Skip to content
Part 10 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Tarihin Kafuwar Birnin Sahara

“Tarihi ya nuna cewa wannan birni namu ya wanzu tsawon shekaru da dama da suka shuɗe, lokacin da mai ƙarfi shi ke da iko, lokacin da haka kawai sai dai ku ga mahara ko mayaƙa masu zuwa su rusa gidajen mutane su kwashe mutanen a matsayin bayi sannan su tafi da dukiyoyinsu. Masana tarihi sun bayyana cewa tun farkon kafuwar garin korarrrun bayi ne suka ƙirƙire shi a matsayin mafaka daga masu kame da kuma siyar da bayi.

Bayi daga kusan kowace kusurwar duniya a wancan lokacin sukan biyo ta nan, na san zaka iya tambayan to nan ɗin a ina muke? Wannan wuri da muke yana tsakanin Birnin Libiya ne da kuma Birnin Misra. Wuri ne da ya sha banban da sauran wuraren da ke cikin wannan yanki na Sahara. Ban san ta yaya mutane ke samun shigowa har su zo wannan wuri ba, sai dai an ce a ƙoƙarin gudun ceton rai da kuma faɗawa ƙangin bauta ne suke tsintar kansu a a nan, kuma duk waɗanda suka zo basa daɗewa suke tashi su yi gaba saboda tsoron kada a biyo su a sake kama su duk kuwa da daɗin zama da wurin yake da shi, kuma in sun tafi basa kuma dawowa. Haka wannan al’amari yayi ta faruwa har aka zo lokacin cinikin bayi a ƙasar Hausa, to daga cikin irin bayin da suka gudu ne suka yi ta yawo har Allah ya kawosu wannan wuri, to ka san shi Bahaushe ba shi da dama, ko da wasu daga cikin Hausawa suka zo suka ga wuri sai kawai suka yanke shawarar zama, don haka sai suka fara gyara wurin tare da ƙoƙarin gina ‘ƴan bukkokin da za su dinga kwana a ciki. Kasancewar al’ummomi da yawa sun sha tsayawa a wajen na tsawon wani lokaci, hakan yasa basu sha wahalar samun kayan aiki ba, don haka kafin wani lokaci sai suka fara ƙawata wannan maɓoya tasu.

Daga nan kuma sai su ka dinga jawo hankalin duk wanda ya zo wurin da cewa su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen haɓaka wannan wuri domin su samarwa da kansu mazauni mai aminci da lumana. Ka ji yadda aka yi har wannan gari ya kafu. Ganin sun fara yawa sai hakan yasa suka kasu izuwa gida huɗu, kashi na farko su ne jarumai mayaƙa, su ke da alhakin koyawa sauran jama’ar gari dabarun yaƙi da kuma kare garin daga hari idan an afko musu. Kashi na biyu kuma su ne magina, su ke da alhakin gina sabbin gidaje da da sauran abubuwan da suka shafi waɗannan. Kashi na uku kuma su ne maƙera, su kuma su ke da alhakin ƙera makamai da kuma sauran kayan aikin yau da kullum. kashi na hudu kuma su ne mafarauta, su ke da alhakin zuwa daji don yin farauta tare da samo ‘ya’yan itatuwa waɗanda ake iya amfani da su a matsayin abinci. 

Daga baya, lokacin da jama’a su ka ƙara yawa ne sai aka fara faɗaɗa ayyukan izuwa maɗinka, manoma da sauransu. Yadda suka samo wannan tsari kuwa shi ne, idan baƙi suka zo sai a tara su kowa ya bayyana irin abinda ya fi ƙwarewa akai, daga nan sai a kai shi cikin ‘an uwanshi masu irin wannan sana’a ko baiwa. Sannan sai aka sanyawa kowacce tawaga shugaba wanda zai dinga jagorantarta. Kowane sashe na waɗannan ƙungiyoyi sun fuskanci ƙalubale iri daban-daban a ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansu fiye da yadda mutum ka iya tunani. To kasancewar bayi na zuwa daga ƙasashe daban-daban, hakan yasa addinai suka yawaita. Mafi yawancin addinan sun jiɓinci bautar ababen bautar ƙasar Misra ne, ƙasar rum da kuma addinin Kiristanci. Duk da cewa a wancan lokacin an samu mabiya addinin musulunci kaɗan daga cikin Hausawan da suka zauna a farkon kafuwar garin, Musulunci bai samu yaɗuwa a ƙasar ba sakamon mutuwa da mafi yawancin mabiya addinin suka dinga yi wanda wasu da dama suke alaƙanta shi da kisan mummuƙe ne. 

Duk da haka, harshen Hausa shi ne ya samu zama fitaccen harshen da ake amfani da shi saboda masu jin harshen ko amfani da shi sun fi yawa. Bayan an samu wasu shekaru, sai ya zamana garin ya fara cika, har ta kai ga maƙwabtan mu irin su Misra, Sudan da Libya sun fara ankarewa da wata al’umma fa tana rayuwa a kusa da su. Wannan dalili yasa shugabannin kowace tawaga na wancan lokaci suka zauna suka yi shawara, akan yadda ya kamata su ɓullo wa al’amarin. Bayan an zauna an tattauna, daga ƙarshe dai aka yanke shawarar katange garin daga dukkan sauran duniya. To yin hakan kuma yana buƙatar shiri babba wanda ke buƙatar ƙarfin tsafi mai girman gaske, to a wannan lokaci dama matsafa sun fara yawaita a cikin mazauna garin don haka sai aka ɗaura musu aikin nemo hanyar da za a iya aiwatar da wannan aiki a kansu. Bayan wasu ‘yan kwanaki kuwa sai ga shi sun gabatar da bincike da kuma mafitar da su ka gano a taskar tsafinsu. Mafitar ita ce, dole a zagaye gaba ɗayan birnin da katanga mai kaurin kimanin zira’i talatin, kuma dole ne wannan katanga sai an haɗa ta da jikkunan ‘yan adam rayayyu yayin gina ta, in ba haka ba kuwa tsafin da za a haɗa wajen ginin katangar ba zai yi tasiri ba. Sannan wajibi ne yayin haɗa wannan tsafi ayi amfani da jinin shugaban kowace tawaga daga cikin jagororin wannan gari, saboda da shi ne za’a ƙera karagar mulkin ƙasar wacce in ba ahalin ɗaya daga cikin waɗannan jagororin ba babu mai iya hawa karagar face sai ya baƙunci lahira. 

Haka kuwa aka yi , bayan an ɗebi jinin kowane daga cikin shugabannin tawagogin sai aka sana’anta karagar mulkin da har yanzu da ita ake amfani a wannan masarauta, sannan aka dinga kama mutane musamman masu laifi da baƙin da ba a gama amincewa da su ba ana gine su a jikin katangar birnin, da haka da haka har aka zagaye birnin gaba ɗaya da wannan gini a cikin shekaru huɗu zuwa biyar. Adadin mutanen da aka gine a jikin katangar a wancan lokacin sun kai kimanin dubu shida da ɗoriya. Domin da ya zamana an rasa masu laifi da kuma waɗanda za a gine da su, sai aka fara da shugabannnin kowace ƙungiya suna bada jama’ar su a matsayin gudunmuwa wajen yin wannan aiki. Da yawan mutane, musamman tsofaffi, sun sha miƙa kansu da kansu domin yin wannan aiki, domin suna ganin cewa su tasu ta kusa ƙarewa, amma ‘ya’yansu suna da rayuwa a gaba don haka za su iya yin komai saboda su samu rayuwa ta ‘yanci saɓanin irin wadda suka yi ta bauta. Da haka ne fa har aka kammala aikin ginin wannan katanga wadda ta zagaye garin gaba ɗaya. Kuma a wannan lokaci ne aka sa wa garin sunan’ Birnin Sahara’ saboda kakanninmu suna fatan samar da wuri mani’imci da babu kamar shi a cikin tsakiyar Sahara. 

Tun daga wannan lokaci babu mahaluƙin da ke iya fita daga cikin wannan birni face sai in ya kasance daga cikin ahalin waɗannan jagororin, ko kuma ya zamana ɗaya daga cikin su ne zai masa jagora domin ya fita, in kuwa ba haka ba, nan take zai zama gawa, wani ma ko gawar tasa ba’a gani.

Bayan kammala ginin katangar ne sai aka yanke shawarar zaɓen shugaba. Inda aka sa kowane ahali suka fitar da wanda zai jagorance su domin a tantance. Tantancewr kuwa ta hanyar yaƙi ce, yaƙin kuma na kisa. Duk wanda ya kashe saura ya zamana shi kaɗai ya rage a raye, to shi ne zai hau karaga. A wancan lokaci tawagar mafarauta ne suka ci nasara, wato Zuri’ar su Dargazu. Bayan sarkin wancan lokaci yayi shekarun sa har ya mutu sai aka ƙara tara waɗannan ahalin aka sake Gawbzawa, to a wannan karo ne ahalin mu na Maƙera suka samu damar cinye wannan gasa, kuma tun daga wancan lokaci har izuwa kan mahaifinmu su ne, ke mulki. Kuma tun daga wancan lokaci ne zazzafar gaba ta shiga tsakanin zuri’ar mu da tasu, domin kakan mu na saba’in da shida ya ƙi kashe kakan kakan Dargazu na wancan lokacin, madadin haka ma, sai ya zaɓe shi a matsayin sarkin yaƙin shi kuma ya haramta wa ahalinsu shiga gasar neman karagar mulki tare da cewa suna da babban aiki a gabansu na ba wa birnin kariya ta yadda basa buƙatar sai sun hau kujerar mulki. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin Birnin Sahara. Domin Tsofaffin da ya kamata a samu cikakken tarihin birnin daga garesu duk sun mutu. Abinda ya samu shi aka sanar da mu kuma shi muka riƙe.

Ko da Sanafaratu ta zo daidai nan a zancenta, sai ni da Sadiya muka yi shiru ko wannan mu ya kasa cewa komai, domin al’amarin dukkan mu ya girgiza mu. Shi kuwa Imran kallon wane waje kawai yake yi ya ƙi bari mu haɗa ido da shi. Bayan mun ɗauki wani lokaci a haka sai na yi ta maza na sake yi mata wata tambayar da cewa, 

“Ya ke wannan mace mai karamci, shin ko zaki iya faɗa min dalilin da yasa mahaifina ya bar wannan birni ya koma wani wuri duk kuwa da cewa ya kasance sarki mai cikakken iko?” 

Da Sanafaratu ta ji wannan tambaya tawa, sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, 

“Mutanen birnin Sahara mun kasance mutane ne masu riƙo da al’adu da kuma addinanmu na gumaka da sauran ababen bauta, babban bokan garin nan wato Hanka’u wanda shi ne kakan boka Wajagi ya taɓa bayyanawa jama’ar Birnin nan cewa duk ranar da suka bari wani baƙon addini ya shigo cikin wannan birni to za’a zo har inda suke a kashe su a raba su da wannan birni da suka gina da guminsu. Hakan ya sa ba sa son mu’amala da kowa daga waje. Duk sarakunan da suka gabata sun bada gudunmuwar su sosai wajen ganin an haɓaka al’adu da addinan birnin Sahara. Amma mahaifinmu, kasancewar ya fi kowa yawo a cikin duniya, tun bayan da ya hau mulki sai ya fara kawo canje-canje da sauye sauye. Wasu daga ciki sun yi wa jama’a daɗi musamman talakawa. Yayin da wasu kuma basu yi ba. Ba’a daɗe da hawan sa ba ya fara baiwa dukkan ƴaran ahalin sauran waɗannan jagorori damar fita waje domin su ga yadda duniya take ciki da kuma irin ci gaban da duniya ta samu. A taƙaice dai, Mahaifinmu ya nemi kawo ci gaban zamani na na’ura da kuma ilimin kimiyya tare da ƙere-ƙere. Sannann ya sanya dole kowane ɗan ahali da ya fita ya tabbatar ya iya harshen turanci kuma in ya dawo gida dole ya koyawa duk wanda suke tare da su. Wasu sun yi kamar yadda yace yayinda wasu kuma da dama suka ƙi bin umurninsa, ba komai ne kuma ya jawo haka ba face suna ganin ta yaya za su koyi yaren wanda ya dinga kama kakannin su yana siyarwa ko ya azabtar da su a matsayin ci gaba? Da yawan bayin gidan sarautar Birnin Sahara yanzu sun iya turanci da wasu yaruka kuma da yawan mutanen fada sun iya turanci don dole. To amma babban abin da ya fi tayar da hankali shi ne, Mahaifinmu ya yi yunƙurin ƙara aure, a ƙa’idar dokar birnin Sahara kuma mace ɗaya jal namiji ke aura komai muƙaminshi. Kasancewar duk addinan Birnin Sahara sun goyi bayan hakan, sai Mahaifin mu ya fara neman addinin da ya amince da namiji ya auri mace sama da guda ɗaya, a garin hakane ya ci karo da Addinin Musulunci, bayan ya canja addini ne sai ya dawo birnin Sahara da nufin ya canja yanayin tsarin birnin gaba ɗaya. Domin a wannan lokacin bala’i ya fara mana yawa a cikin birnin mu, matayen birnin sun nunka mazajen kusan sau goma, ga shi kowane namiji mace ɗaya kawai yake aure. Hakan yasa wasu iyayen suke kashe ‘ya’yansu tun suna ƙanana idan suka ga mace aka haifar musu ba namiji ba. Wasu mwzajen kuma daga cikin mutanen birnin sai suka fara kashe matayen su da gangan idan suka ga sun tsufa domin su sami damar auren yara ƙanana. Da yawan matayen birnin Sahara sun hau tafarkin abar bauta Atemisa, ma’ana babu su babu soyayya ko aure saboda guje wa irin hakan. Wannan na daga cikin dalilin da suka sa mahaifinmu tunanin ƙara aure, saboda sauran mutanen ƙasar suma su yi ko yi da shi a samu sauƙin wannan hali da aka shiga.

Amma ko da ya gabatar da wannan buƙata tasa ga sauran jama’ar fada, sai suka ƙi amincewa da zancensa, har ma suka yi masa barazanar ganin bayanshi da shi da iyalansa matuƙar bai canja addini ya dawo kan addinin da ya gada ba. Tabbas mahaifinmu jarumi ne, jarumin da a tarihin Birnin Sahara ba’a taɓa samun kamar shi ba, amma ya kasance mutum ne da baya son fitina. Don haka kawai watarana sai ya sanarwa da mutanen fada cewa zai yi wata ‘yar daguwar tafiya, amma zai bar ƙasar sa a hannun Shugaban ƙabilar manoma wato Maltanu, wanda shi ne mahaifin Nadiya. Tun daga wannan tafiya ce har yau babu wanda ya ƙara ganin shi. Bayan Maltanu ya mutu ne sai aka baiwa Nadiya riƙon ƙwaryar Sarautar kafin a yanke hukuncin da ya dace saboda ita ce babbar ɗiya a gare shi. A ƙa’ida sarautar gidanmu ya kamata a ce ta dawo, to amma mun lura da cewa so ake yi a ƙwace ragamar mulkin daga ahalinmu. Ana cikin hakan ne sai ga shi kai kuma ka bayyana. Wannan shi ne iya abinda na sani dangane da barin wannan Birni da mahaifinmu yayi.”

Ko da Sanafaratu ta zo daidai nan a zancenta, nan take sai na ji zufa taa fara keto, yayinda ƙwaƙwalwata kuma take neman sauƙi daga bugawar da take shirin yi saboda bayanan da ke zarya a cikinta suna neman su gagareta ɗauka. Zuciyata ta hau dokawa da ƙarfi kamar wanda ake shirin yanka shi. Wurin yayi tsit! Sai ka ce maƙabarta, in banda sautin fitar numfashinmu babu abin da da ake iya ji face ƙarar takun dawakin da ke jan keken dokin da muke ciki.

Bayan kalaman Sanafaratu sun fara zama a cikin ƙwaƙwalwata sosai, sai na fara tunanin ‘to ni kuwa me ya kawoni cikin waɗannan mutane? Idan har mahaifina da kanshi ya gwammace ya tafi ya barsu to ni ya na iya da su? Lallai duk ƙaddarar da ta kawo ni nan mai girma ce. In kuwa wani ne ya kawo ni, to dama ƙila so yake ya ga anyi gunduwa-gunduwa da sassan jikina. Ko da na zo daidai nan a tunanina, sai na ji wani ɓangare kuma na zuciyata na tuhuma ta da cewa, ‘To wa ya ce kayi musu wani abu da har kake ƙorafi? Kuma waye zai iya kawo ka nan in ba Allah ba?. Hakan yasa na ji kunya ma ta kama ni, daga baya kuma na fara jin haushin kaina ba tare da na san dalilin yin hakan ba.

“Me ya faru ne naga kana yamutsa fuska?” 

Sanafaratu ce ta yi wannan tambaya yayinda take kallona da waɗannan mayun idanuwan nata. Da alama tunanin da nake yi ne ya bayyana a fuskata. Don haka sai na yi murmushin ƙarfin hali sannan na ce da ita, 

“Kada ki damu. Ehm…ɗazu na ji Nadiya ta ce ki kula da ni kada in mutu, kuma ta ce za mu haɗu idan har ban mutu ba. Me hakan yake nufi?” 

Ko da Sanafaratu ta ji wannan tambaya, sai na ga ta kalle ni jiki a sanyaye sannan ta bani amsa da cewa,

“Mu ‘yn ƙabilar maƙera muna da al’adu da dama da sai mutum ya yi su kuma ya samu nasara sannan mu ke iya karɓarsa a matsayin ɗan ƙabilarmu, kuma kai ma za ka yi su, don haka sai ka shirya. Sai dai wannan mai sauƙi ne a bisa haɗuwarka da mahaifiyarmu.” 

Ina shirin tambayar ta dalilin da ya sa tayi wannan furuci ne sai ta yi min nuni da hannu alamar in yi shiru sannan ta ci gaba da cewa, “Mahaifiyarmu tana matuƙar son mahaifinmu fiye da yadda za ka iya tunani, kuma ba’a son ranta suka rabu ba. Bugu da ƙari, tafiyar da yayi ya barta da riƙon ɗaukacin ƙabilar maƙera a ƙarƙashin ikonta ya ƙara sawa ta shiga mawuyacin hali. A shekaru biyar ɗin farko da barin mahaifinmu daga Birnin Sahara ta yi alƙawarin yafe mishi idan har ya dawo. Da bai dawo ba sai ta sake shan alwashin in dai ya dawo a cikin wasu shekaru biyar ɗin to zata hora shi sannan ta bari su ci gaba da zaman aure. Haka ta yi ta shan alwashi har aka kawo wannan lokaci, a yanzu haka ta sha alwashin cewa matuƙar ya dawo a cikin waɗansu shekaru biyar ɗin, to da kanta za ta hallaka shi saboda baƙin cikin da ya sata a ciki. Ko da yake na bayyana mata cewa mahaifinmu ya mutu, kuma kana nan zuwa, hakan bai sa fushin ta ya ragu ba, domin ta sha alwashin aiwatar da alƙawarin da ta ɗauka a kanka matuƙar ka zo ɗin kamar yadda na faɗa mata.”

Ko da naji wannan batu sai na yi zumbur na miƙe tare da ce wa bawan da ke jan ragamar keken dokin mu ya tsaya, nan fa na fara ƙorafi akan don me zata hukunta ni akan laifin da ban aikata ba, amma sai Sanafaratu ta bani haƙuri tare da ce min in zauna za ta yi min ƙarin bayani. Bayan na zauna, sai ta ce wa bawan ya ci gaba da tafiya sannan ta dube ni da kyau ta ce, 

“Haidar ina so ka kalli al’amarin ta cikin idanunta, mace ce suka yi auren saurayi da budurwa da mijinta, kuma har sun samu ‘ya’ya a tsakaninsu. Suna zaman lafiya kwatsam watarana sai ya tafi ya barta ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba, a sanadiyar hakan ne ya sa mulkin da yake yi ya dawo hannunta, ita gashi bata da ɗa namiji sai mata, kuma a tsarin mulkin mu mace ba ta shugabanci,Nadiya ita ce ta farko kuma ita ma mugun nufi ne na fadawan masarautar mu yasa suka ɗora ta akai. Rana tsaka kuma sai ɗan shi da ya je can gefe ya haifa da wata matar ya zo ya bayyana mata cewa ai mahaifinshi ya mutu. Shin in kaine hakan ya faru dakai, yaya zaka ɗauki al’amarin?”

Nan da na yi shiru ina tunanin, tabbas tana da gaskiya domin a yadda tunanin mata yake (ha! kada ku feɗe ni nasan irin tunanin ku ne) kai tsaye za ta yi tunanin cin amana ne da butulci yasa ya rabu da ita domin ya je ya auri wata macen, ni kuma da na zo yanzu gani zata yi kawai na zo ne domin in ƙwace sarautar in maida ita da yaranta bayi in taka su yadda nake so. Yayin da nazo nan a tunanina sai na kalli Sanafaratu dakyau sannan na ce, 

“Na fahimci cewa tana cikin ƙunci da baƙin ciki, amma duk da haka bana tunanin ɗaukar hukunci akan wanda bai ji ba kuma bai gani ba ya dace, gaskiyar magana kenan. Kuma ma ai ni ba irin mutumin da ma take tunani bane, domin babu yadda za’a yi in ce zan wulaƙantata, asali ma ni ba ni da burin hawa karagar mulkin nan ma balle abin har ya kai ga wannan matakin, kuma ko ba komai ai ita uwa ce a gare ni.”

 Ko da Sanafaratu ta ji wannan zance nawa sai ta yi shiru tana kallona cike da mamaki, can kuma sai ta fashe da dariya sannan ta ce dani, 

“Wannan wasa ma kake yi, ai hawanka kan karagar mulkin birnin nan ne kawai zai iya kawo mana zaman lafiya tare da samun kwanciyar hankali, ban san me zai faru ba, amma jikina yana bani cewa lallai kai ne za ka zama sarkin mu nan ba da jimawa ba, amma da fari lallai ne sai ka fara samun nasarar shawo kan mahaifiyarmu tukun, don haka sai ka shirya, domin nan da wani ɗan lokaci za mu isa cikin ƙabilar maƙera.”

<< Birnin Sahara 9Birnin Sahara 11 >>

15 thoughts on “Birnin Sahara 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×