prado domin kuwa tare suka fito har yana tsokanarsa kancewa naga fa an chanza ma mota yaushe za,a dauko tabe mufita da ita haka suka rabu suna wasa har yashiga motar suka tafi.

Inspector Sani yadubi kofur abba yace dashi indai hakane to tabbas haneef yasan wanda ya daukeshi domin ya shiga motar ne da kansa batareda wani musuba kojin tsoro sannan yace da Kofur Abba zamu yi bincike mugano wanene yake da irin wannan motar a yan uwansu.

Sun tambayi Hajiya Maimuna ta tabbatar musu da batasan me irin wannan motar ba acikin yan uwanta ko abokai Yayinda shikuma mahaifin sa yace wannan mota motace gama gari acikin abokansa dayawa sunada ita domin motace da gwamnati take yawan bawa ma”aikatan ta.

Inspector Sani yace dole zamu gudanarda bincike akansu dan zata iya yuwuwa da motar daya daga cikinsu ne aka daukeshi domin abokinsa ya tabbatar mana da irin motar aka daukeshi kuma ya shiga motar ne da kansa batare da yanuna alamun jin tsoro ba ga matukin motar.

Ba tare da wani bata lokaci ba suka fara gudanar da bincike daya bayan daya yayinda kowa ya bada tabbacin motarsa tananan a wanna ranar da akayi wannan garkuwar.

Sai mutum daya aka samu tasa motar batanan aka tambayeshi yace ai tana gurin gyara. Da aka tsananta bincike dai aka gano cewa karya yayi motar batanan akwaidai wani abu da yake boyewa nan take akaje aka bibiyi na’urar bin diddigi (tracker) na jikin motar aka bincika duk inda motar tashiga awannan ranar aka kuma gano tabbas motar tashiga wannan garin da aka sace yaron nan take aka fara tuhumarsa akan ina yaron yake.

Asannan ne jikinsa yayi sanyi ya tabbatar da cewa tabbas yayi musu karya akwai abinda yake boyewa amma bashida alaka da yin garkuwa da wannan yaro.

Tabbas motarsa bata nan kuma anyi amfani ne da ita wajen fasa Qaurin wasu kaya zuwa wannan jahar kasancewar sa babba a kasa motarsa baza a binciketa ba shine yasa akayi amfani da ita amma gaskiya baida alaka dayin garkuwa.

lokaci yanata kara kurewa gashi lokacinda masu garkuwar suka bayar kan cewa idan ba’a kawo musu kudinba zasu kashe yaron ya kusa cika.

Hankalin mahaifiyar sa ya yi mutukar tashi ta fara kuka tana rokon mijinta akan ya bada wannan kudade aceto rayuwar danta da kyar aka samu aka shawo kanta kancewa babu abinda zaisameshi za’a dawo mata dashi lafiya.

Ana cikin wannan hali ne masu garkuwar suka kira minister sukace masa tunda aka saba umarninsu akasa yansanda acikin maganar tofa tabbas kashe dansa hankalin ya mutukar tashi yace dasu zaikawo musu kudin yanzu bada sanin kowa ba yazagaya yaje ya yakai musu kudin suka fadi inda za’aje adauko yaron.

A lokacin da Inspector Sani ya samu wannan labarin hankalinsa ransa yayi matukar baci domin kuwa bincikensu ya kusa zuwa karshe amma an bata musu aiki.

Inspector Sani ya ce da minister Habib ya muna Cikin gudanar da bincike zakaje kayi abu ratsin kanka idan hakane mu menene amfanin sakamu acikin maganar kenan cikin damuwa yabashi amsa da cewa bazan iya bari su kashemin dana ba amatsayina na uba dolene nayi duk abinda zan iya dan na ceci rayuwar dana.

Amma ai saikace musu subaka lokaci kafin ka hado kudin Inspector Sani ya fada har lokacin babu fara’a a fuskarsa yasake bashi amsa da cewa sunsan komai sunsan lokacinda nashigo gari sunsan kudin da nazo dasu hatta da adadin kudin sunsani taya zan iya yi musu musu.

Akwai bayanan da aka kawo min inaso na kara tabbarwa ne shine yasa ban fada maka ba amma yanzu inaso ka fadamin suwaye sukasan da maganar kudin nan da kazo dasu inspector sani yayi tambayar yayinda yaake fuskantar.

Gaskiya ni a iya sanina bawanda yasan da maganar domin kuwa nikaina sai aranar nasan da maganar kuma adaren ranar nakarbo su ina dawowa kuwa nabawa matata ta ajiyesu.

lokacinda minister Habib yazonan azancensa sai Inspector Sani yadubeshi yafara da cewa abin zarginmu nafarko acikin wannan case din shine matarka nan take minster Habib ya fusata cikin fushi ya fara cewa,

“Bama bukatar taimakonku kutafi kawai tunda kunkasa aikinku mun biya su kudin sun sakar mana da amma kurasa wanda zaku alakanta da aikata wannan sai mahaifiyarsa.

Kaduba irin damuwarda take ciki ko abinci bata kara ci ba tundaga lokacinda tasamu wannan labarin na batar danta dan Allah yallabai kutafi haka bama bukarku yana gama fadin hakan yatafi yabarshi agurin.”

Kaitsaye dakin matar tasa yanufa yana zuwa yadora hannunsa akan kofar dakin zai bude abinda kunnuwansa suka jiye masa shine yasa ya kame awajen jikinsa yayi sanyi jiyayi kansa yafara juyawa

Matar tasa yaji tana waya tana cewa tunda yabada kudin yanzu zansan yadda zanyi nasa arufe case daganan kuma na nemi murabu daganan mubar gari mutafi wani wajen mufara sabuwar rayuwa.

Budewa yayi yashiga afusace yayinda tayi saurin ajiye wayar tabude baki zatayi magana ya dakatar da ita yana cewa meyasa mekika nema kika rasa me na rageki dashi amma sakayyar da zakimin kenan garkuwa da dana, danki.

Kafin ta bude baki tayi wata magana tuni Inspector Sani yashigo yakara da cewa acikin malaman makarantar danku akwai wanda mukayi zargi da mukaje gidan sa aka tabbatar mana aranar baidowo gida a lokacinda yasaba dawowa ba.

Munyi yunkurin tuhumarsa sai ya tabbatar mana aranar sunyi wani taro amakarantar ne bayan antashi harma ya nuna mana hotuna da akayi wanda mun tabbatar da gaskiyarsa amma kuma munyi tsintuwa acikin hotunan

Domin kuwa acikin hotunan da aka dauka kafin afara taron akwai daukar da ta dauko mana motarda akayi amfani da ita wajen sace danku bayan munsa an bincika mana number motar sai aka tabbatar mana da sunanki akayi register number.

Daganan kika zama abin zarginmu muka bibiyi jadawalin kiran wayar da kikayi inda muka samu number da masu garkuwar suke kira wanda koda ankira bata tafiya amma kin kira number harsau 20 har kunyi magana sannan bawanda yasan taya akayi masu garkuwar sukasan yan sanda sun shiga maganar sannan mijinki ya tabbatar bawanda yasan da maganar yashigo da kudi gida saike taya kenan masu garkuwar sukasan da maganar kudin bama iya kudinba hatta lokacinda yadawo gida duk sun sani.

Duk abida zaki fada zai iya zama hujja akanki agaban kotu. “koda Inspector Sani yazo nan azancensa sai Hajiya Maimuna ta fara magana cikin kuka, “Muna rayiwarmu cikin farin ciki amma tunda akaimaka minister ka watsar da lamarin mu kabarmu kakoma Abhuja da zama.”

Ka zabi aikinka akan iyalanka kana tambayata me nanema narasa daga gareka waye yagayama kudi kadai shine abinda mace take bukata agurin mijinta nima ina bukatar kulawar mijina kamar yadda kowacce mace take bukata.”

Danka yana bukatar mahaifinsa yana bukatar kulawarka bakada lokacinsa koda taron iyayen yara na makaranta mahaifinsa baitaba halarta ba shima AI yanajin zafin hakan.

Shine na yanke hukuncin da naga yafi dacewa dani nakarbi kudinnan ne dan muyi nesa dakai muje mugina sabuwar rayuwa zansa dana yadaina maraicin uba tana zuwa nan kuka ya kwace mata tausayinta yakama minister Habib yajin kamar ya rungumota yabata hakuri amma sai ya dake. Daga nan aka kamata aka tafi da ita kafin afita da ita minister habib ya karaso kusa da ita yace mata tabbas abinda kika fada gaskiya ne dana yarasa mahaifinsa amma bazan bari ya rasa mahaifiya ba kuma ki kwantar da hankalinki Zanyi duk yadda zanyi naga kinfito.

A lokacin aka fice da ita sannan akaje aka bi duk wanda suka taimaka mata ta aikata laifin suma aka kamosu sannan su Inspector Sani suka kamma hanyar dawowa gida.

Suna tafiya a mota a hanyarsu ta dowowa sunajin radiyo sukaji a labarai yan fashi sun fasa babban bankin jaharsu sun kwashi kudade da muhimman takardu.

Aikuwa kafin agama labaran yaji ankirashi a waya akace dashi ya wuce zuwa headquarter zaikarbi case din.

<< Bincike 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.