Skip to content
Part 2 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Da fari har na yanke shawarar in tsaya su kamani kawai don na san dai in ma an kaini kurkukun, to dole a fito da ni, amma daga baya kuma sai na yi tunanin me zai hana in jaraba guduwa? Tunda an ce me rai ba ya rasa motsi? A dai-dai lokacin da nake wannan tunani tsakanina da dakarun Sarauniya Nadiya bai fi tazarar taku biyar ba. Don haka ban yi wata_wata ba sai na juya ina mai falfalawa da gudun tsiya na nufi wannan murtukekiyar katanga da ke kusa da mu.

Habawa! Nanfa aka kasa tsere tsakanina da waɗannan dakaru nata kamar karnuka sun biyo zomo. A zahiri sun fi ni gudu, to amma kasancewar ni gudun ceton rai nake yi sai na ƙara dagewa. Amma fa a duk sa’adda na waiga sai in gansu dab da ni. Babban abinda ya fi tayar min da hankali shi ne, sahara ce wajen babu daɗin gudu, ba don ma Allah yasa mun saba da gudu a cikin yashi ba a ƙauye, to da tuni sun kama ni, kuma gashi ban kai ga isa ganuwar ba. Haka dai na wanzu ina mai ci gaba da falfala gudu ba ji ba gani amma sai ya zama na banza domin duk lokacin da na waiga sai in ga waɗannan dakarun gab suke da kamo ni.

Kwatsam, Sai na hango wani tarin itace da aka jera a jikin wannan katanga da ke zagaye da inda muke. Nan fa na ƙara azama wajen ganin na kai ga wannan tarin itace. Ni da nufina shi ne in yi matakala da icen in haura katangar. Ina zuwa kuwa ban yi wata-wata ba wajen hawa kan wannan tarin itatuwa, sai da ya zamana bai fi taku biyar ba in kama ganuwar sai na ji an ƙwala min kira da wata murya wacce take sautinta yasa na ji gaba ɗaya na’urorin jikina sun tsaya cak! Sun daina aiki. Take na ji gabana ya bada wata ƙara dum!! Yayinda wani ƙaƙƙarfan tunani ya ziyarci zuciyata ba tare da na yi aune ba.

“Sadiya?” Na furta sunanta a hankali cike da mamaki yayinda ƙwaƙwalwata ta fara zarya a tsakankanin abubuwan da suka faru da ni a baya, inda cikin ƙanƙanin lokaci ta kamomin hoton fuskarta a cikin zuciyata.

Sadiya ita ce macen da nake matuƙar so a rayuwata kamar yadda nake son tawa rayuwar, kuma na sha jefa tawa rayuwar a haɗari domin ceto tata. Ita ɗin tamkar ƙanwa take a gare ni, amma yadda nake ji game da ita a wannan lokaci ya wuce son yaya da ƙanwa. To me ya kawota nan? Ya ma aka yi har ta zo nan? Waɗannan da ma wasu tambayoyin ne suka yi min caa! a cikin ƙwaƙwalwata.

Feu! Feu!! Feu!!! Na ji ƙarar wasu abubuwa na wucewa ta kusa da fuskata, in duba haka sai na ga ashe kibiyoyi ne.

‘Subhanalillahi!’

Na faɗi a fili ba tare da na san na faɗi ba a daidai lokacin da hankalina ya komo jikina daga tunanin da na fara yi. Nan take na fara karanta Ayatul kursiyyu tare da Lai’la Ha illah Anta Subhanaka Inni Kuntu Minazzalumin a cikin zuciyata. Aikuwa nan take na ji wani sabon ƙarfi ya shige ni kuma gaba ɗayan wani tsoro da fargaba tare da gajiya sun fita daga jikina. Cikin Wani irin baƙin zafin nama na juyo da baya ina mai falfalawa da wani irin sabon azababben gudu na ban mamaki tamkar tauraruwa mai wutsiya.

Aikuwa sai gashi cikin abinda bai fi daƙiƙa sittin ba na dawo da baya ina ratsawa ta cikin wadannan dakaru kamar iska. Kafin su ankara har na wuce su gaba ɗaya na basu rata. Nan dai na ci gaba da wannan gudu ina mai bin sautin muryar Sadiya da har yanzu take ci gaba da kirana cikin ƙaraji da kururuwar neman taimako. Ko da na iso daidai inda na farka tun a karon farko sai na yi turus! Ba komai ne ya sani yin hakan ba face ganin da na yi wa Sadiya a ɗaure cikin wata sarƙar baƙin ƙarfe kamar wata baiwa. Ta ɗago kai a hankali muryarta cike da rauni ta dube ni tana mai cewa, 

“Yaya Haidar…Ka taimake ni.”

Ganinta da na yi a cikin wannan mummunan hali da kuma raunin da na ji a cikin muryarta ne yasa nan take na ji wani irin baƙin ciki ya lulluɓeni saboda tsantsar ƙaunar da nake mata. Kawai sai Na nufi inda take da wannan azababben gudu nawa da nufin in taimaka mata, duk kuwa da wata murya daga can ƙasan zuciyata na faɗa min bai kamata ina mata irin wannan mugun son ba. Sai da ya rage bai fi taku huɗu ba in isa gareta kawai sai na ji wani abu mai nauyi da kuma ƙarfin gaske ya doki ƙeyata. Daga nan ban sake sanin abin da ke faruwa ba.

*****

A wani ɗaki mai matuƙar faɗi da tsawo na tsinci kaina bayan na dawo cikin hayyacina. A ƙalla tsawon ɗakin zai iya cinye tafiyar daƙiƙa ɗari da ashirin don bana ma iya hango ƙarshensa. Saman ɗakin a shafe take, kuma taga ɗaya ce ƙwal a ɗakin daga can sama inda mutum ba zai iya kaiwa ba. Yayinda na tsinci kaina a wannan hali, sai na kasance mai baƙin ciki domin na fuskanci cewa kamani aka yi. Zuciyata ta sake hasala yayin da na tuna cewa karo na biyu kenan yau da na tsinci kaina a halin rashin sanin inda nake. Ina nan a cikin wannan hali sai na ji alamun motsi daga gefena na dama, da sauri na kai dubana zuwa wurin da motsin yake fitowa, aikuwa sai na yi arba da wani tsohon mutum tukuf da shi. Fuskarsa cike take da farin gashi wanda wuya ta sa har ya koma rawaya.

Gaba ɗayan fatar jikinsa ta tamuƙe tamkar ɗanyar gyaɗar da aka shanyata ta bushe, amma wani abin mamaki shi ne, idanuwansa ƙyar tamkar na matashin da ba zai wuce shekaru ashirin da biyar ba. Na yi matuƙar mamakin ganin wannan al’amari, amma sai ban nuna alamun mamakina a fili ba sakamakon ganin yadda tsohon ya ƙura min ido ko ƙyaftawa baya yi. Nan fa muka fara kallon-kallo ni da wannan tsoho ba tare da ɗayan mu ya ce da ɗayan uffan ba, bayan mun ɗan daɗe a haka sai na ji ya ce da ni, 

“Abokina Haidar, ina maka barka da zuwa ɗaki mafi daraja daga cikin ɗakunan gidan kaso na Birnin Sahara!” 

Na zazzaro ido cikin alamun mamaki don na ji ya faɗi sunana kuma ma har yana dangantani da kansa a matsayin aboki. 

“Wane ne kai? Kuma ya aka yi ka san sunana? Sannan me yasa ka kirani da abokinka alhalin bamu taɓa haɗuwa ba?” 

Na jera masa waɗannan tambayoyi yayinda na yunƙara na miƙe tsaye. Har zuwa wannan lokaci ina jin zafi a ƙeyata. 

Sai a wannan lokaci ne na lura cewa ashe ma ƙafata a ɗaure take da wata murtukekiyar igiya an yi min ɗaurin talala. Ko da ganin haka sai na yi murmushi kawai don na san wannan aikin banza aka yi. Na dubi tsohon na ce,

“Kai nake jira ka bani amsa.” 

”Sunana Imran, kuma ni mutumin wannan birni ne, yau kimanin watanni uku kenan da kulle ni a nan sakamakon wani aikin sihiri da aka aikata akan wani barden Sarauniya Nadiya, amma sai aka ɗora min laifin a kaina alhalin ban ji ba ban kuma gani ba. Hakan yasa ita kuma ta sa babban Bokanta ya mayar da ni tsoho kamar yadda ka ganni ɗin nan kuma ta kulle ni a nan da nufin horar da ni, kuma na san sunanka ne ta hanyar dakarun da suka kawo ka nan, sannan a tsarinmu na gidan kaso, duk wanda kuka kasance a ɗaki ɗaya to ya zama abokin ka. Kuma tun da aka kawo ni nan, kai ne mutum na farko da aka kawo aka haɗa mu tare. Lallai da alama kai fursuna ne mai daraja a wurin Sarauniya Nadiya.”

Ko da Imran ya gama yi min waɗannan bayanai sai na sake tambayarsa da cewa, 

“To kai kuma mene ne dalilin da yasa baka bayyana musu cewa ba kai ka aikata aikin sihiri a gareshi ba?” 

Sai Imran ya ce da ni, 

“Na yi iya bakin ƙoƙarina amma aka ƙi yarda da ni, hatta ahalina ma juya min baya suka yi, a gaban su aka kama ni aka tafi da ni babu wanda ya ce komai. Labari ne mai tsawo gaskiya amma dai ina so ka sani cewa mahaifina ya kasance hamshaƙin tela ne a wannan birni namu, duk zuri’ar mu teloli ne tun asali, kuma duk birnin Sahara babu ahalin da suka ƙware game da sanin sirrin tufafi sama da namu, kowa ya tashi sana’ar da yake gada kenan. Ni kuwa tun ina yaro bani da sha’awar wannan sana’a, dole ce kawai ta sa na maida hankali na iya duk abinda ake so na iya amma ba don ina da ra’ayi ba. Da na fara girma sai na fara ja baya da sana’ar mu ta gado, hakan yasa ‘yan uwana suka tsane ni, duk wani abu na rashin sa’a ko ɓatanci in ya faru ni ake ɗora wa. Wannan ya sa na zamo saniyar ware a cikin ahalina. Basu damu da ni ba kuma na san ko mutuwa na yi ba lallai su yi kewata ba. Yanzu dai kamar yadda na ce, labari ne mai tsawo, ina da ɗan ragowar ruwa a tare da ni, bari in baka ka sha kafin a kawo mana wani.”

Yana kawowa nan a zancensa sai muka ji takun sawaye alamar an tunkaro inda muke don haka sai Imran ya yi tsit. Ba mu ɗauki wani dogon lokaci ba a wannan hali sai ga dakaru sun tunkaro ɗakin da muke, wani gabjejen ƙato ne a gaba yana riƙe da wata zabgegiyar bulala kamar ta dukan dawakai. Ga kuma wasu dakarun mutum ashirin da biyar suna take masa baya.

Ko da suka zo daidai ƙofar ɗakin da mu ke, sai suka rabe gida biyu inda daga tsakiyarsu sai ga farincikin rayuwata Sadiya ta bayyana a ɗaure, gaba ɗaya jikinta ya yi datti, tufafinta suma sun yayyage, kyakkyawar fuskarta ta kumbura saboda tsananin wahala. Ko da ganin irin halin da masoyiyata take ciki, sai na ji wani irin baƙin ciki ya rufe ni sannan tausayinta ya kamani, bansan lokacin da ƙwalla ta fito min ba, duk kuwa da cewa wannan ƙaramar muryar da ke can ƙasan zuciyata na faɗa min bai kamata in yi hakan ba. Ko da yake babu wanda ya faɗa min, na san cewa saboda ni ne ta shiga wannan halin, domin hakan nake ji a jikina. Ban yi aune ba sai na ji muryar shugaban nasu ya ambaci sunana cikin zolaya.

”Haidar… Haidar… Kenan Sarkin Soyayya! To ga masoyiyar taka na kawo maka domin ku yi ganawar ƙarshe, saboda daga nan, sai dai a lahira kuma kai da ƙara ganinta. Hahaha!” Ya faɗi yana mai bushewa da dariya kamar wanda ya sha giya ya bugu. 

Ko da jin haka sai na yi sauri na rarrafa inda take yayin da ita ma ta ƙaraso kusa da ni. Tsawon lokaci muna kallon juna ba tare da wani ya cewa wani komai ba a tsakaninmu. Can dai sai na daure na ce da ita, 

”Sadiya ki gafarce ni, na san cewa duk a dalilina ne kika shiga wannan hali… 

“Dakata Yaya Haidar.” ta katse ni, sannan cikin dauriya da ƙarfin hali ta ci gaba da cewa, 

“Ba mu da lokaci, na gano wani abu da baka sani ba a garin nan don haka duk yadda za a yi ka tabbatar ka tseratar da mu daga wannan wuri, na san zaka iya Yayana, kada ka manta da alƙawarin da ka yi min, kuma kada ka manta da wanene kai. Rayuwata na hannunka Yaya Haidar!”

Daga nan sai ta yi shiru bata ƙara cewa komai ba. Abinda ya ɗaure min kai shi ne, duk da ta yi maganarta a fili amma kamar ni kaɗai ne na ji maganar tata. Ban yi aune ba sai kawai na ga sun ja ta za su koma da ita, shi kuma shugaban dakarun yana ta ƙyalƙyala dariyar mugunta.

Nan take na ji wani irin sabon baƙin ciki ya lulluɓeni, ban san lokacin da na yi wata irin kururuwa mai matuƙar firgitarwa ba, kururuwar tawa ce ta sa gaba ɗaya sauran fursunonin da ke ragowar ɗakunan suka nufo bakin ƙofar ɗakunan su don ganin abinda ke faruwa. Su kuwa dakarun da ke riƙe da Sadiya tsayawa suka yi cak tamkar an zare musu laka a jikunansu.

Shi kan shi shugaban dakarun sai da ya ɗan dakata da dariyar da yake yi sannan ya juyo ya kalleni. A wannan lokaci ba sai na dubi madubi ba, na san cewa tuni idanuwana sun yi ja tamkar an gasa ɗan_buda a wuta saboda tsabar fusatar da na yi. Muka yi musayar kallo a tsakanin mu, duk da cewa akwai ‘yar tazara a tsakanin namu, amma hakan bai hana ni jin fitar numfashinsa da sauri da sauri ba. Cikin fusata na ce da shi, 

”Kai gafalalle mara tausayi, ka sani cewa duk wannan girman jikin naka ya tashi a banza tunda ka kasa tausayawa macen da ko da kun saketa ba za ta iya taɓuka komai ba sakamakon wahalar da ta sha a hannunku, lallai za ka ɗanɗana kuɗarka matuƙar ka sake muka gamu da kai, sakarai kawai nusari mai azabtar da mata!”

Waɗannan kalamai nawa ba ƙaramin harzuƙa shugaban dakarun nan suka yi ba, musamman ma da yake ganin cewa ya ninka ni girma kusan sau huɗu, don haka sai ya yi umurni da a fito da ni daga ɗakin da nake. Ko da jin wannan umurni, sai ɗaya daga cikin dakarun da ke take masa baya ya ce, 

”Ya shugabana, ka sani cewa mai girma Sarauniya bata bamu umurnin fito da shi ko taɓa lafiyarsa ba, don haka ni ina ganin fito da shi tamkar siyowa kanmu ajali ne, me zai hana ka ƙya leshi in yaso a ranar da za’a gabatar da shi a gaban Sarauniya sai ka aiwatar da nufinka akan. 

sa?”

Da shugaban dakarun ya ji wannan batu, sai jikinsa ya yi sanyi. Bayan wani ɗan lokaci sai ya dube ni ya ce, 

”A tsawon rayuwata kai ne mutum na farko da ya fara kirana da nusari kuma banza, a duk faɗin birnin nan babu wanda baya shakkata walau daga jarumai ko attajirai amma sai gashi yau fursina ya kira ni da waɗannan miyagun kalmomi, Lallai ka aikata laifi mafi girman muni a gareni, kuma daga yau ka ƙulla gaba mai tsanani a tsakanin mu, kuma na yi maka alƙawarin ni ne zan zamo sanadin salwantar rayuwarka dama ta duk wani wanda kuke da alaƙa da shi.

Ko da yazo nan a zancensa, sai ya juya ya fice daga sashin mu, yayinda ragowar dakarun suka rufa masa baya. Maimakon in yi shiru nima sai na buɗe murya da ƙarfi ina cewa, 

“Eho! Ya ji tsoro a bashi ruwan maɗaci ya kuskure da na gyambo!

Su kuma ragowar fursunonin sai suka ɓarke da shewa da tafi, yayin da wasu kuma suka dinga fito da kiɗe_kiɗe tare da raye_raye kamar waɗanda aka yi wa albishir da wani gagarumin al’amari.

Ban yi wata_wata ba na kwance ɗaurin da ke ƙafata don dama ba wani ɗaurin kirki bane. Bayan na kwance ɗaurin ne sai na waiga inda Imran yake domin in ga halin da yake ciki. Ai kuwa sai na ga abin mamaki, Imran ya jiƙe sharkaf da gumi ga hawaye sai fita suke daga idanuwansa tamkar an doke shi. Cikin hanzari na ruga inda yake na dafa kafaɗarsa ina mai cewa, 

”Ya kai Imran, mene ne ya sameka haka kake ta wannan uban gumi kamar wanda ya haɗiyi kunama?”

Maimakon Imran ya bani amsa, kawai sai ya ɓarke da kuka abinsa. Ko da na ga haka sai na miƙe tsaye ina mai cewa, 

”Ka ga Imran, ko dai ka sanar da ni abinda yake faruwa ko kuma in ƙyale ka in yi tafiyata tunda ka ga na kwance kaina.”

Ko da jin wannan batu, sai nan da nan Imran ya natsu sannan ya ɗago kai ya dube ni. Har a wannan lokaci idanuwansa basu daina zubo da hawaye ba. Bayan wani ɗan lokaci sai ya buɗe baki cikin wata irin raunanniyar murya ya ce da ni, 

”Ya kai abokina ka sani cewa ka ɗebo ruwan dafa kanka, sannan kuma ka shafa min kashin Kaji a dalilin baƙaƙen maganganun da ka furta wa wannan shugaban dakaru.”

”Kai dai kawai ka tsorata da shi ne Imran, amma babu wata damuwa dangane da maganganun da na faɗa masa.” Na bashi amsa cike da nuna tsantsar rashin damuwa.

“Hmm Haidar kenan.” 

Imran ya faɗi yana mai sauke numfashi tare da yin wani murmushin takaici, sannan ya ci gaba da cewa, 

”Wato na fuskanci baka san ko wanene wannan shugaban dakarun ba ko?” 

”Waye shi? Na tambaye shi.

”Sadauki Dargazu kenan in baka sani ba ka sani.” 

”Haha! Dargazu kuma? Wannan wane irin suna ne haka?” 

Na sake tambaya a karo na biyu. 

”Idan har zan baka amsar wannan tambayar, to hakan na nufin sai na baka tarihinsa koda kaɗan ne domin ka fahimci irin mummunan tashin hankalin da ka jefa mu ciki.

Ganin yana nema ya tsinke da labarin da ba shi ne a gabana ba yasa na ce mishi,

“Ka ga dakata! Ni fa yanzu babban burina shi ne in fita daga wurin nan in kama kaina, kai kuma sai ƙokarin bani wani labari kake yi, kai kasan irin baƙin cikin da nake ciki sakamakon baƙin yanayin da masoyiyata ta shiga a sanadina kuwa? Kasan wane irin hali mahaifiyata zata shiga in ta neme ni ta rasa? Kawai ka daina wannan kukan ka zo mu haɗa hannu mu fita daga wurin nan.”

Duk wannan zance nawa na yi shi ne cikin harzuƙa saboda gani nake ɓata min lokaci kawai Imran zai yi. Ni na faɗi kalmar ‘Masoyiyata’ amma har cikin raina ina jin kalmar bata zauna min da kyau ba. Yayinda a gefe kuma abinda bana so in yi tunanin shi ne na yi. Ban san yaya Mama zata yi ba in ta neme ni ta rasa 

Har na gama wannan bayani nawa kan Imran yana sunkuye bai ɗago ba kuma bai ce komai ba, can bayan wani ɗan lokaci sai ya ɗago da kansa, abinda na gani a wannan lokacin ba ƙaramin tayar min da hankali ya yi ba domin sai da na ɗan razana.

Ba komai na gani ba face tsantsar fusata da harzuƙa da suka bayyana ƙarara a fuskar Imran, idanuwansa sun kaɗa sun yi ja kamar an ciro ƙarfe daga wutar maƙera. Cikin wata irin fusatacciyar murya mai cike da ɓacin rai ya fara magana da cewa, 

“Kai saboda tsabar son kai da ya maka yawa har ni za ka gaya wa zafin rasa masoyi? Ni za ka nunawa damuwa da mahaifa? Ni za ka nunawa zafin rai?”

A yayinda yake wannan maganar yana yinta ne yana matsowa inda nake ba tare da ya ma sani ba. A zahiri ni fa bana wuce ƙalubale don haka abu na farko da zuciyata ta riya min shi ne in mayar masa da martani in yaso a yi wadda za a yi, ɓera ya zubar da garin kyanwa. Amma sai na yi tunanin kada fa in ƙara jefa kaina cikin wata jarfar, kuma zuwa yanzu Imran ne kaɗai mutumin da ya nuna yana tare da ni a wannan wuri da Allah ne kaɗai ya san ko a ina yake, don haka kawai sai na kwantar da kai na buɗe baki cikin murya mai taushi na ce da shi, 

“Ka gafarce ni yakai abokina, ka sani cewa ni na kasance mai saurin fushi ne, ƙarancin hankali da sanin ya kamata, don haka ka manta kawai da abinda ya faru ka bani labarin da ka ce zaka bani matuƙar hakan zai bamu damar fita daga wurin nan lafiya.” 

Yayin da Imran ya ji na tausasa kalamai na, sai ya koma inda yake tun da farko ya zauna ba tare da cewa komai ba. Ganin haka yasa na yi wata doguwar ajiyar zuciya sannan nima na samu wuri na zauna kawai na zubawa Imran ido. Bayan wani ɗan lokaci, sai Imran ya yi gyaran murya sannan ya fara bani labari da cewa,

<< Birnin Sahara 1Birnin Sahara 3 >>

28 thoughts on “Birnin Sahara 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×