Skip to content
Part 12 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Hanya ce ɗoɗar a share ba ko tsinke, mutanen unguwar daga wanda ya gudu sai wanda ya ɓuya a gidan shi ya ƙi fitowa. Muna cikin tafiya sai muka ji hargowar mutane sun nufo inda muke, ashe an je an tattaro jarumai ne tare da ɗebo makaman ƙare dangi domin yaƙar waɗannan macizai. Da suka ganni lafiya ta ƙalau kuma ɗauke da sarauniyar su a cikin wannan keken dokin, sai duk suka tsaya cak suna kallona cikin al’ajabi. Ni kuwa ban yi wata-wata ba sai na sauko tare da kinkimo ta a kafaɗa na nufe su da gudu a firgice da nufin in miƙa musu ita a samar mata da magani ko agajin gaugawa. Ai ko da ganin na nufo su da gudu, sai suka runtuma ihu tare da juyawa da gudu. Jaruman cikinsu kuma suka nufo ni a guje, matsorata daga cikin su kuma suka yi ta kururuwa tare da bangaje juna. Nan aka tattake wasu suka karairaye. Ko da ganin wannan shiririta haka, sai dariya ta nemi ta ƙwace min, amma sai na dake sannan na ɗaga murya ina mai cewa, 

“Ku dakata, sarauniyar ku ta samu rauni ne, na kawo ta gare ku ne domin ku yi mata magani.” 

Wannan kalami nawa ne yasa suka natsu, nan take aka gabato da wani abu mai kama da akwati aka saka ta a ciki sannan muka ci gaba da tafiya muka tunkari wannan babban gini da na hango. Imran da Sadiya su ma suka rufa mana baya. 

*****

Tafiya muke yi gudu-gudu sauri-sauri domin isa inda waɗannan mutane suka nufa domin bata agajin gaggawa, amma zuciyata wani abu ne ya yi tsaye a cikinta. Da fari dai a rikice nake, domin ban san me ya faru da ita ba takamaimai kuma ina tsoron halin da take ciki ɗin. Ban kuma san yadda mutanen ƙabilar maƙera za su fahimci abin ba duba d cewa an kawo musu hari ne a daidai lokacin da na shigo yankin nasu. Sannan ɗazu da Sanafaratu take bani labarin birnin Sahara na ji ta ambaci sunan Allah bayan kuma ta ce min tafarkin abin bauta Khonshu take bi. Sannan tunda muka fara faɗa da waɗannan macizai masu kama da tsuntsaye ban sake ganinta ba. Duk iya tunanin da ƙwaƙwalwata ta yi ta kasa samar min da gamsashen bayani game da waɗannan abubuwa, kuma na kasa cire su daga zuciyata.

Bayan mun ɗauki wani ɗan lokaci muna tafiya sai muka iso wannan fada. Nan fa suka ciro ta daga cikin wannan akwati, sannan akai ta yi mata wasu abubuwa irin na surkulle amma ko motsawa bata yi ba. Nan fa hankalina ya dugunzuma na rasa abinda zan yi. Kwatsam! Kamar daga sama sai na ji muryar mahaifina a cikin ƙwaƙwalwata yana cewa ‘…kada ka manta da Allah a duk inda kake.’ Nan take kuwa na ce su kawo min ruwa, ba a daɗe ba kuwa aka kawo min wani matsakaicin ƙoƙo cike taf da ruwa. Na amsa da bismillah na fara karatu ina tofawa a cikin ruwan. Ba zan iya cewa ga iya tsawon lokacin da na ɗauka ina karatun ba ko kuma ga ayoyin da na karanta ba ko addu’o’i. Domin tun da na kammala Fatiha na daina fahimtar abin da nake karantawa. Da na gama sai na tunkari inda take kwance hannuna riƙe da wannan ƙoƙo. Har da wasu sun fara ƙoƙarin dakatar da ni, amma da na yi musu wani irin mugun kallo sai na ga sun ja da baya babu shiri. 

Ko da na ƙarasa inda take, sai na tallabo kanta sannan na yi ƙoƙari na ɗura mata wannan ruwa a bakinta da ƙyar na kuma yayyafa mata wani a jikinta. Faruwar hakan ke da wuya kuwa, sai ta yi wata irin ajiyar zuciya. Sannan kuma ta ɓarke da amai kamar an buɗe fanfo. Bayan ta ɗauki lokaci mai tsawo tana yin wannan amai, sai ta tsagaita. Ni kuwa sai na ƙara ɗura mata wannan ruwa ta sha sannan kuma na kwarara mata ragowar a kanta da sauran jikinta gaba ɗaya. Take ta sake yin wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske sannan cikin wani irin zafin nama ta miƙe tare da shaƙo min wuya. 

Na yi sauri na saki wannan ƙoƙo da ke hannuna tare da kama hannunta na riƙe gam, ya zamana ta kasa shaƙe ni irin yadda take so. Nan fa muka fara kici-kici ni da ita. Su kuwa mutanen da ke wurin sai suka yi cirko-cirko suna kallon mu kamar a fim ɗin Indiya. Bayan mun ɗauki tsawon lokaci a haka, sai na gwabza mata karo da goshi. Ko da goshinmu ya haɗu sai duk muka faɗi a sume, daga nan ban sake sanin me ke faruwa ba sai farkawa na yi na ganni kwance akan wani gado mani’imci, katifarsa mai laushi ce kamar ta kwanan yara. Na yi ƙoƙari na miƙe na zauna akan wannan gado tare da ambaton sunan Allah. A wani ɗaki mai faɗin gaske na tsinci kaina. Ko’ina na ɗakin lulluɓe yake da wata irin darduma mai ruwan ƙasa wacce da gani kasan mai laushi ce. Saman ɗakin ma irin wannan darduma ce rufe da ko’ina. Ko da na duba da kyau sai na ga ashe hotuna ne a jikin kwalliyar wannan darduma. Nan fa na ƙurawa waɗannan hotunan ido da kyau ina mamakin irin yadda aka sana’anta su haka bisa ƙwarewa. ‘Lallai ko wanene yayi wannan aikin ya kai gwani.’ na faɗi a raina. 

Ina nan zaune ina kallon wannan darduma sai na ji an turo ƙofar ɗakin da nake. Na juya da sauri domin ganin ko waye. Ai kuwa nan take na cika da wani sabon mamakin. Wata budurwa na gani wacce muka yi kama da ita fiye da yadda muka yi kama da Sanafaratu ɗauke da wani abu kamar kaya a hannunta. Kamannin da ke tsakaninmu ta kai kama har ba a magana, domin ita wannan kusan shekarun mu za su zo ɗaya a ƙiyasi, kuma ita ma komai nata irin nawa ne kamar an tsaga kara. Na saki baki kawai ina kallonta ba tare da na ce komai ba, domin ko ba a faɗa ba na san cewa ita ɗin ‘yar uwata ce. Ban ankara ba sai kawai gani na yi ta bushe da dariya sannan ta ce,

“Yaya Sanafaratu ta ce min mun fi kama da kai ban yarda ba sai yanzu. Sannu, ya kan naka?

Ta faɗi cike da kulawa tana ƙarasowa zuwa inda nake. Hakan yasa na dawo cikin hayyacina tare da dafe kaina daidai wurin da na gwabza wa mama karo. Sai lokacin na ji ɗan zafin da yake min. 

“Ya jikin mama yake?”

Na tambayeta a kasalance. Murmushi ta yi sannan ta ce,

“Da sauƙi, ta farka ma tana tambayarka.” 

“Ina abokan tafiyata kuma suke?” na kuma tambayarta. 

“Suma suna lafiya. Kowannensu an bashi masauki kamar yadda kaima aka baka. Ga kaya na kawo maka. Ka yi wanka ka sake kayan ka zo, kowa kai yake jira.”

Daga nan sai ta ajiye kayan a kusa da ni ta juya ta nufi wani ɓangare na ɗakin ta yaye wannan darduma da ta rufe ko’ina na ɗakin, ko da faruwar haka sai ga wata ƙofa ta bayyana a wurin wadda sam da fari ban lura da ita ba. Ta waigo ta dube ni sannan ta ce,

“Nan ne banɗaki, akwai komai a ciki, amma in kana buƙatar wani abu sai ka yi magana.”

“Ina buƙatar darduma ko tabarma haka mai tsafta.” na bata amsa. 

“An gama babban Yaya.” ta faɗi tana murmushi. Har ta juya za ta fita sai na ce da ita, 

“Tsawon wani lokaci na ɗauka ina kwance?” 

Juyowa ta yi a hankali ba tare da murmushin ya rabu da fuskarta ba sannan ta ce, 

“Zai kai kimanin sa’o’i uku, mun ɗauka ma ba yanzu za ka farka ba. Ka yi sauri ka shirya, kowa kai yake jira.” 

Jinjina mata kai kawai na iya kafin ta juya ta fita daga cikin ɗakin. 

Na miƙe da ƙyar jikina na min tsami na nufi inda wannan ƙofa take na buɗe na shiga tare da addu’ar shiga ɓanɗaki. Wani ƙaton bahon ƙarfe na gani da ruwa cike da shi sai tururi yake yi. Ga kuma wani irin ƙamshi da ke tashi kamar a cikin lambu. Daga gefe kuma wasu ƙananan bokitai ne guda biyu masu murfi da na san ba za a rasa ruwa a cikin su ba. Sai kuma butoci guda biyu su ma masu murfi. Can kusa da wannan bahon kuwa, soson wanka ne mai taushi da sabulu wanda da alama ta cikin shi ne wannan ƙamshi ke tashi, sai kuma wani ɗan abin ɗiban ruwa da ke kusa da shi. Sagale a sama kuma daga gefe wani tawul ne matsakaici. Daga can kusurwa kudu kuwa makewayi ne irin na zamani. 

Bayan na ƙare wa ɗakin kallo sai na tuɓe kayana sannan na shiga cikin wannan bahon wanka na zauna. Nan take na ji wani irin ni’imtaccen ɗumi ya lulluɓe ni tare da shiga kowane sashi na jikina. Saboda daɗi har ji na yi kamar kada in fita. Na dai samu na wanke jikina tas sannan na fito na tsane jikina da wannan tawul da ke sagale. Daga nan sai na ɗebi ruwa a cikin ɗaya daga cikin waɗannan butoci na yi alwala sannan na fito. Kayan da ta kawo min na ɗauka domin in sa. Wando ne baƙi mai siffar ɗinki irin na mutanen Pakistan, sai kuma wata riga mai dogon hannu ruwan ƙasa. Na ɗauki waɗannan kayan na saka. Bisa mamaki sai na ji kayan sun yi min daidai kai ka ce dama sai da aka gwada ni tukunna aka ɗinka. 

Na gama sa kayan kenan sai na ji an sake turo ƙofar a karo na biyu. Ko da na waiga sai na ga ashe dai wannan budurwar ce ta dawo. Hannunta na riƙe da wani abu da na san ba zai wuce dardumar da ma ce ta kawo min ce ba. Miƙa min ta yi ba tare da ta ce min komai ba ta juya da nufin ta fita.

“Yaya sunanki?”

Na tambayeta kai tsaye. Juyowa ta yi fuskarta ɗauke da wannan murmushin nata mai sa ni jin kamar kaina nake gani a madubi ta ce, 

“Fa’iza. Sunana Fa’iza.”

Jinjina kai na yi sunan na zauna min. Shimfiɗa dardumar na yi a ƙasa da nufin in yi sallah. Sai a wannan lokacin na tuna cewa ban san wace ƙasurwa bace gabas. Don haka sai na ce da ita,

“Suna mai daɗi. Ina ne gabas?”

“Na gode. Nan ne.” ta nuna min da hannu tana mai sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta fice daga ɗakin. Bayan ta fita ne sai na juya dardumar ta fuskanci gabas na tayar da iƙamar sallar Azahar domin gabatar da farali. 

Bayan na idar sai na fara jero addu’o’i ina roƙon Allah da ya kuɓutar da ni daga hannun waɗannan mutane ya kuma bani ikon cin jarabawar da yake min. Sannan kuma na yi wa mahaifina addu’a kamar yadda na saba. Ita ma mahaifiyata ban barta a cikin addu’ar ba, domin ko da yake tana da juriya sosai, na san cewa yanzu hankalinta in ya yi dubu a tashe yake saboda rashina. Gama addu’ar ke da wuya sai na ji wata irin nutsuwa ta sauka min wadda sallah ce kaɗai ke iya samar wa mutum da ita. Bayan na kammala addu’o’in ne sai na miƙe tare da nannaɗe dardumar na aje akan gadon da na tashi.

Daga nan sai na nufi ƙofar da na ga Fa’iza ta shigo ta ciki kai tsaye ba tare da fargabar komai ba. Ko da na fito sai na yi turus a ƙofar na tsaya ina kallon ikon Allah. Ɗakuna ne jere reras a gefen hagu da dama daga inda nake, domin ɗakin da na fito da alama shi ne na ƙarshe da ke kallon hanyar shigowa gidan gaba ɗaya. Babban abin ban mamaki dangane da wannan gida shi ne gaba ɗaya ɗakunan siffar su iri ɗaya kuma gaba ɗaya an yi musu fenti ne mai ruwan ƙasa.

Na tsaya kawai ina kallon wanna wuri bakina a buɗe. Can kuma sai kawai na miƙe wannan hanya reras ba tare da sanin inda hanyar ta nufa ba. Ban daɗe ina tafiya ba sai na ga an turo ƙofar ɗaya daga cikin waɗannan ɗakuna an fito. In duba haka sai na ga ashe dai Imran ne, jikinshi sanye da sabbin kaya shige irin nawa, sai dai shi nashi koraye ne. Muka gaisa tare da yi wa juna barka da sake haɗuwa. Daga nan kuma sai muka ci gaba da tafiya muna hira muka tunkari ƙofar wannan gida wadda muka fara hangowa daga inda muke. Bayan mun wuce ɗakuna kimanin guda biyar sai kuma muka gamu da Sadiya ita ma ta fito daga wani ɗaki daga cikin waɗannan ɗakunan. Jikinta sanye da wasu baƙaƙen kaya irin na matan mutanen wannan yanki na ƙabilar maƙera. Muka gaisa da ita itama tare da tambayar juna yadda muka kasance bayan rabuwar mu. Ba ƙaramin daɗi na ji ba da ganinsu, musamman ma Sadiya wadda ta sha baƙar wahala a hannun su dargazu. Daga nan sai duk muka rankaya muka nufi wannan ƙoda wadda za ta fidda mu daga cikin wannan gida. 

Ko da muka ƙaraso ƙarshen waɗannan ɗakuna wanda kuma ya yi daidai da isowar mu bakin ƙofar sashen gaba ɗaya. Har na ɗora hannuna akan ƙofar sai muka ji an buɗe ƙofar ta waje. Nan take muka sa kai ta cikin ƙofar kai tsaye muka fita daga sashen gaba ɗaya. Fitowar mu ke da wuya sai muka yi arba da cincirindon mutane maza da mata sun zagaye wani0pp fili wanda aka hura . Wasu a zaune, wasu a tsaye gasu nan dai birjik. Tsayawa kawai na yi ina kallon su tare da ƙoƙarin ganin na fahimci dalilin wannan taruwa da suka yi. 

Ko da ganin wannan wuta tana ci balbal da rana tsaka haka, sai Sadiya ta ruƙo min riga tana me cewa, 

“Wayyo Allahna. Yaya Haidar ko dai gasa mu za su yi su cinye? Anya ba sa cin naman mutane kuwa?” 

Dariya ce ta nemi ta ƙwace min sakamakon jin wannan tambaya da ta yi, amma sai na danne. Sannan na ce da ita,

“Haba ke kuwa, sai ka ce wasu kaji. Wataƙila dai wata al’ada ce irin tasu kawai.”

Kaɗa min kai kawai ta yi, amma alamu sun nuna cewa bata gama gamuwa da wannan batu nawa ba. 

Shi kuwa Imran shiru ya yi kawai yana rarraba ido kamar arnen da ya tsinci kanshi a filin idi. Mamana na hango a zaune kamar babu abinda ya same ta. Tsaye a gefenta kuma Sanafaratu wacce duk jini ne a jikinta, ga wani sabon tabo a gefen fuskarta na dama. Ai ko da ganin wannan tabo sai na ji zuciyata ta ɓaci, nan da nan na hasala. Ban san lokacin da na nufi inda take ba da sauri na riƙe hannunta tare da cewa,

“Me ya same ki? Ya akai kika ji wannan raunin? Waye ya ji miki shi?”

Na jero mata waɗannan tambayoyi ina mai dudduba jikinta ko zan ga wani tabon amma ban gani ba. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce,

“Kada ka damu ƙanina, lafiyata fa lau. Da ka ga wanda ya yi min tabon da sai ka fi tausayin shi a kaina. Zan baka labari daga baya.”

Kai kawai na iya jinjina mata sannan na duƙa a gaban mamana na kamo hannunta cike da kulawa inamai cewa,

“Sannu Mama, ya jikin naki? Babu inda ke miki ciwo ko?” 

Saboda har cikin zuciyata nake jin na damu da su kamar dama can na sansu ne. Gaskiyar Bahaushe da ya ce jininka naka ne har abada. Murmushi kawai ta yi min tare da ɗaura ɗayan hannunta akan nawa. Yin hakan ke da wuya na ji wata kakkusar murya ta ce da ni, 

Gabato gabanmu ya kai wannan baƙo. 

<< Birnin Sahara 11Birnin Sahara 13 >>

6 thoughts on “Birnin Sahara 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×