Shiru suka yi aka rasa wanda zai ce ƙala, tamkar an yi ruwa an ɗauke. Daga wannan ya kalli wannan sai wancan ya kalli wancan. Bayan an ɗauki tsawon lokaci a haka sai Shamadara ta dube ni cike da damuwa ta ce,
“Waɗannan abubuwa da ka buƙata abubuwa ne masu tsadar gaske Haidar.”
“Na sani Mama, sai dai duk tsadar su ba su kai rayuwata ba. Idan har za ku iya tambaya ta da in sadaukar da rayuwata domin samun maslahar matsalolinku, to kuwa ba zai zamo matsala ba don na buƙace ku da ku miƙa wuya a gare ni.”
Na bata amsa cike da girmamawa. Ina kallon yadda sauran suke gyaɗa kai, alamar sun yarda da maganata. Daga nan sai Sanafaratu ta ce,
“Ni a ganina ba mu da wata mafita face mu yarda da abinda ya ce. Ko ba komai wannan karon ɗan’uwanmu ne ya buƙaci da mu miƙa wuya ba bare ba. Kuma na yi imani cewa ba zai ba mu kunya ba. Don haka ni dai na amince da waɗannan sharuɗɗa.”
Murmushi na yi mata sannan na ce da ita,
“Na gode sosai. Ku fahimce ni, ba don na mulke ku nake son miƙa wuya daga gare ku ba, sai don in yi abinda ya dace. Kuma na yi muku alƙawarin duk abinda zan yi ku zai amfana daga yau har zuwa ƙarshen rayuwarku.”
Wannan magana da na yi ta sa jikinsu ya yi sanyi matuƙa. Nan take dukkansu suka yi min mubaya’a, Ashalle ce kawai ba ta yi ba. Ban nuna damuwa game da hukuncin da ta yanke ba. Hakan ya sa ta tambaye ni da cewa,
“Yanzu ni da ban yi maka mubaya’a ba ya za ka yi da ni kenan?”
Murmushi na yi sannan na ce da ita,
“Duk abinda jininka ya yi ko ya zama yana nan a jininka, babu abinda zai canza hakan. Ke jinina ce, babu abinda zai canza hakan.”
Daga nan ba ta ƙara cewa komai ba, ni kuma ban yi wata-wata ba na biya musu kalmar shahada suka maimaita. Daga nan kuma na hau yi musu bayani game da Addinin Musulunci. Abubuwan duk sai na ga sun zo da sauƙi ba kamar yadda na yi tunani ba da farko. Su ma sai na ga suna fahimtar bayanina da kyau saboda da ma sun san wasu abubuwan daga mahaifina. A haka dai har Magriba ta yi, na ja su Salla sannan na barsu tare da Sadiya ita kuma tana yi musu ƙarin bayani, musamman game da hukunce-hukuncen da suka shafi mata. Ni kuma muka ci gaba da tattaunawa da Imran.
A cikin tattaunawar tamu ce yake bayyana min irin ƙarfin alaƙar da ke tsakanin zuriyarsu da tamu. Har ma yake faɗa min cewa dukkan bargunan da na gani a ɗakunan nan gidajen kaf daga wurin zuriyarsu ya fito. Haka dai muka ci gaba da tattaunawa cikin fara’a da annushuwa. Na samu ilimi game da birnin Sahara sosai a wurin Imran. Babban abin da ya fi ba ni mamaki sama da komai kuwa shi ne irin tarin dukiyar da na gani a taskar gidanmu. Da yake ba sa amfani da kuɗi irin namu, ƙarafan daraja ne ga su nan tsibe. Zinare, lu’ulu’u, zubarjadi, azurfa da deman ga su nan maƙil.
Cikin kwanaki biyar al’amura suka fara sauyawa a cikin ahalin maƙera. Sadiya da Fa’iza kuwa tuni su zama ƙawaye, don haka koyaushe suna tare da juna. Ba tare da ɓata lokaci ba kuma Mamana Shamadara ta gayyaci dukkan masu muƙamai na yankin maƙera taron gani na musamman. A wannan taro ne ta bayyana musu cewa ta sauka daga matsayinta na jagorancin ƙabilar ta mayar da komai hannuna. Sun yi murna sosai da jin haka, domin sun nuna hakan a fili. Nan take ni kuma na yi musu taƙaitaccen bayani game da kaina da kuma wani ɓangare na shirina na ganin na kawo wa birnin Sahara ci gaba baki ɗaya. Ban kuma ɓoye musu komai ba game da addinina da kuma yi musu tayin shiga.
Da yawansu sun yarda da tsarin nawa, addinina ne dai ƙalilan daga cikinsu suka karɓa. Ni kuma na nuna musu babu komai, duk wanda ke so ya ci gaba da addininsa babu matsala matuƙar dai ba zai shiga haƙƙin sauran addinan ba. Wannan magana tawa ta yi musu daɗi sosai kuma sun sha alwashin yi min biyayya tare da ba ni haɗin kai wurin tafiyar da al’anurana yadda nake so. Ban barsu sun tashi a wurin ba sai da na tabbatar cewa duk wani wanda yake da wani haƙƙi a wurin zuriyarmu an biya shi haƙƙinsa. Waɗanda ke bin wasu bashi a tsakaninsu ma na sa aka biya musu bashin da ke tsakanin junansu sannan na sa aka yi wa kowanne daga cikinsu kyautar alfarma. Wannan abu da na yi fa ba ƙaramin burgesu ya yi ba. Na sha godiya da sa albarka a wurinsu wasu har suna kuka.
A rana ta shida ne na sa aka kira min dukkan bayin da ke gidan suka taru a wani faffaɗan fili da ke bayan gidanmu. Dukkansu kuwa suka taru maza a gefen dama, mata kuma kuma a gefen hagu. A ƙalla sun kai mutum ɗari uku da arba’in dukkansu. A wannan lokaci kuwa dukkan ‘yan’uwana suna tare da ni. Dama tun a daren jiya mun yi zama na musamman ni da su kuma mun cimma matsaya game da hukuncin da nake so in yanke. Bayan sun gama taruwa sai na miƙe na yi musu bayanin ko ni wanene da kuma matsayin da nake da shi a yanzu. Sannan na sanar musu da cewa na ‘yantar da su gaba ɗayansu. Kuma a madadin hakan ba na buƙatar komai daga gare su face su shiga Addinin Musulunci, shi ma ba dole ba ne sai ga wanda ya yi niyya. Sannan daga ranar duk wanda zai yi aiki a gidan za a dinga biyanshi albashi ne duk wata ba kyauta zai dinga yi ba. Za kuma a inganta musu wurin kwana da suturar da za su saka da abincin da za su ci. Amma duk wanda ya shiga Addinin Musulunci, to in yana da ‘yan’uwa da suke bauta a wani wuri zan ba shi kuɗin da zai je ya fanso su, wanda ba shi da mata in yana so zan ɗauki ɗawainiyar auren ko mace ko namiji. Sannan na karanto musu dokoki da ƙa’idojin aiki da gidanmu, da kuma irin aiyukan d za a dinga yi mana da albashin kowane aiki. Nan fa wuri ya kaure da farinciki da murna wasu har suna suma. Gaba ɗayansu a wannan rana sai da suka karɓi kalmar shahada. Daga nan na bayyana musu cewa masu son zama dakaru su ware wuri guda, na kuma ce Ashalle ce za ta kula da su. Ba tare da musu ba ta je wurin da aka ware domin su ta fara ɗaukar sunaye. Shalibai kuma na ce ita ce za ta kula da masu aikace-aikace gida. Haka dai na raba wa kowa ɓangaren da zai kula da shi. Mamana Shamadara ita na ba wa alhakin biyan kowa albashi da kuma biyan kuɗin fansar ‘yan’uwan waɗanda suka musulunta.
Daga nan kuma sai na sa aka ƙara kira min waɗannan dattijai na ƙabilar maƙera, na ce kowa ya kawo min adadin bayin da ke bauta a ƙarƙashinsa ni kuma zan fanshe su gaba ɗaya. Haka na bi bayin nan kaf na ‘yantar da su sannan na sawa kowa dokar duk wanda zai yi aiki to a biya shi haƙƙinsa. Sannan na bi duk wata maƙera na gyara ta kuma na sa musu haraji daidai yadda ba za su takura ba. Daga nan kuma sai na sa aka buɗe ƙofar yankin maƙera domin masu son yin ciniki da mu su shigo kuma mu ma masu son yi su fita su yi kasuwancinsu. Duk wannan abu cikin sati biyu ya gudana.
A cikin sati na uku ne watarana muna zaune ni da ‘yan’uwana muna cin abincin rana. A wannan lokaci har mun saba da juna da su Shalibai da Baruma. Ita kuwa Fa’iza dama duk ta fi su fara’a, don haka sai zolayana take yi. Ashalle ce kawai zan iya cewa har yanzu ba mu wani saba ba. Amma duk da haka ba ta ba ni wata matsala. In na ce ta yi wani abu kai tsaye take yi. In wani abu ne da take ganin cewa ya saɓa wa ra’ayinta, da zarar ta yi magana in na fahimtar da ita shikenan. Har dai ya zamana yanzu tambayoyin ma sun yi sauƙi. Gidan ya fara cika da mutane yanzu, domin kusan kullum sai an samu wasu sun zo domin su musulunta ko kuma sun zo neman aikin yi ko kuma sun zo neman taimako a kuɓutar da ‘yan’uwansu daga ƙangin bauta. Wannan sa kullum cikin uzuri muke. Sadiya da Imran sun fi kowa jajircewa,musamman wurin koyar da sabbin musulunta ɓangaren addini.
Muna nan zaune muna cin abinci cikin annushuwa, kwatsam sai na ga dogarawa sun shigo, hannuwansu ɗauke da tutoci farare alamar zaman lafiya. Ban yi aune ba sai kawai na ga Sarauniya Nadiya ta danno kai zuwa cikin farfajiyar gidan. Wani irin tsalle zuciyata ta yi ta zo maƙoshina ta tsaya, kafin daga baya ta koma inda take. Wata irin shigar alfarma Sarauniya Nadiya ta yi da ta yi mata kyau matuƙa. Gaba ɗaya kayan jikinta farare ne, ita kanta sai na ga ta ƙara yi min haske da kyau. Ban san na hangame baki ina kallonta ba har sai da ni ta taɓa ni tana mai cewa,
“Rufe bakin haka Yayana ka da ƙuda ya faɗa.”
Duka na kai mata ta goce tare da rugawa da gudu ta rungume Nadiya tana yi mata barka da zuwa. Har dogarai sun yunƙura da nufin su yi maganinta amma sai Nadiya ta hana su sannan ta ce su koma can gefe su tsaya. Daga nan ita da kanta ta har inda Shamadara take ta gaisheta cike da girmama. Daga nan sai Mamana ta yi mata izinin zama akan wannan teburi. Ba musu ta je ta zauna kusa da Sanafaratu. Bayan ta zauna ne sai nan da nan kowa ya fara kawo mata gaisuwa. Bismillah Sanafaratu ta yi mata. Ta ci abincin kaɗan sannan suka ɗan taɓa hira da Shamadara da Sanafartu.
Ashalle ce ta fara tashi daga teburin ta ce za ta je ta duba waɗanda ta ke ba horon yaƙi. Daga nan sai Fa’iza. Imran da Sadiya su ma sai suka tashi suna masu cewa akwai ɗalibai na jiransu a makarantar da muka kafa. A haka dai duk suka sulale, ya rage dags ni sai Nadiya da kuma Mama Shamadara. Tsit wurin ya yi aka rasa wanda zai fara yin magana. Bayan mun ɗauki tsawon lokaci a haka sai Shamadara ta ce,
“Ya kai ɗana, shin ba ka sarauniyarka ba ne?”
“Na ganta Mama.” na ba ta amsa a taƙaice.
“To ai ya kamata ku gaisa ko?”
Ta tambaya tana mai kafe ni da ido. Da kamar ba zan ce komai ba, amma daga baya sai na sa gwiwata guda ɗaya a ƙasa na yi mata irin gaisuwar da ake yi mata. Wannan abu da na yi ne ya sa Shamadara yin murmushi sannan ta ce,
“Sanafaratu ta faɗa min cewa akwai wani tarihi a tsakanin ku biyun nan. Ban san ko wane iri bane, kuma ba zan takurawa ɗayanku da ya faɗa min ba. Abinda kawai zan iya cewa shi ne, ku daure ku tattauna da juna. Domin tattaunawa musayar ilimi ce, gardama kuma musayar jahilci ne. Na yi imani da cewa dukkanku ba jahilai bane. Fatan ba za ku ba ni kunya ba.”
Daga nan ba ta ƙara cewa komai ba sai ta tashi ta tafi abinta. Bayan ta wuce ne sai na dubi Nadiya da kyau na ce da ita,
“Me ya kawo ki nan Nadiya?”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗago kai tana kallona da mayun idanuwan nan nata masu rikita tunanin dukkan wani mai kallon su. Murmushi ta yi wanda ba shi da alaƙa da farinciki sannan ta ce,
“Ka yi haƙuri Haidar. Na san cewa na yi maka ba daidai ba. Na san na ɓata maka rai, kuma ban san tsawon lokacin da ka ɗauka kana gurmususu da abinda ke damunka a zuciya ba. Amma na san iya lokacin da ni na ɗauka kafin na iya danne tunaninka daga yi wa rayuwata barazana. Ina roƙonka da dukkan wani abu da ka ke ganin ƙimarsa da ka yafe min laifina. Kuma ina so ka sani cewa duk abinda na yi ba ma yi bane don ba na sonka ko kuma don son zuciyata. Ba ni da zaɓi ne a wancan lokacin, amma yanzu ina da shi kuma na zaɓi zuwa da kaina domin in nemi afuwarka. Don Allah ka yafe min.”
Ko da ta zo nan a zancenta, sai na ga hawaye sun fara zubowa daga kayawawan idanuwanta suna sauka akan lallausan kumatunta. Duk wani fushi da nake yi da ita sai na ji yana narkewa da sauri-sauri tamkar an zuba wa gishiri ruwa. Cikin sanyin murya na ce da ita,
“Nadiya, ba kya buƙatar sai kin yi min magiya. Na riga na yafe miki tuntuni, abinda ya wuce ya riga da ya wuce. Kuma kamar yadda ki ka faɗa, ba ki da zaɓi ne, yanzu na fahimci hakan. Sai dai ban san a wani matsayi zan ɗauki tarayyar mu ba a yanzu.”
Wannan karon murmushin da ya bayyana a fuskarta na farinciki ne, saboda taushinsa ma na musamman ne. Share hawayenta ta yi da wani irin farin hankaci mai ƙamshin gaske. Bayan ta gama sai ta kalle ni a nutse ta ce,
“Muna iya ɗorawa daga zumuncin da ke tsakanin iyayenmu kafin su bar duniya.”
Mamaki ne ya danne ni. Kacaniyar aiyukan da na fara yi a yankin maƙera har ya sa na manta da cewa akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin zuriyarmu da ta su Nadiya. Jinjina kai na yi sannan na dubeta na ce,
“Hakan ya yi min. Amma in ba za ki damu ba, zan so ki min bayani game da irin zumuncin da ke tsakanin iyayenmu. Ban san komai ba game da hakan, kuma zan so sani a yanzu tun kafin lokaci ya ƙure min.”
Ajiyar zuciya ta sake yi tana mai gyara zama sannan ta ce,
“Maltanu shi ne mahaifina, kuma shi ne shugaban manoma na birnin Sahara. Duk wani kayan abinci da ake amfani da shi a birnin Sahara daga wurinmu ake samu saboda ƙasar yankinmu ne kaɗai ke iya fitar da hatsi a duk faɗin birnin Sahara. Wannan dalili ya sa ake ɗaukar mu da muhimmanci sosai a cikin al’ummar wannan birni baki ɗaya. Kowa yana so ya yi mu’amala da mu saboda samun kayan masarufi. Sai dai ahalin maƙera ne kaɗai suke mu’amala da mu da zuciya ɗaya. Wannan dalili ne ya sa zumuncin da ke tsakanin yankunan namu ya fi ƙarfi fiye da na kowanne. “
Dakatawa ta yi na ɗan wani lokaci sannan ta ci gaba da cewa,
“Tun da can muna shukan amfanin gona irin su doya, wake, dawa, masara, gurji da sauransu. A hankali kuma sai muka dinga fita muna ƙaro ilimi game da noman zamani da sauransu. Yau ga shi mun wayi gari har mangul da gishiri muna sarrafawa, kuma duk mun samu wannan nasara ne sakamon gudunmawar da muke samu daga hannun zuriyar maƙera. Wannan ya sa akwai aminci mai ƙarfi a tsakanin ɓangarorinmu. Shi ya sa ma da mahaifinka zai yi wannan doguwar tafiya ya bar riƙon sarautar a hannun mahaifina. To sai dai kuma, akwai wani babban dalili da ya sa mahaifinka daɗewa bai dawo ba daga wannan tafiya wanda ba kowa ya san da shi ba. Nima kaina bam sani ba sai da mahaifina ya kwanta ciwon ajali tukunna.”
“Nadiya, idan ba kya so ba lallai sai kin faɗa min ba. Sirri yana da daɗi, kuma kowa yana da nashi.”
Na faɗa a sanyaye domin jikina na bani cewa abin da duk za ta faɗa min to ba ƙaramin sirri bane. Girgiza kai ta yi cikin nuna rashin damuwa sannan ta ce da ni,
“A’a Haidar, duk da cewa sirri ne da ban taɓa faɗa wa kowa ba, akwai buƙatar in sanar da kai domin kai ma ya shafe ka. Wataƙila ma ka san wani abu game da hakan wanda zai iya taimaka min nima.”
Cikin rashin fahimtar maganarta na ce da ita,
“Kamar yaya kenan?”
“Mahaifina yana da ƙanwa guda ɗaya da ta ɓace. Lokaci ɗaya kawai aka bemeta aka rasa. Kuma a wannan lokaci ana gab da ɗaura mata aure ne da wani wanda ba ta so. An yi neman duniyar nan amma ba a ganta ba. Lokacin da mahaifinka zai yi wannan doguwar tafiya sai mahaifina ya roƙe shi da ya bincika daga nan ko zai gano inda ƙanwar tasa take. Sai dai har mahaifina ya mutu bai dawo ba balle mu san ya gano inda take ko bai gano ba.”
Ko da ta zo daidai nan a bayaninta, sai nan da nan na ji wani irin gumin da ban san ko daga ina yake ba yana keto min. Cikin tsananin ruɗewa na tambaye ta,
“Ya… Sunan.. Ta? Ita ƙanwar mahaifin naku ya sunana?”
“Murjanatu.”
Ta bani amsa cike da rashin fahimtar dalilin da ya sa ni ruɗewa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka.
Very nice